Sashe 65
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yana fara shiga gidan da sallama, a falo ya samu Waheedah, ta mishi wani irin kyau cikin jan lace din daya karbi fatarta, ga jambakin da yake so manne da labbanta tana saka komai kwance mishi.
"Wahee"
Ya tsinci kan shi da fadi maimakon amsa sannu da zuwan da tai mishi.
Karasawa yayi ya zauna gefenta kan kujerar yana fuskantarta.
"Ya jikin ki"
Idanuwa ta ware mishi
"Naji sauki"
Numfashi AbdulKadir ya shaqa yanajin komai ya mishi dai-dai.
"Sannu"
Murmushi tayi mishi da yasa yakai hannu yana taba labbanta, yanda baya dangwalo janbakin ta yana bashi mamaki, muryarshi can kasan makoshi yace
"Idan babu matsala zata zauna a gidan nan, bangarena tunda bana amfani dashi"
AbdulKadir yai maganar yana sa tanajin kamar tana da zabin da bataga dalilin da zaisa ya bata shi ba, batako hango auren shi ba, gashi dashi yanzun, kamar yanda yake da iko da kan shi, haka yake da iko da gidan shi.
"Banda matsalar komai"
Ta fadi tanajin ta sama-sama, kamar gangar jikinta ce a zaune tare dashi.
Ruhinta na tsaye a gefe yana kallon abubuwan da suke faruwa kamar bai shafe shi ba.
Gyara zama AbdulKadir yayi yana kwantar da kanshi a kafadarta, ita din alkhairi ce a rayuwar shi fiye da yanda zata taba sani.
Tasa yanajin saukin abinda ko a labarin da yakeji mai matuqar wahala ne.
"Nagode.
Nagode da yanda kikasa komai yazo mun da sauki"
Batace komai ba, dan batasan me ya kamata tace ba, yakai mintina goma a zaune yayi luf a jikinta, kafin ya tashi.
"Sai ina?"
Ta tambaya
"Akwai kayanta a mota, zan shigo dasu"
Mikewa Waheedah tayi
"Baka fadamun yau zata zo ba, ba'a kara share wajen ba"
Dan daquna fuska AbdulKadir yayi
"Bansani ba nima, kayan ne dai kawai.
Ba zakiyi shara baki da lafiya ba"
Kai ta girgiza mishi
"Amman a haka za'a saka mata kaya babu shara?"
Idanuwa AbdulKadir ya kankance mata, a halin da take ciki ba zata iya karawa da fadan shi ba.
Shisa tayi shiru, wajen ta bishi har bakin mota, duk da ya hanata daukar komai.
Tsaye tayi tana kallon shi yana kwasar kayan yana kaiwa, jinta take kamar a mafarkin da zata iya farkawa ko da yaushe.
Harya gama kwashe kayan tas.
Tukunna ya kama hannunta suka koma cikin gida.
Harya zauna ya tuna da kwakwar daya siyo mata tana mota, ya sake fita ya dawo da ita a leda.
Guda biyar duk sun bare mishi.
Mika mata yayi
"Na dauka ka manta"
Kai ya girgiza mata, ya zauna, ita tana mikewa ta nufi kitchen.
Guda daya ta wanke, ta saka sauran a fridge, wuka tasa ta huda ta tsiyaye ruwan tana shanyewa ta yanka kwakwar da tasan cikine kawai ya saka mata sha'awarta, dan sai dai in zatayi kunun aya tadan balla, amman ba damunta tayi ba, a cup ta zuba ta dauka tana komawa falo, wuta tagani
"Yaushe suka kawo?"
Ta tambayi AbdulKadir
"Yanzun fa, kina tashi"
Zama tayi, komai a kunne yake, remote din na hannun AbdulKadir yana yawon shiga tashoshi dashi.
"Wahee baki bani kwakwar ba...yau ba kina cin abu baki bani ba"
Murmushi tayi mai sauti, duk da batajin wani nishadi
"Yi hakuri...
Wallahi na manta ne"
Langabar da kai yayi, bata saba mishi ba, kome takeci tana bashi, bai saba tambayar ta ba.
