Sashe 74
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Duk wannan kishin da yake nuqurqusarta, da gajiyar da take fadin tayi, zaka fahimci yanda rabuwa da AbdulKadir shine karshen abinda take son yi...!
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
#LubnaSufyan
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Cikin baccin da baisan lokacin daya dauke shi ba yaji wayar shi na ruri, idanuwan shi a rufe ya lalubota, har kiran ya yanke, numfashi ya sauke yana dora wayar a kirjin shi hadi da gyara kwanciya.
Wani rurin yaji wayar ta sake dauka, dakyar ya bude idanuwan shi yana ganin Nuriyya ce, dagawa yayi ya kara a kunne batare da yace komai ba
"Masoyi..."
Ta kira ta dayan bangaren, shirun AbdulKadir ya sakeyi, sosai ta bata mishi rai, Waheedah ce a tunanin shi da komai shisa baiyi lokacinta ba har yanzun
"Hello..."
Ta sake fadi, muryar shi can kasan makoshi cike da bacci yace
"Ina jin ki"
Ya lumshe idanuwan shi da suke mishi yaji saboda bacci
"Naga baka dawo ba har yanzun...
Dan Allah kayi hakuri..."
Ta karasa maganar muryar ta na karyewa
"Ina gida ni tun dazun"
Cewar AbdulKadir din yana ganin rashin hankalin Nuriyya da zatayi tunanin dan ta bata mishi rai zai tafi wani wajen, a lokaci daya kuma yana ganin yanda har yanzun bata san wa take aure ba, jin tayi shiru yasa shi fadin
"Kiyi bacci, sai da safe"
Kafin tace wani abu ya kashe wayar shi.
Bai taba zaton akwai ranar da matar shi zata bata mishi rai harya raba shimfida da ita ba, duk fadan da zaiyi da Waheedah in dai suna gida daya a jikin shi take bacci, ko baya mata magana kuwa.
Numfashi yaja yana sauke shi, kirjin shi zafi yake sosai, tunanin Waheedah din yanzun ya kara taso mishi da wata irin kewarta.
Wayar shi ya duba yana ganin karfe sha daya na dare, karamin tsaki yaja, dare ma baiyi ba sosai, ga baccin gabaki daya yabar idanuwan shi.
Lambar Waheedah ya kira a kashe
"Dan Allah ki kunna wayarki, ba sai kin daga ba Wahee, ko ringing din naji a kunne na zan dan samu nutsuwa"
AbdulKadir ya fadi yana sake gwada kiran wayar, a kashen dai ya sake ji, tashi zaune yayi ya jingina bayan shi da jikin gadon.
Dayan pillow din ya dauka yana dora shi kan cinyar shi.
Bude wajen text yayi yana rasa abinda zaice mata, ko da can kalaman shi taqaitattu ne, balle yanzun kuma.
Fasa tura mata yayi yana scrolling can sama, tsofin sakunanta ya dinga karantawa, duk yawan da suke dashi sai yaga sun kare mishi da wuri, WhatsApp ya koma yana jin dadin yanda baya goge chat, dan lokutta da dama ita take goge mishi in ta dauki wayar, sai tace yana cika waje.
Danma ya hanata goge mishi nasu, tunda idan yana wajen da babu network su din yake karantawa suna rage mishi kewarta.
Lokacin da yabi duk wani text dinsu ya gama karantawa karfe biyu saura.
Duniyar yakeji ta mishi wani irin fadi, ga kadaici naban mamaki daya lullubeshi, da yanajin nutsuwa sallah zaiyi har gari ya waye, amman bashida wannan nutsuwar.
Saukowa yayi daga kan gadon yana fita daga dakin zuwa bangaren Nuriyya.
Bacci ya samu tanayi hankalinta a kwance, shi yace tayi bacci da kan shi, baisan me yasa baccin ya bata mishi rai ba
'Kin batamun rai, bana tare dake shine kikayi bacci kika barni'
AbdulKadir ya fadi a ran shi yana girgiza kai, bandaki ya wuce ya watsa ruwa.
A rayuwar shi baya hada wani da wani, hakan na cikin abinda bayaso sam, ko fada Hajja take mishi ran shi yana baci yaji tana kwatanta shi da wani.
A wajen shi Allah ya halicci mutane daban-daban mabanbanta halaye da ra'ayoyi, har kamanni ma, wanda Allah ya halitta yan biyu sukazo da kamanni daya, suka kwanta a ciki daya ma saika sami halayensu daban.
Sai gashi yanzun daya fito ya tsinci kan shi da hada halin Nuriyya da na Waheedah a waje daya yana aunawa, Waheedah ba zata taba bacci tabarshi ba, ko da shi ya bata mata rai, a yanda zata dinga kallon shi da idanuwanta kawai zaka gane babu nutsuwa a tattare da ita.
'Na baka hakuri fa Sadauki, kai mun magana dan Allah, wallahi a takure nake jina, ni banason yin fada da kai'
Kalamanta suka dawo mishi
'Hamma har yanzu fushi kake mun?
Babba da hakuri aka san shi'
Takance, duk idan tayi amfani da Hamma to ya kwana yana mata fushi, ko tana son tambayar shi unguwa, zatace shifa Yayanta ne.
Murmushi yaji ya kwace mishi, kafin kirjin shi ya sake amsawa kamar zai bude, har zazzabin rashinta a kusa dashi yake ji.
Sai da ya sake komawa bangarenta ya sakko gajeran wando da singlet tukunna ya dawo dakin Nuriyya din, baccin da take zai hana mata, tunda shi ya kasa, kuma bayajin tunanin Waheedah zai barshi ya samu.
