Sashe 11
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da yanzun kin kai kitchen, kiyi sauri, wallahi kikai latti ubanki zanci"
Uniform din ta ajiye akan kujera tana nufar kitchen, tasan da gaske yake, zai iya yana gama cin abincin shi ya fita Islamiyyar, tana da tabbacin zai iya riganta zuwa, kuma babu abinda zai hanashi dukan ta, fiye dana kowa ma, dan in ya tare latti su gefe yake sawa su ware, in yaima sauran bulala biyar-biyar nasu sai yakai goma.
Wani lokacin zata rantse da Allah yanayin murmushin shi yakan canza duk idan ya kama wani ya zane, kamar akwai nishadi na musamman da duka yake samar mishi.
Lokutta da dama ko fada Hajja tai mishi akan su yake huce wa, motsi ma in kayi bai mishi ba zai iya ja maka duka.
Sai dai yana da wani hali daya, babu wanda ya isa ya dake su a waje, babu malamin da baisan rikicin Abdulkadir ba duk Islamiyyar, tun baikai haka ba, hannunsu yake kamawa har inda malamin da ya dake sun yake ya tambayi dalilin da zaisa yai musu kalar dukan dayai musun, tun ana bashi suspension, har suka gaji da halin shi suka kyaleshi, su da kansu basa son a dake su ya sani, basama fara zuwa suyi labarin inda zaiji.
Kan kujera ya samu waje ya zauna yana jiran Zahra ta dafa mishi taliyar ta kawo.
Yau bata jira kowa a gidan ba, dan ranta kal take jin shi, tunda Mami ta siyo musu sabon takalmin makaranta ita da Amatullah, ta tambayeta ko zata iya bama Nuriyya wancen natan, dan kafar su daya.
Kai kawai Mamin ta daga mata, dan tasan ko ta hanata ma a sace zata dauka ta bata.
Da takalman da atamfar da wata yar uwar su Mami ta bata, taqi rabawa da Amatullah ta roki Ammi din ta kara siya musu wani yadi aka dinka musu doguwar riga ita da Nuriyya, duka ta hado ta saka a leda tana shiga gidansu Nuriyya da yake liqe jikin nasu, ba wani babban gida bane, daki ukune a cikin gidan, Nuriyya ce babba a gidansu, kuma yarinya kwalli a wajen mahaifiyarta da Allah yai ma rasuwa wajen haihuwarta din, tana da kannai guda hudu yanzun haka da matar babanta ta haifa dashi, ga cikin na biyar a jikinta.
Zakai karya idan kace Mama kamar yanda su Nuriyya suke kiran matar baban nata Maryama tana musguna mata, da zuciya daya matar take rike da ita, wanda abune mai wahalar samu a wannan zamanin, yanda mata suke musguna ma yaran mijin su da zaman kishi sam bai ma hadasu da iyayen yaran ba abune mai matuqar muni daya zama ruwan dare.
Sai dai Baban Nuriyya talakane sosai, dan sana'ar kanikanci yake a wani gareji, da kuma kacokan din sana'ar suka dangana, danma mutum ne da yake tsaye kan iyalan shi da dukkan karfin shi.
Waheedah zata iya cewa ta tashine taga Nuriyya a rayuwarta, dan a lissafi da akayi, wata daya Nuriyyan ta bata, kawancen su abune da zai baka mamaki, dan tunda karancin shekarun Waheedah ko abu aka bata saita tambaya ina na Nuriyya din, tun Mami na hanata shiga gidan su Nuriyya dan ita macece da batason tashin hankali a rayuwarta, harta hakura da taga kawancen na yarta da Nuriyya abune da kaddara ta hada.
Yanzun ma sallama ta rangada tana gaishe da Mama data amsa tana dorawa da
"Hassanar taki na ciki..."
Dariya kawai Waheedah tayi tana wucewa ta nufi dakin su Nuriyyan.
