Sashe 89
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na fada miki ki tauna maganar da zaki fadamun baki jini ba, uban me yasa ni da gidana ba zan ajiye kudi inda nake so ba?
Me yasa zaki dauka?
Me yasa zaki daukar mun?
Rashin hankalin ki bai fada miki kudin zai iya kasancewa ba nawa bane?
Ban nuna miki salary dina ba Nuriyya?"
Ba sosai take jin maganganun AbdulKadir din ba duk da hargowar da yakeyi kamar kiris yake jira ya rufeta da duka
"Abinda nake miki bai isheki ba sai kin daukar mun kudi?
Kin dauka ban san kina zarar mun ba duk idan na ajiye?
Ban miki magana bane saboda ina guje mana zuwa inda muke yanzun.
Kinsan kudin wa kika dauka?
Kinsan kunyar da kika sakani a ciki?
Me kike so in ce mishi?
Ni na dauki kudin?
Ko ke kika dauka?
Me yasa zaki mun haka?"
Zuwa lokacin radadin da take ji ya fara yin kasa, sai hawayen bakin cikin da suke silalo mata suna busar da tsoron shin da takeji, tunda ba mala'ikan mutuwa bane ba, ta dauka yafi karfin dubu arba'in da biyu da har zai zauna yana mata tijara akan su
"Ni na dauka, saboda na tambayeka ka hanani shisa nagani na dauka, me yasa kai baka fadamun ka ajiye kudin ba?
Me yasa kai baka fadamun ba naka bane ba?"
Nuriyya ta tambaya cike da tsantsar rashin kunya tana saka wani murmushin takaici kwacema AbdulKadir din
"Akan dubu arba'in da biyune zaka mareni?
Ni ba jaka bace da zan zauna kana jibgata"
Kai AbdulKadir ya girgiza, idan yana ganinta a gaban shi, idan taci gaba da magana zai daketa saiya ji wani daga cikin kasusuwan ta yayi kara alamar karyewa, zai daketa sai ta kasa ko nishi balle alamar kuka, ballantana ta sami bakin da zata tsaya tana kallon shi cikin idanuwa tana mishi rashin kunya, zai zabar musu abinda zai fi musu sauki, muryar shi a hankali ta fito kamar yana dandana duka kalaman shi
"Kije gida Nuriyya, kije gidan ku ki dan huta, nima in huta"
Sheqeqe Nuriyya take kallon shi, tana jin auren shi yau kamar sartse a makoshin ta, bambancin su da Anas na bayyanar mata
"Ni babu inda zanje babu wata shaida, sai inje musu saqaqa ince me?
Yaji na yo?
Ka sakeni mana sai in tafi da Hujja"
Ta karashe maganar tana watsa mishi wani kallo kafin ta dora da
"Ni ba kai bane mijin dana dauka na aura, ba haka Waheedah take fadarka ba, ba haka take nuna ka ba"
Da mamaki AbdulKadir yake kallonta
"Kin aureni akan abinda Waheedah take fada ne daman?"
Dan sosai yake son ya kwantar da bacin rai ya fahimci maganganunta, amman su kansu tunzura shi sukeyi, ba shi ta aura ba, mijin Waheedah ta aura shine abinda take son fada mishi.
"Me zanyi da kai?
Wallahi AbdulKadir ba kai bane mijin da nake burin aure, kudinka da halayenka basuyi mun ba, ba zan iya zama da kai da wannan bakaken halayen ba"
Nuriyya ta karasa maganar tana jin zugin da kuncinta yake na marinta da yayi, garama ya saukake mata auren shi, Asma tace mata da kyawunta ta zauna namiji na wahalar da ita, kuma gaskiya ne, in yau ta gama iddarta tana da tabbacin samarine zasu dinga mata layi.
Numfashi AbdulKadir yake ja yana fitarwa idan taci gaba da magana tabbas zai datse igiyar dake tsakanin su, maganganun da take fada din na kara tunzura shi sosai da sosai, dan bai kara sanin yanda zuciyar shi take doka mata ba sai yanzun da take fada mishi maganganun da yasa shi jin kamar ita din bata taba son shi ba.
Abinda take tunanin auren shi zai samar mata shi take so.
Abinda taga kamar auren shine ya samarwa Waheedah shi ta biyo.
Lokutta da dama kuma ba mata kawai ba, har maza na wannan wautar, ba a karin mata ta biyu ba maza kanyi kuskuren nan, a ta farkon ma, da yawa kan dauka auren wata mace shine cikar farin ciki, idan har baka da farin cikin da kaine silar samarwa kanka shi, cikar shi zatayi maka wahala idan wani ya zama sanadin farin cikin ka, ko da zama na yau da gobe bai taba wannan farin cikin naku ba, rabuwa ta kaddarar rayuwa ko mutuwa kan iya giftawa, sai kayi yaya?
Aure kan samar da farin ciki, amman baya nufin duka farin cikin naka zai zamana a zagaye da shi auren.
Mata sunfi kowa yin wautar nan, musamman a zamanin da muka tsinci kan mu a ciki.
Zamanin da yasa idan mace ta samu jinkirin auren da ba laifinta bane za'a dameta da yawan surutai har ya sata jin yin auren ne kawai hanya daya ta samun farin ciki, a wasu lokuttan kuma idan yarinya bata tashi cikin wadata ba, bata kuma da wadatar zuciya sai ta dora ginshiqin aurenta da samun farin ciki akan auren mai kudi, wasu kuma hange-gange shine yake halakar dasu, kinga mace cikin rufin asiri, kinganta daga sama da mijinta suna cin me kyau su sha me kyau, sai wannan kyallin ya haska miki shi, sai kiga kamar ta samu duk wani abu da shine burinki a zaman aure.
