Sashe 70
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kin tambayeni kudin takalma na hanaki ne?"
AbdulKadir yake tambaya yana kallonta, kai kawai take girgiza mishi, mikewa AbdulKadir yayi abincin gabaki daya ya fita daga ranshi, itama Nuriyyar mikewa tayi tana dana sanin fada mishi, hannun shi zata kama yace
"In kika tabani saina mareki Nuriyya..."
Tsaye tayi tana zare idanuwanta da suke cike da rashin gaskiya
"Yau ya zama ranar karshe da zakimun amfani da kudin hidimar gida kan wani abu daban, wallahi ranki zai mugun baci tunda naga alama ke baki da hankali"
AbdulKadir ya karasa maganar ranshi a bace
"Dan Allah kayi hakuri"
Nuriyya ta fadi, wani irin kallo AbdulKadir din ya watsa mata, hakurin da take bashi ne yakejin yana kara bata mishi rai, wucewa yayi yana komawa bangaren Waheedah, dan idan yana ganin Nuriyya komai zai iya faruwa.
Kan kujera ya kwanta yana lumshe idanuwan shi.
Da Waheedah na nan ma koyayane zuciyarshi zatai sanyi, amman tayi tafiyarta saboda ta daina damuwa dashi, abinda yafi tsana fiye da komai ya tsinci kanshi tsundum a ciki, tunanin safiyar ranar da sukayi fada da ita.
Kwanan shi biyu da zuwa, yana kula da yanayinta tunda yazo.
Shirunta ya mishi yawa, bai dai tambaya ba sai safiyar ranar tana kitchen tana soya musu fanke ya shiga yai tsaye yana jingina bayan shi da kantar kitchen din
"Wahee me yake damun ki?"
Ya tambaya, da wani nisantaccen yanayi a fuskarta ta girgiza mishi kai
"Lafiya ta kalau"
Ta fadi tana cigaba da aikinta, da idanuwa AbdulKadir din yake binta harta gama ta dauki kulolin tana wucewa falo.
Har suka karya idanuwan shi na kanta, shirun nata tabashi yake har kasan zuciyarshi, ranar ta karbi girki, tunda hutu zaiyi kwanan shi biyu a wajen Nuriyya.
Sake binta kitchen yayi ya samu tana wanke-wanke
"Shirunki yamun yawa"
Batare da ta kalle shi ba ta amsa a takaice
"Babu komai"
Kasa fita yayi daga kitchen din harta gama wanke-wanke tana goge kitchen din, ta dauki karamin towel na goge-goge ta sake fitowa falo, AbdulKadir din na binta.
Tana jin shi, batada abinda zatace mishi, bata kuma jin yin surutun, yana tsaye Nuriyya ta fito tana fadin
"Masoyi..."
Goge-gogenta Waheedah ta cigaba dayi duk da zuciyarta da takejin kamar zata bude kirjinta ta fito, ta gefen idanuwanta taga Nuriyyar ta ka
raso ta kama hannun AbdulKadir din tana saka wani irin tukukin kishi taso mata.
Batasan me suke cewa ba saboda zafin da kirjinta yakeyi ya dauke mata hankali daga kan su.
Bayau ta fara gani ba, wani lokaci suna zaune a kujera Nuriyyar zata fito daga bangarenta tazo ta zauna gefen AbdulKadir din, ko ta kwantar da kanta a jikin shi, ko ta rike hannun shi, duk wani abu da jikinsu zai hadu a gaban Waheedah din ta kula shi takeyi.
Bata taba daga kai ta kalle su ba, ballantana tayi magana, tasan idan aka tsaya tambayarta kalar soyayyar da take yiwa AbdulKadir ba zata iya misaltata ba.
Sai dai koda wasa batayi tunanin tana da zafin kishi ba sai da taga Nuriyya a kusa da shi.
Bata kara sanin zafin kishinta ya girmama ba sai lokacin da AbdulKadir din ya fara mata hirar Nuriyya da batason ji, baya kuma kula da bata tanka mishi duk idan yanayi.
Ko film take kallo in sun kalla da Nuriyya saiya fara bata labari har abinda Nuriyya din ta fada kan film din.
Babu abinda tagaji dashi sai yanda ran girkinta ko ba ranar girkinta ba sai dai tagansu a bangarenta zaune suna jira tagama girki suci, idan girkin Nuriyya dinne ma inta zuba musu tare suke ci mata abinci a falo.
Bata taba jin tagaji dasu biyun ba irin wannan karin, daga Nuriyyar har shi AbdulKadir din daya kwaso mata ita ya ajiye mata a gida tagaji dasu, ko ganin su bata son yi.
Ji take idan bata dan fita tasha iska koyaya ba komai zai iya faruwa.
Tanajin kamar daga randa Nuriyya ta shigo gidan wani abu mai kama da bomb ya kunnu a cikin jikinta, abinda ganin Nuriyyar da AbdulKadir ke karama gudun lokacin fashewa, yanzun tanajin yana gab da tarwatsewa kuma ba zaiyi kyau ba.
Muryar AbdulKadir din taji yana fadin
"Wai zata fitane da, kuma ta fasa"
Dagowa Waheedah tayi tana kallon shi, kafin taji Fajr ya riko mata hannu
"Omma banga socks ba, nasa uniform din"
Kai ta jinjina mishi
"Zan duba idan na shiga daki Fajr"
Sakin hannunta yaron yayi yana komawa kan kujera inda ta kwantar da Ikram
"Karka tasar mun yarinya bangama aikina ba"
Tace mishi, hakan yasa shi matsawa gefe ya zauna.
