← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 94

Sashe 14

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Allah ya shirya"
Daquna fuska Abdulkadir yayi
"A'a Hamma...a'a wallahi, naji kamar kana so kace mun yaro"
Ware idanuwa Yasir din yayi, bai gama mamakin Abdulkadir ba yaji ya dora da
"Kaima yanzun kake level 2, bawai ka girmeni bane can da yawa"
Yassar ne ya kara kai mishi duka da kafa, wannan karin yana kaucewa dan yagan shi
"Me nayi?

Karya na fada?

Nidai Hamma Yasir karka fara gwada kirana yaro wallahi, ko mu kadaine balle a gaban yara"
Abdulkadir ya karasa fadi yana kumbura fuska
"Me zai faru in nace maka yaron?"
Yasir ya tambaya
"Nidai ai kashedi nayi"
Ganin abin zai zama fada yasa Yassar cewa
"Ya isa haka...

Abdulkadir tashi daga falon nan"
Kallon Yassar yake kamar ya mishi magana da wani yare daban dana Hausa
"Yes ka tashi naje, ka jini kuma"
Wata dariya mai sauti Abdulkadir yayi
"Bazan tashi bafa, dan kallo nake, sai dai shi ya tashi"
Ya karasa maganar yana nuna Yasir da dan yatsa, murmushi kawai Yasir yayi
"Ka kyale shi kawai Yassar"
"In bai kyaleni ba ya zaiyi dani daman?"
Dafe kai Yassar yayi yana sauke numfashi, su Babangida da Mubarak daman basu sake saka musu baki ba, asalima kallon su suka ci gaba dayi, dan babu wanda ya shirya rashin kunyar Abdulkadir din, ganin kowa yai shiru yasa Abdulkadir mayar da hankalin shi kan film din, duk da zuciyar shi da yakeji ta kawo wuya.

A hankali yake jin soyayyar da ake gudanarwa a film din na nutsar mishi da wani abu a kasan zuciyar shi, kamar yanda ya fada ne yana da buri mai yawa akan matar shi, kuma auren soyayya zaiyi, bazai auri yarinyar da bayaji har kasan ranshi ba, dan da kadan soyayyar da yake ma kakin sojoji zata dara tata.

Kamar yanda Waheedah tace Nuriyya zatai mata kitso, hakan ya faru ranar juma'a, tana dawowa daga makaranta, kaya kawai ta sake ta fadama Mami zata shiga gidan su Nuriyya, Amatullah ma anan tabarta zatayi wanke-wanke ta shirya itama su fita kitson dasu Zahra.

A dakin su Nuriyyan suka zauna dan yin kitson
"Karkimun manya fa"
Waheedah ta fadi, tana saka Nuriyya kwashewa da wata irin dariya
"Dame za'ayi kananun kitson to?"
Duka Waheedah takai mata
"Bana son iskanci, ai kinga dai gashina ya fara dawowa Allah"
Dariya Nuriyya ta sake kwashewa da ita, tana kallom gaban kan Waheedah din da duk ya giwgwiye, daman bawai tana da gashin kirkin bane, taje wata yar ajinsu ta fada mata tayi retouching da Petals yana saka bakin gashi, dan farin Waheedah yasa gashin ta jane, Petals din baisaka mata bakin gashi ba saima gaban daya kara kwashewa kamar an aske
"To zaki sake gwada Petals dinne?"
Nuriyya ta tambaya har lokacin tana dariya, ita kanta Waheedah murmushi take
"Allah zai kama mun ke, dan gashin nan da kike mun wulakanci sai kin tashi da safe ya kwakushe"
Duka Nuriyya takai mata, duk da ba za'a sakata a layin masu dogon gashi ba, Allah ya bata yalwarshi babu laifi, tana kuma bala'ij ji da gashin har ranta.

"Aniyarki ta biki"
Wannan karin Waheedah ce tayi dariya, hira suke sosai ana kitson, a haka har aka gama
"Ki tambaya Mami muje rijiyar lemo gobe in Allah ya kaimu"
Nuriyya ta fadi, gidan Antynta take son zuwa, kuma Naira Hamsin gareta, batajin zata isheta, in suka tafi da Waheedah din tasan zata biya kudin motar.

