← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 94

Sashe 51

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AbdulKadir take kallo da yake dariya harda rike ciki
"Ba abin dariya bane, da gaske cinnaka ne..."
Kai kawai AbdulKadir ya iya daga mata saboda dariyar da yake, dakyar ya iya cewa
"Sannu...

Mu karasa kallon watan..."
Kafin ya rufe baki ta fara girgiza mishi kai, tana murza cinyarta da azaba ta isheta
"Akwai dalilin da yasa bama yin wasu abubuwan a najeriya..."
Wata dariyar AbdulKadir yaji ta sake kubce mishi
"Mu koma daki..."
Waheedah ta fadi tana wucewa, yabi bayanta, kasa ta zauna kan kafet tana cigaba da murza cinyarta, AbdulKadir din ya zauna kusa da ita, hadi da riko hannunta, da murmushi a fuskar shi har lokacin, yanzun ya tabbatar da abinda tagani a film ne taso gwadawa, saboda bata da hankali
"Ki daina murzawa..."
Hannunta ta kwace, ya sake riko shi, yana saka karfi wannan karin, skirt din ya kama da dayan hannun shi ya daga sama, yana duba inda cinnakan ya cijeta, wajen haryayi burdi, abinka da farar fata, har yayi ja.

Duk da tausayinta da yaji bai hana shi cewa
"Baki da hankali Waheedah..."
Shiru tadanyi, tana tunanin abinda tayi, kafin dariya ta kubce mata, tana saka AbdulKadir din jin wata sabuwar dariyar shima, dariya suke kamar babu wani abu da zai iya taba farin cikin su.

Yanzun ma dariyar yake yi da sautin ta ya dawo dashi hayyacin shi, yana saka wani abu matsewa a kirjin shi, dariyar na dishe mishi, kan shi ya dafe da hannuwa biyu
"Waheedah....Waheedah karki mun haka dan Allah...

Ki rufamun asiri..."
Yake fadi shi kadai.

Bai san iya lokacin daya dauka zaune a wajen ba, kafin sauron da yake ta girbar shi yasa shi mikewa ya koma cikin gidan, dakin Nuriyya ya wuce, ya sameta a kwance, da alamar tayi bacci, dan ta kunna fitilar wayarta ta dora akan drawer din gefen gadon.

Kayan jikin shi ya rage ya wuce bandakin yana watsa ruwa.

Fitowa yayi ya saka gajeran wando ya zagaya ta gefen gadon ya hau yana kwanciya.

Baifi mintina goma ba yaja karamin tsaki ya sauko, wayar Nuriyya ya dauka ya haska har zuwa falon ya dauki tashi wayar.

Anan ya tsaya yana kiran lambar Waheedah, ta kuwa shiga, da alama ta kunna wayar, dagawa tayi, ya numfasa zai magana ta kashe wayar a kunnen shi, tana saka shi dawo da fuskar wayar ya kalla dan ya tabbatar da kashe mishi waya tayi a kunne.

Wata irin dariya da bata da alaka da nishadi yayi, yana sake dannawa ya kirata, a kashe yaji wayar.

Wata dariyar ya sake yi
"Zaman lafiya ne bakya so Waheedah, tashin hankali kike nema dani shisa kika kashemun waya a kunne"
Ya fadi yana wucewa daki ya koma ya kwanta, juyi kawai yake yana duba agogon wayar da yaga kamar baya tafiya dai-dai, dan yaqi yin sauri.

Gari yake so ya waye, asuba a gidan Yassar zatai mishi, zaiji dalilin da zai sa ta kashe mishi waya a kunne, bayan tafi kowa sanin bayaso.

Bai samu bacci ba sai bayan sallar Asuba, dan yanda yaga rana haka yaga dare, da safen ma ciwon kai ne ya saka shi kwanciya.

Tunda Waheedah na gidan Yassar babu inda zataje, in yayi baccin ya tashi sai yaje ya sauke mata.

