Sashe 92
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ban taba saka maka baki akan Nuriyya ba, yaune na farko saboda yau dinne nake ganin zakayi kuskure mai girma, in kuma ina da wani muhimmanci a wajenka zaka hakura kabarta tunda ba tada inda yafi nan din, babu kuma wanda ya wuce kaddara dagani har kai"
Jim Baba yayi yana tattauna maganganun Mama din, zuciyar shi na tafasa sosai, amman yasan gaskiya ce ta fada mishi.
Babu inda Nuriyya take dashi da zataje, bakuma zai kyauta ma mahafiyarta ba, dan sunyi zaman da baya manta ta a duk daga hannuwan shi da zaiyi dan gabatar da addu'a.
Wucewa yayi dakin batare da yace komai ba sai addu'ar neman shiriya da yake ma Nuriyyar a ran shi.
Numfashi Mama ta sauke tana daga labulen tare da fadin
"Inya huce kije ki same shi ki bashi hakuri, sai a kira AbdulKadir din aji idan abinda zai gyaru ne"
Hawayen fuskarta Nuriyya ta share tana girgizawa Mama kai.
"Saki uku ne"
Labulen Mama ta saki tana girgiza kanta kawai.
Addu'a ce kawai abinda ya rage tsakaninta da Nuriyya, alwalar isha'i ta daura ta shige daki kawai.
Nuriyya kuwa kwanciya tayi, batafi mintina goma ba aka kawo wuta.
Cajin wayarta ta saka ta fito tsakar gida ta wanke fuskarta ta koma tayi sallar isha'i.
Sai take jin tadan samu natsuwa yanzun da tasan babu inda zataje.
Baba bazai koreta ba, zata samu tasan yanda zatayi ta kwaso kayanta ta siyar dasu, dan batason shigowa da komai gidan sai kudinta da kayan sawa.
Lambar wayar telanta ta laluba tai mishi magana ta whatapp dan akwai kayanta wajen kala biyar da zai kai mata gida washegari, tayi mishi kwatancen nan gidan tace ya kawo mata, su zata samu tadanyi amfani dasu kafin taje ta kwashe kayanta ta siyar ta siyi wasu na kece raini.
Ta kuma yanke hukuncin Asma ce kadai zata san aurenta ya mutu, itama dan ta tayata siyar da kayan kitchen dinne, sauran saita samu mijin da zasu girgiza da jin shi tukunna zata sanar dasu dan suzo biki.
Biki zatayi na alfarma ba irin na AbdulKadir da akai tayi mata tsegumin ko yar walima batayi ba.
Da wannan tunanin na sabuwar rayuwar da zatayi bacci mai karfi yai awan gaba da ita.
Yana shiga gida ya hango Yassar tsaye da waya a hannun shi yana dannawa, parking yayi ya fito daga motar
"Kai nake shirin kira, Waheedah tace mun ka fita tun dazun baka dawo ba...kar in sake ina maka magana kana kama hanya ka wuce, dan ubanka kasan yanda ka dagamun hankali?
Yanzun ma machine na hau nazo"
Juya mishi idanuwa AbdulKadir yayi
"Na sha ruwa lafiya...
Kai fa?"
Ya fadi yana saka Yassar din watsa mishi wani kallo
"Bana son iskancin banza...
Me ya faru?"
Numfashi AbdulKadir yaja yana fitarwa, hadi da jingina bayan shi da motar shi, sosai yake jin kunyar Yassar din, muryar shi can kasan makoshi yace
"Dan Allah Hamma kayi hakuri, tun dazun naso inje amman kunyarka nakeji shisa na kasa zuwa....
Wallahi kunyarka nakeji har yanzun...