In ta tambayeta ma ba zata hana ta ba, tambayar ce ba zata iya ba, wani abu na mata zafi a kasan zuciyarta da tunanin hakan.

Kai Waheedah ta girgiza mata
"Da wahala Mami ta barni wallahi"
Dan duk yanda Mami ta yarda da kawancen su da Nuriyya, tasan bata son yawon da babu dalili, duk da in ana biki ko suna a bangaren su Nuriyyan takan barta taje wasu lokuttan, amman yanzun tasan babu wani dalili, fada ma zatai mata.

Hannu ta saka cikin aljihun wandon Pakistan din da take sanye dashi ta zaro Naira dari, kudin makarantar da aka bata ne ranar, babu abinda ta siya dashi.

"Ki dai siya ma su Nana ko Guava ce"
Karba Nuriyya tayi cikin ranta tana fadin
'Ashe su Nana'
A fili kuma batace komai ba, dan bakinta yakan yi nauyi da taima Waheedah godiya a irin yanayin nan, ita ma Waheedah bata taba damuwa ba, dan a ganinta sun zama yan uwan ita da Nuriyya, babu wannan a tsakanin su, mikewa Waheedah tayi tana kakkabe jikinta, hadi da durqusawa ta dauki hijab dinta
"Ki gaishe da Antyn dan Allah.

Bari inje nasan su Amatullah basu dawo ba, in kamawa Mami girki"
Kai Nuriyya ta jinjina, tana jin son cin komeye zasu girka din, dan ta tabbatar zaiji nama.

Mami bata kwauron nama a abincin ta
"Inkin dawo ki biyo, dambun shinkafa Mami zatai mana, in kuma baki biyo ba naba Aminu ya kawo miki"
Dacin da takan ji wasu lokuttan Nuriyya taji ya mata sallama a cikin makoshin ta, zatayi komai dan suyi musayar matsayi da Waheedah, da duk rana take sa tana kara jin yanayin.

"Wai aita magana kiyi shiru ki kyale mutane"
Numfashi Nuriyya ta sauke
"Ba kunne yake ji ba?

Ai ina jinki ko?"
Kai kawai Waheedah ta jinjina tana saka Hijab dinta
"Allah dai ya shirya halinki"
Ta juya ta fice daga gidan, wanka Nuriyya ta shiga, da yake ba nawa gareta ba, nan da nan ta shirya, taci uwar kwalliya, wata doguwar riga da Abban su Waheedah din ya siyo musu lokacin dayaje Umrah ta saka tana nade kanta da mayafins rigar daya bala'in karbarta.

Sallama tayi da Mama tana ficewa daga gidan, a kofar gidan su Waheedah taci karo da Abdulkadir dan nan ne hanyar da zata bi ta nufi titi, haka kawai zuciyarta tai wata irin dokawa, ba tun yanzun yake mata kyau ba, yakan yi mata kama da mazan da takan karanta a litattafan Hausa.

"Ina wuni Hamma?"
Ta furta a hankali, a karo na farko da Abdulkadir zaice ya tsaya ya kare mata kallo, baisan tana da kyau har haka ba, ga yanayin jambakin ta ya zauna a fuskarta, raini ne bayaso ko a wajen yan gidansu, shisa duk wasu tarkacen kawayen su Zahra baya damuwa da su, in sun gaishe shi ya amsa, in basu gaishe shi ba shikenan, sam bayason raini da rashin kunyar kananun yara.

"Lafiya..."
Ya amsa tukunna ta wuce, cikin gida ya koma, yana kudurta a ranshi kudin kayan kwalliya daban zai ware ma matar shi, dan ko wajen aiki ya koma yana son tuno fuskarta da kwalliyarta da yasan zasu rage mishi kewar ta da zaiyi.