Mika mishi kofin tayi, yasa hannu ya dauka.
Kallo suke suna hira jefi jefi har aka kira magriba.
Ita tayi daki, shikuma ya fita masallaci.
Ya dawo ne ya samu text din Nuriyya
'Masoyi duk sanda ka tashi kazo mu tafi, na fada musu, na gama hada sauran kayan kuma'
Wayar ya mayar aljihun shi.
Yana cewa Waheedah
"Yau zata zo"
Idanuwanta ta ware akan fuskarshi, kafin ta daga mishi kai a hankali, cike da wani yanayi a idanuwanta da yasaka shi karasawa inda take ya zauna, ya kama hannunta yana rikewa
"Wahee kimun magana dan Allah...
Ki daina kallona haka...
Kimun magana zaifi"
Murmushin karfin hali tayi
"Abinne yake mun bakunta, shine kawai"
Numfashi ya sauke yana yawata idanuwan shi kan fuskarta, duk da bata saba mishi karya ba, haka kawai zuciyarshi ta kasa nutsuwa waje daya.
Baice mata komai ba ya sumbaci hannunta yana mikewa.
"Saina dawo"
Kai Waheedah tadan daga mishi
"Allah ya tsare hanya"
Tana sake kwanciya cikin kujerar.
AbdulKadir kuma ya fice daga gidan.
Yana motane yake tunanin haka yaso bikin shi da Waheedah, yaje ya dauko matar shi su tafi, babu wannan al'adar na cewa sai an rakota, ya dauka duk sai anyi su Walima da kamu kamar auren shi da Waheedah.
Anty Talatu ce take fada mishi, ko da za'ayi wani abin sai dai ko ita Nuriyya in zatai walima, kuma batace mishi zatayi din ba.
Hakan yafi mishi, badan zai hanata in tasoyi ba, amman yana ganin daurin aurene kawai ya zama dole, kuma yake da muhimmanci, shi bayason duk wani abubuwa da bai zame mishi dole ba.
Sai dai abinda ya dinga mishi yawo bayan yaje ya dauko Nuriyyan a hanyarsu ta zuwa gida shine yanda Babanta bai bukaci yagan shi ba, ko ita Mama din ma, a tunanin ko za'ayi musu wata nasiha kamar yanda aka saka shi a gaba lokacin auren Waheedah.
Sai yaga ta bude mota ta shiga batare da tace mishi iyayenta nason ganin shi ba.
Wata zuciyarta sai take darsa mishi ko haka aure na biyu yake, tunda ana ganin babu wata kuruciya a tattare dasu biyun, kuma duk an rigada an fada musu abinda ya kamata a aurensu na farko.
A hanya ya tsaya dasu yai siyayyar abinda yake tunanin zasu bukata, saboda Nuriyya din, dan yasan Waheedah ba komai ta keci ba yanzun.
Ya dai siya mata apple ko zataci, tunda yasan tana so sosai.
Tukunna suka karasa gidan.
Sai da Nuriyya ta ganta a cikin harabar gidan tukunna taji wata irin faduwar gaba da bata taba tunani ba.
Da bata damu ba data fadama su Baba cewar AbdulKadir din yace zaizo su tafi.
Su duka Allah ya kiyaye sukai mata batare da sun kara wasu kalaman a kai ba.
Ita tana cikin nishadin da fushin da suke da itane karshen abinda yake ranta.
Amman yanzun tunanin fuskantar Waheedah ya dawo mata da komai sabo, wani irin tsoro takeji har kafafuwanta na mata rawa.
Da AbdulKadir ya zagayo ya bude mata motar sai da ya mika mata hannun shi tukunna ta kama ta fito daga motar, ya mayar ya rufe, yana sakin hannunta ya bude bayan motar ya dauko dayan akwatinta yana soma jan shi zuwa cikin gidan.
Da wani irin sanyin jiki na mamaki take bin bayan shi, tana kallo ya tura kofar yana shiga da cikin gidan da sallama.