Dan Allah kayi hakuri"
Kai Yassar yake girgiza mishi tunda ya fara magana, in duka kudin AbdulKadir ya kashe zai hakura da sake motar, idan fiye da hakan yake bukata zai siyar da motar ya bashi duka kudin, yafi karfin wani dukiya a wajen shi, ballantana dubu arba'in da biyu, shi ya biyo bayan shine saboda yaga yanayin bacin ran daya shiga
"Dan Allah ka daina wannan maganar AbdulKadir, kasan kafi karfin wannan kudin a wajena"
Kai AbdulKadir ya jinjina
"Nasani,amman ajiya kabani saboda baka son taba kudin"
AbdulKadir ya karasa yana kallon Yassar din
"Nikam kabar maganar kudin nan, kayi zuru-zuru, duk azumin ne?"
Kai AbdulKadir ya girgiza ma Yassar din
"Banajin dadi Hamma, kirjina ciwo yake mun"
Cike da damuwa Yassar yace
"Ko zamu koma asibitin ne?
Kaga shisa suka so ka kwana rannan dan suga yanayin jikin, kuma baka shan magungunan ko?"
Numfashi AbdulKadir ya sake saukewa, kafin ya sauke muryar shi yana fadin
"Na saki Nuriyya...
Saki uku"
Cike da rashin fahimta Yassar yake kallon shi dan kamar daga sama haka yaji maganar
"Bangane ka saketa saki uku ba, baka da hankali ne kai?
Ina tunanin ka ya tafi?
Rashin hankalin naka har yakai haka"
Kai AbdulKadir yake girgiza mishi
"Baka san me tayi mun ba Hamma, baka tambayi me tayi mun ba, kar kaimun fada bakaji duka abinda ya faru ba"
Sosai Yassar yake kallon AbdulKadir din, sam baiji dadin jin maganar ba, badan yana son Nuriyya ba, sai dan saki abune mai girman gaske
"Koma me tayi maka, shisa addini ya bada maslaha akan ka fita kabar mata gidan idan kaga zata tunzuraka, karka yanke hukunci sai ka samu nutsuwa ka sauka daga fushin daka dauka.
Macece ita, ba ko yaushe take da hankali ba, komai ya fito daga bakinta fada maka zatayi"
Shiru AbdulKadir yayi, dan maganganun Yassar din ciwon da yakeji suke kara mishi, cikin taushin murya Yassar yaci gaba da fadin
"Nikam sam banji dadi ba, kuma baka kyauta mun ba Wallahi, na dauka munyi magana ta fahimta akan wannan zuciyar taka da rashin neman shawara"
Wani abu AbdulKadir ya hadiye da yai mishi tsaye a wuya
"Kayi hakuri"
Ya fadi yana sa Yassar din kallon shi, yanayin AbdulKadir din na karya mishi zuciya, da kaga alamun shi kasan yana cikin jimamin rabuwa da Nuriyya din, amman kaddarar suce tazo da haka.
Da yawan lokutta mutane biyu kan hadu dan su koyar da juna wani darasi kafin kaddara ta raba hanyar su, hakan ne abinda ya faru da zaman AbdulKadir din da Nuriyya
"Allah yasa hakan shine mafi alkhairi"
Cewar Yassar yana dorawa da
"Karka saka damuwa sosai a ranka, babu wanda yake wuce kaddarar shi, yin aure da mutuwar shi lokaci gare su, Allah bai nufi zamanku zai tsawaita ba"
Kai AbdulKadir din ya jinjina
"Hakane Hamma...
Nagode"
Sallama Yassar din yai mishi, babu yanda baiyi da ya sauke shi gida ba, amman yaki, cayai yaje ya kwanta ya huta, yana bukatar ya samu wadataccen hutu.
Bai wani ja maganar ba, dan kan shi ciwo yake sosai, har bakin kofa dai ya raka Yassar din tukunna ya dawo yana shiga gida da sallama.
Baiga Waheedah a falo ba, hakan yasa shi ya wuce cikin daki ya sameta a kwance.
Kan gadon ya karasa ya dauki Imaan dake bacci yana sauketa kasa kan nata gadon, ya matsa sosai ya rungume Waheedah ta baya yana sauke wani irin numfashi da baisan yana rike da shi ba.