Abba shiya fara musu tsokanar nan ita da Nuriyya gashi kowa ya dauka, duk idan ya siyo mata abu zai bata wani irin shi yace na Hassanarta ne, dan shaquwarsu zaka rantse yan biyune, duk da kamannin su da halayensu ya bambanta, Waheedah fara ce sosai, kuma siririya ce ta gaske, tana da kyau da in zaka tsaya ka kalleta sosai zakaga bashi da alaka da hasken fatarta, sannan komai nata da sanyi takeyin shi, gashi babu wanda zaice ya taba ganin bacin ranta balle kuma fada, shisa tasu tazo daya da Nuriyya din, ita kadai take iya hakuri d
a halinta.
Sannan Waheedah zata iya sati fuskarta bata ga ko hoda ba, dan ma farace, ba zatace bakinta ya taba ganin jambaki ba, kwalliya kwata-kwata ba abu bane da yake gabanta, indai ta saka kaya masu kyau tadan goga turare mai sauqin kamshi, shikenan.
Nuriyya na da fada sosai, ba zaka daga mata dan yatsa ka sauke batare data lankwasa shi ba, ba fara bace, zaka iya saka hasken fatarta a mutanen da ake ma laqabi da masu kalar cakuleti.
Kusan kyawun mahaifiyarta ta biyo, dan kowanne irin kaya Nuriyya tasa saikaga sun amshi jikinta, tana da matsakaicin tsayin da mutane da yawa zasu iya kiranta gajera, amman a dire take, tun da yan shekarun tan nan zaka fahimci Allah ya halicci mace a wajen, cikar lokaci kawai take jira ta karasa fitowa.
Gashi fuskar nan tana daukar kwalliyar dake kara fito da ita, da wahala ka kalli Nuriyya baka sake kallonta ba.
Itama aji ukku take a sakandiren gwamnati ta mata dake nan cikin barikin sojoji, sannan islamiyarsu daya da Waheedah.
"Kardai kice baki shirya ba..."
Waheedah ta fadi ganin Nuriyyan a kwance kan katifar dake tsakar dakin, bayan tayi sallama tana daga labulen, takalman kafarta ta zare a bakin kofa tana shiga dakin sosai.
Sai lokacin Nuriyya ta tashi tana fadin
"Nayi wanka, har alwalar la'asar nayi, uniform fa zan tashi in saka..."
Gefen katifa Waheedah ta zauna tana ajiye jakar makarantarta da ledar kayan data kawoma Nuriyya din hadi dabin farantin daya ke ajiye a gefen katifar
"Kai dan Allah Nuriyya, me kuka dafa mai manja baki kawomun ba?"
Waheedah ta bukata dan ita duk abincin mai manja baya wuce ta, ga yan gidan nasu basu cika son manja ba, ko alala sai ace da farin mai za'ayi aci da sauce, itakam tana son abinci mai manja, kallon ta Nuriyya tayi
"Gero da wake ne..."
Bakinta Waheedah taji yana tara yawun kwadayi, dan inba gidansu Nuriyya ba bata taba ganin inda aka dafa gero da wake ba, sai kuwa in sunje Bugaje ne da Abba, akan kawo musu, bamai ci sai ita.
"Zakici ne in zubo miki?"
Nuriyya ta tambaya a daqile, wani lokaci irin rainin wayan nan na Waheedah yana sata jin wani maqaqi a makoshin ta, ta tabbatar abincine mai rai da lafiya aka dafama su Waheedah a nasu gidan, da wahalar gaske in babu naman kaji, amman tana nuna mata kamar su wanda suka dafa din yafi nasu, badan batason mahaifinta ba, tana jin shi har ranta, amman idan akai mata tayin musayar rayuwa da Waheedah da gudu zata amsa, kodan ta dinga zuwa makarantar kudi tana turanci kamar yanda taji sunayi, duk da itama nacin ta yasa tana da kokari naban mamaki, kuma tana kwaba turancin duk yanda yazo mata, Waheedah na gyara mata sosai.
