Sashe 57
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wasu kanyi dan su huce haushin wani abin da matarsu ta gida tayi ko take musu, wanda duk dalilai ne da basu kamata a dubasu wajen karin aure ba, shisa ga sunan, yara kanana suna fama da mata biyu da basu san yanda zasuyi dasu ba, tunda ta farkon ma tana neman fin karfinsu.
Bayaso AbdulKadir ya kasance cikin mazan da zasu duba wannan dalilin wajen kara aure.
Duk a cikin yaran shi babu wanda yake da mata biyu, a matan dai akwai wanda suke da abokan zama.
Jin AbdulKadir din yayi shiru yasa shi dora tambayar tashi da
"Me yasa kake son kara aure?
Kuna samun wata matsala da Waheedah ne?"
Kai AbdulKadir din ya girgiza mishi da sauri, bazai ce a zamansu da Waheedah basu taba samun matsala ba, amman inzai fadi gaskiya yafi bata mata rai fiye da yanda take bata mishi rai, dan ko abu yai mata bata taba daga mishi murya ba, in tai mishi maganar ya balbaleta da fadan shi sai dai ta bashi hakuri ta wuce daki, da duk idan ya bita kuka yake samun tanayi.
Waheedah macece da yasan maza da yawa zasu so samun irinta, bata taba bashi wani dalili na dana sanin aurenta ba, asalima hukuncin aurenta na daya daga cikin abubuwa mafi girma na alkhairi daya sami rayuwar shi.
"Kawai ina son kara auren ne, babu wani dalili bayan haka Abba..."
AbdulKadir ya karasa maganar da yakeji tana fitowa daga zuciyar shi.
Kai Abba ya jinjina,haka kawai yakejin maganar ta kasa zauna mishi.
Har ga Allah duk lokacin da zai ga Waheedah a gidan sai yaji gabanshi ya fadi, dan yana tunanin ko AbdulKadir din yayi mata wani abu, amman har gashi aurensu na dosarma shekaru biyar ko a fuskar yarinyar bai taba ganin damuwa ba.
Yafi kowa murna, dan baiyi tunanin akwai macen da zatai hakuri da baudadden halin AbdulKadir na tsayin lokacin ba.
Shisa yaji auren bai zauna mishi ba, yana jin yaron har kasan zuciyarshi, bayason yana zaune lafiya ya jajibo abinda zai zame mishi matsala.
Numfashi mai nauyi Abba ya sauke
"Kayi tunani akan maganar nan dai AbdulKadir, aure ba abu bane da zaka tashi kaji kana sonyi, yana bukatar natsuwa a cikin shi"
Kai AbdulKadir yake girgizawa, bayason abu ya dame shi, gudun tunanin ne yasa shi yanke hukuncin yin auren.
Baiga dalilin da Abba zaice mishi ya kara yin wani nazari ba
"Nagama duk tunanin da zanyi...
Auren kawai nake sonyi, shisa nazo na fada maka"
Shiru Abba yayi kafin yace
"Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi, yar gidan wacece?
Wacce unguwa take?
In yaso sai kayi mata magana su saka mana rana, ni da Alhaji Hamisu da Alhaji Hadi sai muje ayi magana"
Goshin shi AbdulKadir ya tana yana share zufar da yaji alamar tana tarar mishi.
Bai taba tunanin muryarshi zatayi saukar da tayi yanzun da yake furta
"Nuriyya ce Abba?"
Kallon shi Abba yayi yana jiran ya tabbatar mishi da rashin hankalin da Hajja kance yana tattare dashi.
Wani abu da yaji ya tokare mishi wuya AbdulKadir yake hadiyewa, ko kadan bayason kallon da Abba yake mishi
"Abba ita Nuriyyar...Dan Allah karkace wani abu...ita nake so in aura"
Abba bai taba tunanin akwai ranar da zai so wanke fuskar AbdulKadir da mari haka ba, da auren shi harda yaro.
"Ban taba yarda da baka da hankali ba sai yau AbdulKadir, wallahi yau ka tabbatar mun da cewar baka da hanlali.
