← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 94

Sashe 78

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da hannu yai ma yaron alama da yazo, yana sake runtsa idanuwan shi, can sama-sama yaji muryar Khalid din na fadin
"Hamma...Hamma lafiyar ka kuwa?"
Ko kai AbdulKadir ya kasa girgiza mishi, dan iskar wajen ta sake mishi kadan, Khalid kuwa a karo na farko da ya kai hannu yana kama na AbdulKadir din da tsoro daban, dan yanda yakeyi kokawa da numfashin shi kamar mai asthma
"Hamma..."
Khalid ya kira cike da tsoro, kafin AbdulKadir din ya lumshe idanuwan shi yana wata irin faduwa da ta saka Khalid sakin wani ihu daya fito daga kirjin shi da yake cike fal da tsoro
"Hamma AbdulKadir!"
Yake fadi yana tsugunnawa hadi da girgiza AbdulKadir din da baisan a wacce duniya yake ba, da gudu Khalid ya tashi yana nufar bangaren Mami da shine yafi kusa dashi, a falo yake kiran
"Mami, Hamma....

Hamma Mami"
Cikin tashin hankali Mami ta kama Khalid din, zatace a yaran gidan yana daga cikin wanda basu da hayaniya, baya shiga harkar kowa, daga gaisuwa sai kayi da gaske zaka sake jin maganar shi, duk cikin yaran Mama yafi kowa fita daban, bata taba ganin shi a hargitse ba, shisa lokaci daya hankalin ta ya tashi
"Wanne Hamman?

Me ya faru Khalid?"
Ya kasa magana, da hannu kawai yake nuna mata alamar waje, bin bayan shi kawai tayi, daga nesa ta hango AbdulKadir din, da gudu ta karasa, cikin bayanannen tashin hankali tace
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un....

AbdulKadir...

Khalid kira Hajiya Safiyya..."
Juyawa yaran yayi zuwa bangaren Hajja da ko mintina biyu ba'a cika ba ta karaso wajen tana tsugunnawa ta kama AbdulKadir din ta dago shi jikinta tana kasa yarda yaronta ne a kwance kamar gawa
"AbdulKadir..."
Ta kira tana dora hannunta a kan kirjin shi, bugun zuciyarshi shi a cikin tafin hannunta na nutsar da wasu bangarori a tare da ita da batasan a tashe suke ba sai lokacin, wani irin numfashi take saukewa, Mami da take tsaye cikin tashin hankali itama tace
"Mu tafi asibiti..."
Kai Hajja take girgiza mata, su biyun duka tana da tabbacin ba zasu iya daga AbdulKadir din ba, balle su saka shi a mota
"Ki kiramun Yassar"
Hajja ta fadi, badan babu wasu manyan yaran gidan da in aka kirasu zasu zo ba, sai dai duk wani abu da ya shafi AbdulKadir din Yassar ne yake fara sani, wani lokaci yana ma rigan su sani, kuma shine mutum na farko da ya fara zuwa ma Hajja a kai.

Har Mami tabar wajen ta kuma sake dawowa Hajja na zaune rike da AbdulKadir, zata kirga lokuttan da taga bashida lafiya a tsayin rayuwar shi, rashin lafiya dai wadda zata kwantar dashi.

Shisa yanzun bata ma san asalin abinda take ji ba, lokacin take gani baya mata sauri duk da ba agogo bane a gabanta, sai taga kamar tayi awanni zaune a wajen kafin motar Yassar ta shigo cikin gidan.

Ko kasheta baiyi ba ya fito, kallo daya za kai mishi kasan a hargitse yake, baiko bi ta kan su Hajja ba ya tsugunna yana dago AbdulKadir din hadi da girgiza shi
"AbdulKadir ba za kai mun haka ba fa"
Yassar yake fadi muryar shi dauke da wani yanayi na karaya da tsantsar tashin hankali, baya tunanin ko su Hajja suna shiga tashin hankalin da yake shiga duk lokacin da aikin AbdulKadir zai kai shi wani waje mai hatsari, yana da Yasir, amman a duniya ji yake idan ya rasa AbdulKadir yayi rashin da har nashi numfashin ya tsaya ba zai taba komawa dai-dai ba.