Bakisan yanda zaman aurenta yake tare da mijinta ba, bakisan me take jurewa ba, bakisan shima me yake jurewa a zama da ita ba, zamantakewa ta tsakanin ma'aurata sirrine da yake a lullube, abinda idanuwanki suka gani baya nufi shine komai, zai iya yiwuwa mijin wadda kika kyalla idanuwanki a kai bashi bane abinda burinki yake bukata.
Karki so mutum dan abinda kike tunanin kin ga matar shi ta samu a tare dashi, ko da zatonki ya zama gaskiya ba kida tabbas ke zaki samu irin wannan a tare dashi.
Duk da wasu matan ma na da laifin ganin mijin su nasu ne su kadai, wasu kance 'Ta auri mijin wata'.
Dan kawai ta shiga a ta biyu.
Babu wani abu mijin wata daga lokacin da musulunci ya halarta karin uku bayan ke tun kafin wanzuwarki, mijinki nata ne itama.
Wahalhalu da yawa mutane su suke dorama kan su ita, kwanciyar hankali baya zuwa idan baka neme shi ba.
AbdulKadir ko kadan bai zaci ta aure shi da wata manufa da ta wuce ta son zama dashi kamar yanda yake son zama da ita ba, shisa ya juya yana ficewa daga dakin.
Takawa yake dan ya fita daga gidan ya tafi wani waje, koma ina ne inda ba zaiga Nuriyya na wani lokaci ba kafin ta tunzura shi ya yanke musu hukuncin da su duka ba zai musu dadi ba.
Amman sai ta biyo shi, a falon Waheedah ta sake shi zai wuce ta gaban kitchen din shi tana kama mishi riga ta janyo shi saida ya juyo
"Nuriyyaa"
Ya sake kira cikin wani sabon kashedin, Waheedah taji takun tafiyar shi tun kafin ya fito, ta kuma ji muryar su dan tana hango kafar shi guda daya, da yake kujera ta saka ta zauna a kitchen din ta jingina bayanta da lokar kitchen din ta dora roba kan cinyarta tana gurza kubewa
"Ka dawo ka saukake mun wannan kaddararren naka, dan Wallahi ba zanje gidanmu babu wata shaida ba, ni dama nagaji da zama da kai..."
Numfashi AbdulKadir ya sauke ya kama hannunta yana banbarewa daga rigar shi yana fadin
"Kin gaji da zama dani right?
Ki jirani Nuriyya, duk mu huta da rashin albarkar da take bin mu"
AbdulKadir ya karasa dan shi kan shi yanajin yagaji da bala'in nan, yanzun nan kuma yanajin rashin albarkar iyaye ce take bibiyar shi shisa a kasa da sati biyu komai ya jagule musu shida Nuriyyar, shima a gajiyen yake jin shi, maganganun kowa da suka fada mishi sun tabbata, hankalin su ya kwanta, sai su kalli idanuwan shi suyi mishi dariya su fada mishi da yaji maganar su daga farko da baizo inda yake ba yanzun.
Dakin Waheedah ya wuce, Nuriyya na tsaye bakin kofar kitchen din Waheedah din tana girgije-girgije, ta wutsiyar ido Waheedah ta ganta, ko dagowa batayi ba, kubewarta take gurzawa a hankali tana bin karatun daya shigo na Suratul-Mulk cikin muryar Qari Sheikh Ghamdi da ke nutsar da abubuwan da batasan a tashe suke a tattare da ita ba.
Bata kalle su bane saboda basu bane a gabanta, saboda fadansu bai shafeta ba, asalima bata da alaka da shi.
Nuriyya na nan tsaye AbdulKadir ya dawo da takarda a hannun shi, dayan da biro rike, fuskar shi kawai zaka kalla kasan ran shi a matuqar bace yake
"Gashi nan, na sake ki saki daya"
Runtsa idanuwan ta Waheedah tayi tana jiran taji ko zata girgiza tare da abinda ya girgiza daga kalaman sakin aure da AbdulKadir ya furta, asalima tana bude idanuwanta ji tayi kamar tare da sakin Nuriyyar ya dauke mata wani katon dutse daga saman kai.
Nuriyya kuwa bata karbi takardar ba, kallon AbdulKadir din takeyi bata son sake hada wata hanya dashi ko ta wasa ce, wani auren zatayi na mai kudi inda ba za'ai mata tijara kan dubu arba'in da biyu ba
"Daka haifu cikin Hajja da ka karashe biyun ai, kaga duk sai ka hutar damu"
Sosai AbdulKadir yake kallon ta, a duniya babu wanda ya taba zagin shi haka, babu wanda ya taba kallon shi ya zage shi haka, saki daya ko uku, har a bayan zuciyar shi yanajin kamar yanda ya nuna babu wanda ya isa ya hana shi lokacin daya aureta, sai wata kaddarar da baiyi fata ba, haka yakejin yanzun ma babu wanda ya isa ya saka shi sake zaman aure da ita ko da su kadai suka rage a fadin duniya, saboda bayason gauraya yaran shi da matar da ta fada mishi maganganun da Nuriyya ta fada mishi.
Takardar ya yaga yana komawa cikin dakin, ko mintina biyu baiyi ba ya fito da duka littafin a hannun shi yana dago kafar shi daya ya dora littafin a jiki yai rubutu ya yago ya mika mata.