Nuriyya kake magana, kawar Waheedah, Nuriyya aminiyar matarka, ita kazo kana fadamun kana so ka aura"
Kallon Abba AbdulKadir din yake yana rokon shi daya fahimce shi, yasan lokutta da daman mutane na barin abinda addini ya halarta musu dan al'ada na ganin hakan bai kamata ba, kuma tun da ya fara tako kafarshi da niyyar furta maganar auren Nuriyya yasan zai fuskanci wannan matsalar, amman shi mutum ne da surutu irin wannan basa damun shi sam, bayajin akwai wani abu da addini zai halarta mishi kunya ta hanashi yi.
"Bafa haramun bane Abba"
AbdulKadir din ya fadi yanajin yanda ranshi ya soma baci, Hajja ce ya tsammaci zatai mishi wannan maganar ba Abba ba, tunda shi namiji me zai fahimta.
"Idan baka fitar mun daga daki ba, wallahi saina wanke ka da mari, marar kunyar banza da wofi..."
Mikewa AbdulKadir yayi yana fadin
"Babu abinda nayi da ba dai-dai ba Abba, nikam zan aureta..."
Dafe kai Abba yayi, yanajin zagin da bai taba tunani ba na mishi yawo a cikin kai, da yana da tsohon hawan jini bacin ran da yake ciki yanzun zai taso mishi dashi.
Yanajin AbdulKadir din na sake cewa
"Zan mata magana sai a ta fadi ranar da zakuje din"
Kafin yaja mishi kofar yana ficewa daga dakin...!!!
#Teamwaheedah
#TeamAbdulKadir
#LubnaSufyan[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
INA GODIYA DA ADDU'O'IN KU DA DUKKAN SAKKONIN KU.
KEEP THE COMMENTS FLOWING, NAGODE, NAGODE, NAGODE.
Har ya shiga gida ran shi a bace yake jin shi.
Yana jin Waheedah tun da ta amsa mishi sallama tai mishi sannu da zuwa tana bin shi da ido.
Yasan ta fahimci ran shi a bace yake.
Kitchen ta shiga ta samu babban plate ta zuba musu abinci a ciki, manja ta zuba musu ta saka cokulla guda biyu a cikin abincin, maggi ta dauka da robar yaji ta fita falon.
AbdulKadir na zaune inda tabar shi akan kujera, so take ta tambaye shi waya bata mishi rai, amman batajin dadin jikinta, ba tajin zata iya da fadan shi da daren, shisa tayi shiru.
A kasa ta ajiye abinci da robar yajin ta dora maggin a sama.
Kitchen ta koma ta dauko wani plate din da kofuna guda biyu, ta bude fridge ta dauko pure water guda biyu, sai robar da cittarta take a ciki, in dai an kawo ruwan roba gidan AbdulKadir ne yazo ya fita ya siyo shi, barnar kudin nan bada ita akeyinta ba, akwai gidan ruwa a unguwarsu, maigadi take ba ya siyo mata leda goma ta zuba a fridge din, sai ta kwana biyu bata nemi ruwa ba.
Danma Fajr na mata barnar shi, idan yagan shi a roba kuma bakinta baya hutawa da surutu, babu qishin da yake ji, zai dauko ne kawai dan yasata magana.
A kasa ta samu AbdulKadir ya sakko, itama ta ajiye ruwan ta samu waje ta zauna.
Maggin ta barbada ta bude robar yaji ta zuba, duka ta cakuda, tasan AbdulKadir zai tsaya kallonta sai ta cakuda inda zataci suci wajen tare, ko ta cakuda mishi na gaban shi, in sunje gidan su har mamakin yanda yake komai da kan shi take, amman da sun dawo yaga su kadai ne zai shagwabe mata.
Badan batason hakan ba, wani lokaci abin kanyi mata yawa, gashi, ga Fajr.
Abincin suke ci, bakajin komai na tashi a dakin sai karar cokulla.
Sun gama kenan ta zuba mishi ruwa ta mika mishi kofin sukaji sallamar Yassar.