"Kema kinsan zanci ai"
Waheedah ta fadi, daman ba wani abin kirki Waheedah din taci ba, girkin Mama sai godiyar Allah.
Mikewa Nuriyya tayi tana nufar karamin kitchen dinsu ta samu faranti ta zubo mata gero da waken ta zuba mata manja da yaji a gefe ta dauki cokali ta saka mata a ciki, dakin ta koma ta ajiye mata plate din a gabanta
"Allah dai yai miki albarka yarinyar nan"
Harararta kawai Nuriyya tayi, ledar dake gefenta Waheedah ta dauka tana miqa ma Nuriyyan da fadin
"Anty Asabe taban atamfa kwanaki, sai Mami ta bayar akai mana doguwar riga nida ke"
Da sauri Nuriyya ta karbi kayan da murmushi a fuskarta tana kasa tsayawa ta kwance ledar, yagawa tayi tana fito da doguwar rigar da dinkin yai matuqar burgeta, kasan rigar ta tsugunna ta tattaro sai lokacin ta kula da takalman da suka fado, kafa daya ta dago, badan tasan Waheedah da takalman ba, zata ce sabone yanda ta wanke shi fes dashi.
"Ke banza harda takalmi kika hado dashi"
Kai Waheedah ta daga mata, dan ta cika bakinta da abinci, saida ta fara hadiye wani daga ciki tukunna tace
"Nakine...
Mami ta siyo mana sabo"
Ta karasa maganar tana kara kai wani cokalin bakinta.
Takalmin Nuriyya ta mayar ta ajiye kan katifa tana jin wani irin abu a kasan ranta da ta kasa fassara shi.
Bawai batai murna da kyautar bane ba, tana tunanin har lokacin da zatakai tana saka kwancen abubuwan Waheedah, tana da wani irin buri a rayuwarta, tana son taga ranar da zatazo ace itace take da damar yima Waheedah irin hidimar da takeyi da ita, ba zataki ace idan damar tazo Waheedah bace a kasanta, hakan zai mata dadi ba kadan ba.
Idan bata samu damar yin karatu ta zama wani abu ba, ba zata taba auren marar hali ba, zata auri mai kudi, irin mijin da takanji a cikin litattafan hausar da bata jima da soma karanta su ba.
"Kisa uniform dan Allah Nuriyya..."
Waheedah ta fadi dan ta kusa cinye abincinta, kayan ta linke ta ajiye su a gefe tana dauko uniform dinta da su kansu tsofin na Waheedah ne ta bata bayan an dinka mata sabo, abinda takeji kasan ranta girma yake karawa, batun yanzun ta jima tana jin yanayin ba, yana kara girma ne duk lokacin da zataga Waheedah da sabon abu, ko kuma Waheedah din ta bata abinda ta rigada tai amfani dashi.
Kayan ta zira tana dauko doguwar hijab dinta ta saka, Waheedah ta rigata fita ta nufi randar ruwan su Nuriyyan da take ajiye a tsakar gida tasa cup
din dake sama ta dibi ruwa tasha.
"Nuriyya dan Allah kibar kwalliyar nan ki fito haka, wallahi zamuyi latti"
Daga can cikin dakin Nuriyya ta amsa da
"Dan Allah karki isheni, hoda kawai nake shafawa..."
Dan ana duka kan yawan kwalliya a islamiyar tasu, duk da haka saida ta kara wajen mintina goma bata fito ba.
Sallama sukai da Mama, bayan Nuriyyan ta fito suka nufi hanyar kofa tare, suna fitowa kofar gida suna cin karo da Abdulkadir, wani irin dokawa da zuciyarta tayi saida ta riko hannun Nuriyya
"Ina wuni Hamma"
Nuriyya ta fadi a tsorace itama, prefect ne a makarantar, batun anan tasan shi farin sani ba, duk da inba a makarantar su ba, bai taba dukanta ba.