Burin shi akan matar shi mai girma ne, shi kanshi yasani, duk da burin shi na saka uniform ya girme shi nesa ba kusa ba, amman ya matsa mishi ya samu wajen zama daram a zuciyar shi.
*#TeamAbdulKadir*
*#TeamWaheedah*
*#FWA*
*#AnaTare*
[7/27, 1:13 PM] +234 816 124 4732:
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Akan ce kwanaki na gudu, bai taba yarda da hakan ba sai bayan sunan shi ya fita cikin jerin mutanen da suka samu gurbi a makarantar horar da sojoji ta NDA da take cikin garin Kaduna, bayan surutun da ake tayi ja cewar makarantar nada wahalar samu, sai kana da hanya.

Zai karya idan yace Abba baisan mutane ba, ko cikin kawunnan shi baza'a rasa wanda yasan wani da zai taimaka mishi wajen samun makarantar ba, baidai nemi taimakon su bane kawai.

Kuma da yake yana da rabo sai gashi Allah ya bashi.

Ranar wani sama-sama yake jin shi, sosai ya yarda ranaku na gudu.

Duka yaushe ya fara sakandire, gashi harya kammala yana shirin jefa takun farko a hanyar shi ta cikar burin shi.

Ji yake kamar ya janyo lokacin tafiyar, yan gidan kansu sun fahimci nishadin da yake ciki, dan tunda suke basu taba ganin ya wuni da murmushi a fuskar shi ba, ko gaishe shi kayi ranar da murmushi yake amsawa.

Idan ka tona ran kowa a gidan qal yake, musamman yaran da duk ya kasance akwai tazarar koda satika ce tsakanin shi da Abdulkadir, har tambaya sukayi akace musu akan shekara daya ma ba'azo gida ba, dan sai hutun sallah da ba koyaushe yake kaiwa sati biyu ba ballantana ma ya shige hakan.

Ran su qal suke jinshi, zasu sakata su wala a gidan batare da tunanin Abdulkadir din ba.

Yanzun ma abinci suke ci a dakin Anty.

Waheedah ta kalli Zahra tace
"Wai da gaske daga shekara sai shekara Hamma Abdulkadir zai dinga zuwa gida?"
Kai Zahra ta daga mata tana hadiye abincin data cika bakinta dashi.

"Haka naji Hajja da Hamma Yazid na maganar..."
Kai Waheedah ta jinjina tanajin wani abu yai mata tsaye a wuya batare da sanin dalili ba
"Kinsan duk yanda nake murnar tafiyar nan...Zanyi kewar shi fa"
Ta karasa maganar tana dan yin jim
"Babu wanda yake shan dukan Hamma Abdulkadir irinki duk gidan nan...kewar me zakiyi tashi?

Jibgar da ki
ke sha?"
Nabila tai maganar tana cakuda abincin ta, dariya Zahra tayi, dan batasan ya zatai ma Nabila bayani ta fahimce ta ba, da gaske ne babu wanda yake shan dukan Abdulkadir din duk gidan kamar ita, sai dai ko shigowa yayi bai ganta ba sai ya tambaya tana ina, idan abu ya shigo dashi ko bata nan sai yasa an ajiye mata, tana kula da ko aiki yake so ai mishi ita kadai yafi matsawa, da wahala rana ta fito ta koma bai taba lafiyarta ba, duk da hakan tana jin Yayan nata har kasan ranta.

Abincin suka ci gaba daci suna hira abinsu, Anty ta fito daga dakin baccin ta tana ganin yanda suka mayar mata da falo
"Lallai yaran nan, falo nane haka?

Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Ta karasa ganin shinkafar dake dankare kan kafet dinta
"Wallahi tas zaku sharemun daki...ko kwayar shinkafa banason gani"
Turo baki Nabila tayi dan Allah ya dora mata son jiki naban mamaki
"Anty su Hamma ne fa..."
Hararta Anty tayi
"Banga su Hamma ba, kuna gani..."
Waheedah kam murmushi tayi hadi da fadin
"Za'a share Anty...

Damun gama.
Chapter 14 · 0% Book details