Ita ta amsa mishi sallamar tana kallon yanayin shi ko zata fahimci dalilin zuwan shi da dare haka.
Murmushi yai mata yana amsa gaisuwar ta hadi da dorawa da
"Duk suna lafiya.
Ya jikin ki?"
Sunkuyar da kanta tayi kasa a kunyace, tana amsawa can kasan makoshi, idanuwa Yassar ya sauke kan AbdulKadir, hakan da Waheedah ta kula da shi yasa ta mikewa ta dibi kwanonin ta wuce kitchen, acan tasha ruwa tukunna ta fito tana ma Yassar sallama ta wuce daki.
Kowa ya batama AbdulKadir din rai tasan bazai wuce a gida bane, tunda taga Yassar yazo.
Shisa tabasu waje, in AbdulKadir yana so taji da kanshi zai fada mata, ita kam kaya zata sake ta kwanta abinta.
Yassar mikewa yayi, baisan yanda akayi ya iya dora murmushi a fuskar shi ba, bayan abinda yake so yayi daya shigo shine wanke fuskar AbdulKadir din da mari.
Abinci zaici Abba ya kirashi rai a bace yake fada mishi abinda AbdulKadir din yake shirin yi da ko a mugun mafarki Yassar bai taba hango faruwar lamarin ba.
"Magana nake son yi da kai"
Kallon shi AbdulKadir yayi yana kankance idanuwan shi, ran shi ya kara baci, Abba kiran Yassar yayi ya fada mishi kenan, kuma baiga dalilin yin hakan ba, tunda zai fadama Yassar din da kan shi, magana ce da ba boyuwa zatayi ba, dan baiga abinda zaisa shi ya fasa ba, ya rigada ya furta.
"Ina jin ka ai"
Ya amsa, mikewa Yassar yayi, idan AbdulKadir bashida hankali, shi yana dashi, da alama Waheedah bata sani ba, ba zaiso ta faraji daga bakin shi ba.
"A waje zamuyi magana ba anan ba"
Cewar Yassar yana ficewa daga dakin, tashi AbdulKadir yayi yabi bayan shi har wajen motar shi, suka tsaya.
Sun kai mintina biyu Yassar nason hadiye abinda yakeji yana taso mishi ko zai samu nutsuwar yima AbdulKadir din magana batare daya dura mishi ashar ba.
"Abba ya kirani...."
Shiru AbdulKadir din yayi, yana jira Yassar ya fada mishi wani abu da bai sani ba, wannan tsohon zance ne tunda gashi tsaye a gefen shi yana huci kamar sabon biredi.
"Ka ce mun wasa kake AbdulKadir, dan wallahi na kasa wrapping din kaina akan maganar nan"
Kallon shi AbdulKadir yayi
"Yaushe Abba ya zama abokin wasana?
Meye wahala a fahimtar maganganun da nayi?
Auren da zan kara ne yake maka wahalar fahimta?"
Numfashi Yassar yake ja yana fitarwa a hankali, da alama idan bai kai zuciyarshi nesa ba, mota zai koma yajata ya take AbdulKadir din duk su huta.
"Bansan me kake so ince maka ba Hamma...
Bansan me yasa kazo kana kallona kamar akwai haramci a cikin abinda nake so inyi ba"
AbdulKadir yake fadi ranshi inyai dubu kowanne a bace yake, tun a hanya yake jin maganganun daya fadama Abba suna dawo mishi, abin na mishi kamar mafarki, yana kasa yarda da abinda yake shirin faruwa din.
Amman zuwan Yassar ya kara tabbatar mishi da cewa auren zaiyi babu fashi.
Dan baiga dalilin da zaisa Yassar ya dinga mishi kallon da yake mishi ba.
Kai Yassar yake girgizawa, muryarshi a gajiye yace
"Bani da matsala da auren ka, wadda zaka aura din ce damuwata, me yasa sai ita?
Kawarta ce AbdulKadir..."
Kankance mishi idanuwa AbdulKadir yayi
"Sai me ya faru dan kawarta ce?