Sashe 2
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mami Paapi ne..."
Wani irin shiru ya biyo bayan maganar yaron, shiru ne da hayaniyar shi tafi ta surutu, dan ko wani yazo wucewa shirun da yake wajen zai iya taba shi, dakuna fuska Abdulkadir yayi yana son nemo kalmar abinda ya lullube shi.
'Kunya'
Wata murya ta furta can kasan kwakwalwar shi, sai dai shida kunya nada wata irin tazara da bazata misaltu ba, bata taba kamo shi ba ko acan ba, baisan ma ya akan jita ba, kai tsaye yake dukkan al'amuran shi, yau kam ba kamoshi kawai tayi ba, lullube shi tayi ruf, bargon rashin gaskiya mai kaurin gaske na bin bayanta, numfashin shi ma kamar a lissafe yake jin fitar shi.
"Mami kinga abinda nake ce miki ko?"
Aminu ya fadi yana korar shirun da yake kewaye da wajen.
"Aminu..."
Mami din ta kira cike da kashedi, akan ce yaro baya karya, musamman mai karancin shekaru kamar Fajr, sai dai yaran yanzun kuruciyar su cike take da abin mamaki, bakomai daya fito daga bakin su bane abin yarda, hakan shine take ta fadama kanta dan karta yarda da abinda Fajr din ya furta, duk da yanayin Abdulkadir din ya gasgata maganganun yaron nashi, amman batason ta yarda da hakan.
Sam bata kula da girgiza mata kai da Aminu yake ba saida yace
"Karki ce inyi shiru wannan karin ma, kina jin abinda Fajr ya fadi, Wallahi na jima da sanin Hamma Abdulkadir ne ajalin Adda Wahee..."
Cikin tashin hankali Mami ta kalli Aminu din, yanayin kallon na sakashi kasa karasa maganar da yake, dauke idanuwan shi yayi daga kanta yana watsa ma Abdulkadir da yake tsaye wata irin harara, wani daci Aminu yake ji a kasa makoshin shi, ba tun yanzun Abdulkadir ya gama ficewa daga ranshi ba, Mami nace mishi Waheedah ta fadi ta fasa kai ya san Abdulkadir nada hannu dumu-dumu cikin faduwar tata, sai dai ko kadan bai hango sanadin zai zamana da hannun shi ba, ya dauka bacin ranshi ne ya sata faduwa tunda duk sun san tana da hawan jini.
Da yana da iko kan igiyar auren Waheedah da Abdulkadir da tuni ya sa almakashi ya datse ta, datsar da babu hanyar da za'a abi a sake daurata har abada.
"Hamma..."
Zainab ta kira cike da wani yanayi dayasa Abdulkadir din sake kasa da kan shi, dan koya dago ma bashi da kalaman dazai musu amfani dashi, baisan me zaice musu ba, yawan magana ba dabi'ar shi bace ba tunda can, ko da yana da abin fadi kuwa, ballantana yanzun da babu abinda yake so kamar kasa wajen ta bude dai-dai inda yake tai kasa dashi.
Kafin ta sake cewa wani abu likitan ya fito daga dakin da Waheedah take, wasu Nurses guda biyu na biyo bayan shi.
Idanuwan shi ya sauke kan Abdulkadir, sai dai kafin yace ya bishi office kamar yanda Mami tasani ta riga shi magana da fadin
"Ni mahaifiyar tace, wannan kannen tane, duk abinda zaka fada mishi zai mai-maita mana ne, gara ka fada anan din kawai..."
Abdulkadir din dai likitan ya sake kallo, kai yadan jinjina mishi a hankali yana bashi izinin yin magana, numfashi ya sauke tukunna yace
"Babu wata matsala In shaa Allah, munyi mata karamar tiyata saboda buguwar ta shiga sosai...badai yanzun zata tashi ba, amman zaku iya shiga ku ganta, banda yawan surutu dan Allah, kar a tasheta, tana bukatar hutun sosai ko dan jininta da ya hau fiye da na da..."