Amsa shi Waheedah tayi tana mikewa, ta sake kaya zuwa wata atamfa da tafi dazun yin kyau, ga wani irin kwarjini da yaga ta mishi, gidan gabaki daya sai kamshin turarukanta yakeyi da yai mishi dadi.
"Sannu da zuwa..."
Ta fadi, tana ware idanuwanta ganin Nuriyya, harara ta watsa mata
"Sannu Nuriyya"
Ta fadi, dan rabon da ta sakata a idanuwanta harta manta, duk da suna chatting kuma suyi waya.
Amman batace mata ta dawo ba, tunda ko shekaranjiya ta kirata sun gaisa.
Ita kuwa Nuriyya wani irin ras kirjinta ya doka jin kalaman Waheedah din, da kuma harar datai mata.
Maganar tata nasa AbdulKadir yaji nashi kirjin ya doka, cikin wani irin tashin hankali ya taka yana kama hannun Waheedah ya soma janta, juyawa tayi tace ma Nuriyya
"Ina zuwa..."
Kafin ta mayar da hankalinta kan AbdulKadir din cike da mamaki.
Har bedroom dinsu, sannan ya saki hannunta tana kallon zufar da goshin shi yakeyi.
"Waheedah..."
Ya kira yana jin sauran kalaman sun makale mishi, kallon shi takeyi da irin zufar da yakeyi, kafin wani abu ya sara mata a tsakiyar kai.
Lokacin da tayi ma Nuriyya magana taga ta matsa tana boyewa bayan AbdulKadir din har jikinta na taba nashi, batasan me yasa sai yanzun kwakwalwarta ta zabi tayi processing wannan yanayin ba.
Numfashi take ja a hankali tana fitar dashi, a nutse takeyin hakan tana son iskar ta isa inda ya kamata.
Kafin ta iya kallon AbdulKadir, muryarta na dukan dodon kunnenta da fadin
"Nuriyya..."
Tayi shiru tana sake jan wani numfashin ta tabbatar da kirjinta ba zai bude zuciyarta ta fito ba, tukunna taci gaba
"Nuriyya ka aura?!"
Kasa magana yayi, zufa yakeji tana tsatsafo mishi a duk wata kafa da zai iyaji, abin har mamaki yake bashi, tunda zazzabine ruf yaji ya rufe shi duk da zufar da yakeyi.
"Ma shaa Allah"
Waheedah ta fadi tana sake kallon shi da fadin
"Kabarta ita kadai"
Ya bude bakin shi yafi sau biyar yana mayarwa ya rufe kafin ya iya furta
"Waheedah..."
Dariya tayi da tasa shi sake kallonta
"Sadauki...
Kaje..."
Badan yana son ya tafin ba, sai dan yana so ya fita daga dakin ko zai ji iska na ratsa shi.
Fita yayi yana samun Nuriyya a tsaye bakin kofa kamar mai jiran kyat ta bude tayi ta kanta.
Da gasken a tsorace take, dan tana da tabbacin AbdulKadir din ya janye Waheedah ne dan karta far mata.
"Muje.."
Ya fadi lokacin daya karasa yana kama akwatinta ya dauki sauran ledojin da baisan ya sake su ba, suka wuce har bangaren da zata iya kira nata yanzun.
A falo ya ajiye akwatin ya nufi bedroom din tabi bayan shi, ledar ya ajiye yana shiga bandaki ya dauro alwala, itama yace taje tayi.
Sallah yaja su sukayi ta godiya ga Allah, kafin AbdulKadir din ya mike ya dauko ledojin yana cire na Waheedah ya fice daga dakin ya nufi bagarenta, kwankwasawa yayi yana turawa.
A tsaye ya sameta tana dauko kayan bacci
"Sadauki..."
Ta fadi, ya karasa
"Apple na siyo miki"
Hannu ta mika ta karbi ledar
"Aikam ka kyauta, dan banajin cin komai"
Space din dake tsakanin su AbdulKadir ya hade yana zagaya hannuwan shi ya rungumeta a jikin shi.
Zuwa yanzun ya kasa gane ko da gaske lafiyarta kalau ba, yasan Waheedahr shi daban take da duk wasu mata daya taba cin karo dasu.