Da safe dakyar Nuriyya ta tashi sallar asuba, tana ta turo baki saboda baccin dake idanuwanta, bata kwanta da wuri ba, idan tace dan bai dawo bane karya take, kallo takeyi a system dinta suka dauke wuta, bata tuna dashi ba sai da chargyn system din ya kare, kudine ta riga ta kashe, fada ne zaiyi ya gama.
Ita ko kadan batama hango zai mata fada akan dubu arba'in ba, yanda take ganin kudin shi, yafi karfin dubu arba'in, idan nashi ran ya baci itama natan a bace yake.
Data kirama yace tayi bacci tana kashe wayar guntun tsaki taja ta ajiye ta kwanta, daman ko baice ba baccinta zatayi.
Dan tunda harya dawo daga ko ina Major ya kaishi bai mata fada ba wani abu ya nutsu a ranta.
Batajin akwai wani babban abu da zatayi mishi kuma da zai kai wannan, iya kacin shi fada, duk da fadan na tsaya mata a rai, in yayi yagama shikenan.
Ta kula bashida riko, da wahala ya kwana yana fushi kan abu daya.
Tana idar da sallah ta janyo wayarta, chajin taga saura goma, dan ta manta ta saka sanda aka kawo wuta.
Haka kawai tunanin azumi da saura kwana biyu ya diro mata, wayar AbdulKadir din da take kan drawer din gado ta janyo, ta saka sunan Waheedah a cike taga bai bude ba.
Tasan dai duk password din shi baya wuce sunanta, dan waccen wayar daya sake haka password din yake, har wani daci-daci take ji duk idan ta dauki wayar shi, shisa yanzun taji zuciyarta tayi wani tsalle da tunanin ko sunanta ya saka, jikinta har bari yake lokacin da ta saka sunanta, sai taga wayar bata bude ba, kamar daga sama taji sallamar shi yana dorawa da
"Me kike mun da waya?"
A dan tsorace ta daga kai tana sauke idanuwanta cikin nashi daya kankance mata
"Bakomai, zan duba abune, nama kasa budewa kuma"
Gira daya AbdulKadir ya daga mata dan baiga abinda ta ajiye a wayar shi da zata duba ba, hakan ta kula dashi yasa ta dora da fadin
"Hotuna zan kalla fa, wayata babu chaji, ban saka ba na manta"
Karasawa AbdulKadir yayi yana hawa gadon
"Ko gaisheni bakiyi ba kike son cinyemun chajin waya"
Murmushi Nuriyya tayi mishi tana matsawa sosai ta kama hannun shi
"Ina kwana"
Kankance mata idanuwa AbdulKadir yayi
"Waheena"
Ya fadi yana zare hannun shi daga cikin nata yaja kafafuwan shi ya hau dasu kan gadon, cike da rashin fahimta
"Password din"
Ya fadi yana kwanciya ya lumshe idanuwan shi, Nuriyya tabi shi da kallo yanda yake shirin komawa bacci kamar bai fada mata abinda taji dacin shi ya taso daga kasan zuciyarta zuwa makoshinta ba.
Har wani hucin bacin rai takeji kamar kububuwa, AbdulKadir kuwa baccin shi ya koma, yana barin Nuriyya nan zaune ranta in yai dubu a bace yake.
Dan kamar ba zata bude wayar ba, kafin ta yanke hukuncin Waheedah ba zata hanata latsa wayar AbdulKadir din ba, tunda yanda takejin mijinta ne itama haka takeji.
Kuma tana so ta shiga messages din shi harna whatsapp taga ko yaushe Waheedah zata dawo.
Wani malolon takaici ya sake taso mata, ganin saita kara saka wani password din tukunna zata iya gani, gashi lambobine wannan karin, hakura tayi tana shiga wajen kira taga ko yayi magana da Waheedah.
'Matar Sadauki'
Sunan farko data fara cin karo dashi a jerin wajen kiran wayar AbdulKadir yaso wanke mata bacin ran da takeji, kafin ta kula da kiran fita yayi ba shigowa ba, tana kuma ganin
'Nuri'
Daga kasa, wannan karin wani irin tsakine ya kwace mata, fita tayi tana kara kula da wallpaper din AbdulKadir din, hoton Fajr ne daya sata jin son samun nata yaron taso mata yana zuwa mata wuya, ba sosai takanyi tunanin samun ciki ba, amman duk idan taga giccin Fajr tanajin kamar ace yaron nata ne.
Kulle wayar tayi zata ajiye taga hoton dake fitowa idan an kulle waya kunshine, daga yatsun ta gane hannun Waheedah ne.
A gefen AbdulKadir ta ajiye wayar tana addu'ar ya mirgino ya dora mata nauyi screen din ya samu matsala ko zai rage mata takaicin da take ciki.
Mikewa tayi ta cire hijabinta, kan gadon tahau daga can karshe ta kwanta, banda tafasa babu abinda ranta yake, kafin ta matso tana kwanciya jikin AbdulKadir din da Waheedah takeyi kamar nata ne ita kadai, sai dai duk yanda bacci bai wadaceta ba, ta kasa samun shi, data rufe ido hoton hannun Waheedah ke mata yawo da sunanta da take da tabbacin ita tayi saving din lamba dinta a haka a wayar AbdulKadir din, saboda rashin aji, ita ba zatai haka ba da ta dauki wayar AbdulKadir din tana sake nata sunan zuwa
'Matar Masoyi'
Da tunani barkatai a ranta, dukkan su suna hadewa sukai mata wani irin zafi lokaci yake ta tafiya, wutar da aka kawo yasata sakkowa daga kan gadon.
Chaji ta fara sakawa tukunna ta shiga wanka ta fito, gaban mudubi ta zauna ta tsara kwalliya sosai a fuskarta, bum short ta saka da wata karamar riga, tana samun hula ta saka a kanta.