Hannunta ta dora kan nashi dake cikinta, tana lumshe idanuwanta, tana jin yanda zuciyarta ke bude mata duk wata kofa da ta taba son shi hadi da dokawa da karfin gaske, tana jin yanayin kaunar shi da kusancin shi da ita hakane kawai yake haifar da ita, tana jin yanda tayi kewar yanayin sosai.
"Sadauki"
Ta furta cikin yanayin daya manta rabon da yaji ta fadi, da sauri ya kamata yana juyo da ita, sosai yaji dadin hasken da yake gauraye da dakin, idanuwanta yake kallo yana ganin soyayyar shi a ciki, yana ganin yanayin daya manta rabon daya ganshi a tare da ita.
Wata ajiyar zuciya ya sauke yanajin ciwon da yake ji ya rage mishi, rungumeta yayi sosai a jikin shi
"Nagode..."
Ya fadi batare da yasan dalilin yin godiyar ba, kawai ya tsinci kan shi da son yi mata godiyar ne.
Dumin jikin shine taji kamar ya wuce misali, hakan yasa ta taba wuyan shi, tana sauko da hannunta ta saka cikin rigar shi tana taba jikin shi sosai
"Zazzabi kakeyi"
Ta furta tana dago kanta daga jikin shi tana kallon idanuwan shi da yake kara kankance mata
"Tashi ka sha magani"
Dakuna fuska yayi yana girgiza mata kai
"Ba zazzabi nakeyi ba, banajin dadine kawai"
Dan daga mishi girarta tayi duka biyun, duk da sanin dalilin rashin jin dadin nashi na saka wani irin kishi naban mamaki tsirga mata
"Shine zazzabin ai, kaci abinci?"
Kai ya sake girgiza mata
"Banajin yunwa, na sha shayi a wajen Hajja"
Wannan karin zame jikinta Waheedah tayi daga nashi
"Kaje gidan shine baka taho da Fajr ba Sadauki?"
Hararta yayi
"Nine bani da kunya ai, kije ki dauko shi da kanki"
Murmushi tayi kawai tana sauka daga kan gadon
"Karki wahalar da kanki, ni babu maganin da zan sha"
AbdulKadir ya fadi, komawa kan gadon tayi tahau tana saka hannunta cikin aljihun shi ta dauki mukullin motar shi, Hajja tace mata yana asibiti rannan, ta tabbatar an bashi magunguna, suna mota dan inya shigo dasu gida zata sa yasha.
Aikam magungunan ta dauko a mota tana dawowa dasu dakin ta ajiye kan gado
"Bafa zan sha magani ba saboda lafiyata kalau"
Har lokacin batayi mishi magana ba, fitowa da magungunan tayi kala hudu, akwai paracetamol a ciki, shi kadai ta ballo guda biyu tana sakawa a hannunta ta mika mishi, akwai ruwa a roba kusa da ita data shigo dashi ta dauko ruwan, kunshin hannunta yake kallo, shiyasa shi karbar maganin yana hadawa da hannunta ya rike
"Ka sha dan Allah, shi kadai ne ai"
Dauke idanuwan shi yayi daga hannunta yana sauke su cikin nata
"Bazan sha ba gobe"
Yai maganar cike da tabbaci, kai kawai Waheedah ta daga mishi, tana kallon shi ya shanye maganin yana hade fuska kamar zai amai, sosai ya dakuna fuskar shi yana turo mata labban shi, murmushi kawai tayi, fushi yake dole saboda tasa shi yasha magani.
Ko Fajr inta bashi magani da kuka da komai yake sha, ko AbdulKadir din yana nan baya tayata, ca zai mata magani bashida dadi.
Tsaf halayen shi yaron ya kwashe.
Bata matsa mishi yaci abinci ba, dan tasan in har da kanshi zaice mata bayajin yunwar to bazai iya cin abincin bane ba.
Ita ta kashe musu fitilar dakin tukunna tahau gadon, duk da tana rike a jikin shi, ko kadan ya nemi bacci ya rasa, ita kanta ba baccin takeyi ba, rashin baccin shi ya hanata yin nashi, suna kwance har karfe uku kafin su tashi su karasa raya daren ta hanyar gabatar da sallolin nafila.