Ba zaice ga abinda yake faruwa ba, dan bacci yake daya kwana biyu bai samu irin shi ba, yaji kamar ana taba shi, wata irin damqa ya kaima hannun Nuriyya da yasata sakin ihu, idanuwan shi da suke cike da bacci ya sauke akan ta, tukunna ya saki hannunta da yake rike dashi.

"Masoyi da ka karyani..."
Ta fadi a shagwabe, kan shi yakeji kamar ana buga ganga a ciki saboda ciwon da yake yi
"Ki kira sunana in zaki tasheni daga bacci, karki tabani..."
Kai taje daga mishi tana murza hannunta
"Zan fita ne daman..."
Cike da rashin fahimta yake kallonta, hakan yasa ta dorawa da
"Nace maka zanje wankin kai, tun shekaranjiya..."
Kai ya jinjina mata, dan ya manta sunyi maganar, idanuwan shi ya fara lumshewa da alamun shirin komawa bacci tace
"Masoyi...."
Batare daya bude idanuwan nashi ba ya amsa ta da fadin
"Nuriyya ki duba wallet dina ki dauki kudi, dan Allah kibarni nikam"
Turo labbanta tayi tunda ba ganinta yake ba, ya bata kudi tun randa tai maganar, hakan dai ba zai hanata sake dauka ba, tunda ya manta.

"Daman in dauki motar ka tunda bacci kake, ko zaka fita?"
Ko kadan bayason dogon surutu, tsoro ya hana Waheedah koyon tuqi tun lokacin daya siyi mota, ba yanda baiyi daya koya mata ba, ya gaji ya kyaleta, Nuriyya kuwa da kanta ta nuna mishi tana son koya, ko sati biyu basu hada ba ta fara hawa babban titi, karambanin ta yana burgeshi lokutta da dama.

Zai fita da motar shi, indai Nuriyya ce yasan zata bata lokaci kafin ta dawo, amman bayason yin surutun shisa yace mata
"Allah ya tsare, ki karamun mai...

Karki dade kuma"
Murmushi tayi, sai da ta sumbaci fuskar shi tukunna ta zagaya gefen shi tana daukar wallet din shi da take ajiye kan gado, kudin ciki ta kirga taga dubu bakwai ne, duka ta kwashe tunda yace ta kara zuba mishi mai.

Mayafinta ta dauka ta saka, tukunna ta dauki mukullin motar ta fice.

Ranta kal take jin shi, zata fito a matar hamshaqin da take jinta, tun daga shigar jikinta, da leshi ne daya sha dinkin doguwar riga zuwa takalman kafarta da mayafinta, tasan ta wuce rainin kowa.

Gata matar soja, wanda taga dama zata taka babu abinda zai faru.

Haka ta shiga gidan man da ta fara samu a hanya, sosai ta kosa saboda layin da yake gidan man a ranar kamar anayin wata hidimar, duk da watan azumi ya gabato, amman sauran wajen kwanaki takwas, ballantana ace siyayyar azumi ce ta saka garin cunkushewa, danne danne waya takeyi a cikin motar tana hade rai ita kadai, ta sauke gilasan motar daman yanda za'a fi hangota, tana kuma jin dadin yanda duk wanda ya kalleta saiya kara kallon ta.

Man dubu uku ta zuba, ta ja motar kenan da nufin fita daga gidan man wayarta ta fara ruri, kawarta ce da sukayi FCE tare.

Bata kashe motar ba ta tsaya amsa wayar, barkewa sukayi da labari, tana fada mata auren wata bazawarar kawar su da za'ayi da kuma kalar shagulgulan da suka tanada.

Honking taji an isheta dashi, taja karamin tsaki hadi da zuro kai ta window din motar, har lokacin bata sauke wayar daga kunnenta ba, a wulakance tace
"Idan sauri kakeyi, kayi juya ka fita ta inda ka shigo mana"
Shima mutumin da yake cikin motar shi qirar golf leqo da kai yayi
"Bangane in juya in fita ba, Hajiya bakiga layin da yake bayana bane?