Kai Mami ta jinjina tana mishi godiya tukunna ya wuce, hannun Fajr ta kama tana raba Abdulkadir ta shiga cikin dakin, daga inda take tsaye tana hango ramar da Waheedah tayi, tayi wata irin ramewa da duk da idanuwanta a rufe suke kana ganin ramin da yake kasan su, kanta nannade yake da bandeji, hannunta daure da karin ruwa.
Wani irin abu Mami taji ya matse a cikin zuciyarta, a hankali ta taka tana jan kujera ta zauna, ta dora Fajr kan cinyarta.
Hannu yaron yakai kan jikin Waheedah
"Omma..."
Ya fadi, Mami na kama hannun shi ta janye
"Karka tashe ta Fajr, bacci take kaji..."
"Ni zan sha ruwa..."
Fajr ya fadi yana sa Mami din juyawa ta kalli Aminu da suma duk sun shigo dakin.
Kafin tayi magana Salim yace
"Bari in karbo...
Ruwan kawai ake bukata?
Ko zan taho da wani abin..."
Waheedah ta kalla, tasan babu abinda Abdulkadir ya dauko, hakan yasa ta fadin
"Ka fara kawo ruwan dai, sai kazo kuje gida kai da Zainab akwai yan abubuwan da zaku dauko mana..."
Kai Salim ya jinjina mata yana juyawa ya fice daga dakin.
A bakin kofa yaga Abdulkadir a tsaye, kallon shi kawai Salim yayi yana girgiza kan shi, tukunna ya wuce, kan kujerun da suke wajen Abdulkadir ya karasa yana zama, yau gabaki daya nasa shi jin abubuwan da yake tunanin yayi bankwana dasu shekaru da dama da suka wuce, yanzun kallon da Salim yai mishi yasa shi jin wani irin abu na lullube shi, so yake yaga halin da Waheedah take ciki, amman ya kasa shiga dakin, kunyar hada idanuwa da Mami yake ji, bazai iya shiga in tana nan ba.
Kanshi ya saka cikin hannuwan shi yana dafewa.
Tunanin barkatai na soma kawo mishi ziyara.
Salim na kawo ma Fajr ruwan suka juya su duka ukkun, harda Aminu, dan Fajr dinma manne musu yayi, dole ta karbi Ikram daga hannun Zainab, towel din da yarinyar take ciki tayi amfani dashi ta goyata.
Tukunna ta danyi dabara ta zauna kan kujerar dakin, tunda ta rubber ce.
Shisa tace har babbar darduma a dauko musu.
Sosai ta nutsar da hankalin ta kan Waheedah, hannunta da ya kara zama siriri, daman abinka da ba qibar kirki ba, yanayin kaddarar yarinyar nasa idanuwan Mami din cika taf da hawaye.
Tana da hakuri da kauda kai tasani, amman na Waheedah yayi yawa, ita ko baki ba zata iya budewa tace ana mata abu ba, in kuma ka tambaya murmushi kawai takanyi
'Mami rayuwar duka babu yawa, komai zai wuce kamar bai faru ba'
Shine maganar ta a ko da yaushe idan kaso sanin halin da take ciki, da ba'a ganewa in baka kula da yanayin ramewar da take a tsaye, ko murmushin ta da baya kaiwa cikin idanuwan ta ba, to ita dai kam Mami zata iya cewa tun yawon arba'in din Ikram da tazo musu rabon da ta sakata a idanuwan ta, sai dai a waya, ta kuma hana su Aminu kawo mata zancen gidan Waheedah din, dan haka ko sun kula da wani abin in sunje ba zuwa suke suna fada mata ba.
Batasan iya lokacin da ta dauka a zaune a wajen ba, sai da taji sallamar su Zainab din, amsawa tayi a hankali, yawan su na bata mamaki, kusan su duka gidan suka dawo, kasa-kasa suke magana, tarkacen da taga sun kwaso zaka rantse watanni zasuyi a asibitin, da alama abincin ranar da duk basuci bane ba zasuci shi yanzun a asibitin.