Su Hajja nada wasu yaran, shi kam ji yake bashi da wani dan uwan, shisa yanzun ma yake da tabbacin basa cikin tashin hankalin da yake ciki.

A kafadar shi ya saka AbdulKadir din yana mikewa da shi, bayan motar shi ya bude ya saka shi a ciki, ya rufe murfin.

Harya zagaya bangaren direba ya shiga yana jin nauyin AbdulKadir din a tare dashi, baibi ta kansu Hajja ba, baima kula da ta shigo motar ba, ja kawai yayi yana nufar hanyar da zata kaishi wani asibitin kudi da yake yan albasa na rijiyar lemo, dan abokin shi yana aiki a wajen shisa har yasan da asibitin, tunda a cikin lungu yake.

Gudu yake yanajin kamar yabi takan motocin da suke gaban shi saboda saurin da yakeyi, a haka suka karasa asibitin, a kafadar shi ya sake daukar AbdulKadir yana shiga asibitin da gudu, wasu nurses na hango su suka taho dan su taimaka musu, ko ba mata bane Yassar bayajin zai mika musu AbdulKadir, wani daki suka nuna mishi, ya nufa da AbdulKadir ya shimfide shi kan gadon dakin, ana kiran likitan daya shigo a rikice shima.

Ya gane Yassar din, dan yana zuwa wajen Dr Isa sosai
"Kadan fita..."
Yace mishi, yanda Yassar ya daga ido ya kalle shi cikin yanayin dake fassara 'Wasa kake amman ko?' yasa likitan mayar da hankalin shi kan AbdulKadir da ko motsi bayayi har lokacin, bugun zuciyar AbdulKadir din na tabbatar mishi da a sume yake.

Duk wata allura da akai mishi da ruwan da suka daura mishi a kan idon Yassar akayi shi.

Da suka gama ma, baibi ta kan su ba, likitan ma da yayi mishi magana yaga alamar hankalin shi ba'a kan su yake ba, shisa ya fita yana samun Hajja dake tsaye bakin kofar, ko takalma babu a kafarta, Hijab din jikinta ma sallar azahar zatayi da a haka zata fito, ita sukai ma tambayoyin da suke bukata wajen bude ma AbdulKadir din kati, lokacin Dr Isa ya fito wajen, Dr Aminu na kallon shi da fadin
"Mahaifiyar Yassar ce abokin ka, sun kawo marar lafiya ne"
Gaishe da Hajja, Dr Isa yayi yana mata kallon sani daman tunda ya zo wajen, amman shi yasan ba Mama bace ba, sai dai ko cikin matan Baban Yassar din.

Mai jiki yake tambayarta, yana cewa taje kawai zai karasa sauran, har kudin bude katin shi ya biya.

Tukunna ya karasa dakin da AbdulKadir din yake suna gaisawa da Yassar daya dora da
"Me ya same shi wai?"
Dan sai lokacin yaji ya samu natsuwar bukatar hakan, Hajja likitan yadan kalla da take zaune kan farar kujerar roba, tana share kwallar da taji ta tarar mata a gefen idanuwanta
"Kayi mun magana Isa, dole zata sani tunda Maman shi ce"
Kai Dr Isa ya jinjina dan yayi magana da Dr Aminu shisa yace
"Jinin shine ya hau sosai, Allah ya rufa asiri daya samu matsala, dan Allah a gujema daga mishi hankali.

Idan ya kara faduwa haka zai iya samun matsala sosai..."
Wani abu Yassar yaji ya kulle a cikin shi
"Hawan jini?"
Ya maimaita cike da shakku a muryar shi, yana ganin kai da Dr Isa ya daga mishi
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un...oh Allah na"
Cewar Yassar da yakejin wata sabuwar damuwa ta lullube shi, ganin halin daya shiga yasa Dr Isa yi mishi sallama hadi da yiwa AbdulKadir din fatan samun sauki.