Ke ai yakamata kiyi gaba saiki amsa wayar...

Wannan ai rashin tunani ne..."
Bude baki Nuriyya tayi tana kallon shi cike da mamakin kalaman shi da take dauka a matsayin tsantsar rainin hankali, tunda can ma ba hakuri gareta ba, dan ko matar babanta sai da tace ta dauka aure zai sa ta rage fada, amman hausawa kan ce mai hali baya barin halin shi.

"Asma zan kiraki, ina zuwa..."
Ta karasa tana sauke wayar daga kunnenta ta bude murfin motar ta fito, zuwa lokacin hankalin mutane da yawa ya fara dawowa kan su, musamman zagin da Nuriyya ta fara sirfawa mutumin, ganin kalar motar da ya fito daga ciki da kuma yadin jikin shi, sam bata kula da su biyu bane, dayan babban mutum ne, zai kai shekaru arba'in da biyar ko da doriya ma.

Jikin shi sanye da shigar kananun kaya, rigar mai dogon hannu.

Fuskar shi manne da farin gilashi.

"Hajiya daga cewa ki fita zaki fara zagin shi?

Kanki daya kuwa"
A hasale Nuriyya ta mayar da hankalinta kan shi
"Ko zaka rama mishi ne?"
Jinjina kai mutumin yayi, yana rufe murfin motar ya zagaya a fusace, hakan yasa dayan abokin tafiyar tashi rike shi, da sauran mutane ma, harda ma'aikatan gidan man da suke ta ba Nuriyya hakuri ana so ta wuce ta tafi, amman ina, jinta take matar soja ce ita, sojan ma AbdulKadir, tana da tabbacin babu wanda ya isa ya tabata.

Mutumin da ake rikewa kuwa fadi yake
"Alhaji Mannir ka sakeni in ci uban yarinyar nan..."
Kafin wani ya kula, hannun Nuriyya ya tashi sama ta kuwa yi nasarar zira shi tana dauke mutumin nan da marin da yasa wajen yin shiru na mintuna, kafin a taru a shiga tsakani.

Huci kawai take tana girgije-girgije.

Wasu mata da suma sukazo shan mai suka fito daga motar su suna kama Nuriyya din suka janyeta gefe, kuka ta fashe dashi tana fadin
"Dan sun gani mace shine zasuci mun mutunci, wallahi sai na kira mijina...

Dan bazan yarda ba"
Daga gefe mutumin da har lokacin bai daina kokarin kwacewa ba yace
"Ki kira shi fa, dan yau ina son ganin uban da ya tsaya miki a fadin garin Kano da ketaren ta..."
Sosai mutane suke kokarin bashi hakuri, dan dayan abokin tafiyar daya kira da Alhaji Mannir ne ya samu ya fitar musu da motar su sukayi parking daga can gefe suka tsaya.

Duk da mutane da suke basu hakurin cewar su tafi, kafin rigimar tayi nisa, tunda da alama Nuriyya din matar wani babban ce shisa taja rigimar.

Ita kuwa Nuriyya AbdulKadir ta kira tana saka mishi kuka cewar wasu sunci mutuncinta a gidan mai.

Sai da ta fada mishi sunan gidan man ta kuma ji yace mata ta jirashi, tukunna ta kashe wayar ta koma gefe tana matse hawaye.

Mutanen gurin kowa da abinda yake fada, wanda ba'a fara rigimar a gabansu ba suna tambayar me ya faru, da yawa da aka fara a gabansu kuma suna tir da hali irin na Nuriyya din, wasu ma tafiya sukayi, da yawa kuma sun ma sha man, amman suna tsaye dan ganin karshen rikicin.

Gajeran wando ya saka, ya dauki farar riga ya dora, wayar shi ya saka a aljihu ya dauki wallet din shi, dubawa yayi yaga babu kudi a ciki, bazai iya tsayawa ATM ba, ran shi in yai dubu a bace kowanne yake, tun jiya yake neman inda zai huce haushin da yakeji, bai samu ba.
Chapter 51 · 0% Book details