Kujera Zainab ta mikoma Anty, dan a wajenta ma sukaje suka amshi abinci suke fada mata Waheedah na asibiti, ta biyosu suka taho tare.
"Haj.
Halima wai dagoki sukayi kenan"
Mami ta fadi, Anty na zama da fadin
"Ai baki kyauta mun ba, ko ba zaki shigo ki fadamun Waheedah na asibiti ba ai saiki aikomun ko?
Ke ce zaki kwana da ita?"
Murmushi kawai Mami tadan yi, daman tayi niyyar Zainab ta kwana ne, ita da dare saita tusa su Aminu a gaba, kirkin Anty bazai gaji da bata mamaki ba.
"Ya jikin nata?"
Anty ta tambaya
"Gata nan dai bata tashi ba har yanzun..."
Mami ta fadi, su Nabila da suka fara fada da Salim Anty ta kalla
"Zanci ubanku wallahi, ku kamar kaji bakwa zama waje daya?"
Harara Salim yake watsa ma Nabila
"Anty hannuna ya fara taba plate din..."
"Ni na riga gani, Anty kice yabarmun suci dashi da Aminu..."
Nabila ta fadi a tabare, Salim na samun damar fisge plate din.
"Kuci tare ke da shi..."
Shagwabe fuska Nabila tayi, idanuwanta na cika da hawaye
"Ni bazan ci dashi ba"
Numfashi Anty ta sauke
"Na sake magana akan ku saikun koma gida, tunda ba yara bane ku, da ina sanyin surutu dana taho da Albarkah..."
Sanin halinta yasa suka nutsu, tare suka zuba abincin, tana kallo suna kaiwa cokulan juna karo, dauke idanuwanta tayi daga kansu, dan sun saba, kullum cikin fada suke, ko makaranta zasu je haka suke kamar kaji, kuma ta rasa kalar fadan nasu, randa ya jibgeta kuma tana kuka haka zata bishi su tafi tare.
Indai kace zaka shiga rigimar su kaine zaka sha kunya.
"Ikram ce kika goya haka?"
Anty ta tambaya tana daga hijab din Mami, taga yarinyar ta farka tana ta kalle-kalle.
"Idon ta biyu ma..."
Cewar Anty
"Ikon Allah..."
Mami ta fadi tana mikewa ta kwance goyon tana sauko Ikram
"Ke baiwar Allah babu magana..."
Inji Mami tana gyarama Ikram din zama, da alamu hakurin mahaifiyarta ta biyo, sam yarinyar bata da rigima, ruwa ta karba ta zuba a murfin tana ba Ikram din
"In kuma basa ba yar su ruwa fa?"
Anty ta bukata
"Nidai ai na bata, wannan shirmen nasu na zamani ba dani za'ayi shi ba, cikin su babu wanda ba'a bama ruwa ba, meya same su?"
Dariya Anty tayi
"Ni kaina bazan iya ba wallahi, gani nake daukar alhaki ne..."
Hira suke a hankali a hankali, Anty ita tasa Mami dan tsakurar abinci, dan damuwa ce fal ranta.
"Ba za'a zuba a mika ma Abdulkadir ba kuwa?
Yana wajen nan"
Mami ta fadi tana sa Anty kallon ta
"Ni rabani da wannan dan Allah, ya koma gida yaci wajen dayar matar shi, ban zubo abincina da shi ba nikam"
Shiru Mami tayi, sai dai duk yanda taso ta nuna halin ko in kula da Abdulkadir din sai ta kasa, Ikram ta mikama Anty tana mikewa ta taka zuwa kofa tasa hannu ta bude dakin tana leqa kai, yana zaune kuwa ya hade kanshi cikin hannayen shi.
"Abdulkadir..."
Ta kira a hankali tana kallon yanda ya dago kai, idanuwan shi sun sauya launi.