Yassar din idanuwan shi ya tsayar kan AbdulKadir da sai lokacin ya motsa yana saka Hajja fadin
"AbdulKadir..."
Fuskar shi ya dakuna batare daya bude ido ba yace
"Wahee..."
Kunne daga Hajja har Yassar din suka kasa, can kasan makoshi AbdulKadir yake ci gaba da sambatun da baisan yanayi bama
"Waheedah kiyi hakuri...

Bazan iya ba, Wallahi ba zan iya ba"
Numfashi Hajja ta ja tana fitar dashi, idanuwanta na cikowa da hawayen tausayin dan nata, sosai maza suke tunanin suna da iko akan mace, saboda musulunci da al'ada sun saka matan a karkashin su, sai dai yawa cikin mazan sun ma abin juyayyar fahimta, musulunci bai saka mace a kasan namiji saboda ta kasance mai rauni ba kawai, sai dan wani karfin zuciya da Allah ya dasa mata da bakowane yake fahimta ba, mace na da juriyar daukar laulayin ciki da yafi kowanne yanayi wuyar sha'ani, tana da juriyar naquda da duk wani kashi da yake bayanta sai ya motsa, a lokaci daya kuma tana da juriyar daukar hakuri da kaddarar wahalar da namiji.

Mace zata iya hakurin shekaru da bakin cikin da namiji ba lallai ko a fuskarta a fahimci hakan ba, amman rana daya zata ware ta kwatanta rama kadan cikin wulakancin, harshen da namiji sai yayi tashin da duk wani makusancin shi zai fahimci yana cikin yanayin damuwa, karshe sai yaba mutane tausayi saboda ya kasa jurewa har a juyar da al'amarin ana ganin ita macen tayi hakuri, cikin masu mata rashin adalcin harda yan uwanta mata, su da ya kamata su fahimci halin da take ciki fiye da kowa.

Shisa Hajja take ganin a duniya babu babban munafuncin da mata suke yaudarar kan su da shi sai fadin
'Ciwon 'ya mace na 'ya mace ne'
Dan yanzun da take zaune a gaban AbdulKadir take kara karyata zancen, badan bataji zafin abinda yaiwa Waheedah ba, ta kwatanta kanta da Waheedah ta kuma san ko kusa ba zata dauki abinda Waheedah ta dauka ba, idan bata mutu ba, auren nata zai mutu.

Har kasan ranta kuma take jin da Waheedah din Zahra ce da wahalar gaske idan bataje ta dauko 'yarta ba.

Amman ba Zahra bace, Waheedah ce, kuma a wannan gabar danta take ji fiye da ita, ciwon 'ya mace kan zama na 'ya mace ne kawai idan akwai samun riba a cikin al'amarin, shisa munafunci ne kawai a fadin hakan.

Waheedah take so tayi hakuri ta yafe ma AbdulKadir, dan kuwa ba zata jure ganin danta a cikin wannan halin ba, hakan yasa ta fadin
"Yassar zaka dan zauna da shi inje in dawo?"
Kai Yassar ya jinjina mata, ya sanar a wajen aikin shi, babu inda zai iya zuwa in ba gani yayi AbdulKadir din yaji sauki ba.

Tun farko abinda yake mishi gudu kenan, amman AbdulKadir bayajin magana, taurin kan shi sai Allah, abinda zuciyar shi ta gaya mishi dai-dai ne shi yake aikatawa, bai taba zaton zai kwatanta ba Waheedah hakuri ba sai yanzun, yana kuma jin son kai da rashin son gaskiyar da yake cikin hakan, bai damu bane kawai.

"Kabani mukullin motar ka"
Babu musu Yassar ya dauka ya mika mata, karba Hajja tayi tana mikewa.
Chapter 78 · 0% Book details