Hankalinta ta mayar kan AbdulKadir
"Zanje gida anjima..."
Tana kallon yanda yake girgiza mata kai tun kafin ta karasa maganar
"Zaki barni ni kadai...
A'a kam, ba yau ba Wahee"
Cikin idanuwa ta kalle shi wannan karin
"Ni ina so inje, dan Allah kabarni"
Ta karasa maganar wani abu na mata tsaye a makoshi, kai AbdulKadir ya kara girgiza mata
"Karma mu fara jan maganar nan, ba zakije ba"
Hawaye taji sun cika mata idanuwa da take da tabbacin basu da alaka da hanata fita da yayi, kawai tagajine har cikin kasusuwan jikinta
"Gaskiya Sadauki sai naje...
Ina so inje gida nikam"
Da bayanannen mamaki a fuskar shi AbdulKadir yake kallon ta, bata taba mishi magana da wannan yanayin ba, baya kuma son ta fara
"Ba zakije ba to"
Ya fadi yana kankance mata idanuwanshi, sai dai rikicin da yake cikin nata yafi nashi
"Zamu gani"
Ta fadi tana juyawa da nufin komawa kitchen ta wanke towel din da yake hannunta
"Me kika ce?"
AbdulKadir din ya tambaya ranshi a bace, juyowa tayi tana saka idanuwanta cikin nashi
"Kajini ai, ca nayi zamu gani"
Murmushi AbdulKadir yayi me sauti
"Zamu ga me?"
Ya tambaya, wuce shi Waheedah tayi ta ajiye towel din tana fitowa, bataso kome takeji ya tarwatse mata cikin gidan.
Ta gaban AbdulKadir din tazo wucewa
"Bafa inda zakije Waheedah...kinjini ai"
Ikram ta gyarama kwanciya, ganin kamar zata fado tana cewa
"Sai kai tayi kuma"
Sosai AbdulKadir yake kallonta
"Rashin kunya zakimun Waheedah?"
Ya tambaya yanajin kanshi har dumi yake dauka saboda bacin rai, dagowa tayi tana matsowa kusa dashi
"Idan rashin kunya nai maka me zai faru?"
Mamakin da yakeji ne yake kokarin danne yanda ranshi yake tafasa, da za'a tambayeshi zaice babu rana daya da Waheedah zata iya daga mishi murya balle harta kalli cikin idanuwan shi tana fada mishi magana.
Murmushin takaici ya sake kwace mishi, juyawa yayi da nufin yabar mata dakin, dan komai zai iya faruwa yaji tace
"Na dauka wani abin zakayi ai..."
Baisan me ya shiga kanta haka ba, har tambayarta yayi da yaga kamar wani abin yana damunta tace mishi bakomai
"Waheedah ki kiyayeni, Allah ki kiyayeni, karkice zaki fara mun rashin kunya.
Gidane ba zakije ba, duk kwanan nan ma babu inda zakije, ba gida kawai ba ko ina ne ma"
Dariya Waheedah tayi da take nuna mishi shidin bai isa ba, tana kara bata mishi rai
"Lallai..."
Ta fadi tana sakeyin wata dariyar, runtsa idanuwan shi yayi yana budesu a kanta, ranshi in yayi dubu a bace yake, ya manta ranar karshe da wani abu ya bata mishi rai irin hakan, bayajin ma a duniyar shi gabaki daya akwai wanda ya isa ya bata mishi rai har haka, sai dai ita din.
"Ban isa ba kenan ko me kike son ce mun?"
Ganin kallon da take mishi ya tabbatar mishi da abinda take nufi kenan
"Waheedah..."
Ya fadi cike da kashedi
"Meye Sadauki?
Nifa sai na fita, kaji na fada maka ma"
Juyawar yayi yana soma tafiya, gidan zai bar mata gabaki daya, idan ya daina jin bazai dauke ta da mari ba sai ya dawo yaji ta inda rashin kunyar nan da ba halinta bane take fitowa.
Bin shi Waheedah tayi tana riko hannun shi, in bata fita ta shaki wata iska daban da ta gidan ba tanajin matsala zata samu, kirjinta zafi yake
"Kace mun inje ni dai, kaji...
Dan Allah"
Hannun shi ya zame daga cikin nata
"Ki sakeni kafin in mareki"
Wannan karin mamakine karara fuskar ta
"Saboda zan fita shine zaka mareni?
To ka mareni dan Allah...
Ka mareni kaga in zai hanani fita"
Hannun shi AbdulKadir ya zame yana ci gaba da tafiya, sake riko shi tayi, ko kadan baisan ya akai hannun shi ya sauka kan fuskarta ba yana hadawa da tureta, ya manta yanda ko kadan bata da kwarin kirki, kafin ya rikota takai kasa kanta na buguwa da table din da yake ajiye a wajen, lokacin dayai kasa yana rikota har jini ya fara taruwa inda da alama ta fasa kanta ne.
A rikice yake girgizata
"Waheedah...Waheedah..."
Tunda yake a duniya bai tunanin zaiga tashin hankali kalar wanda yake gani yanzun da take rike a hannun shi kamar bata numfashi ba.
Baiyi tunanin akwai abinda zai gigita shi kamar wannan gigitar ba, sai yanzun da yakejin duniyar ta hade mishi waje daya.
Gyara kwanciya yayi yana sauke wani irin numfashi, kuskurene yayi da baisan ta inda zai fara gyarashi ba, na lokacin ya manta yanda Waheedah matarshi ba kanwarshi ba, da tana kanwar shi har lokacin zai dauketa ya kaita asibiti, in taji sauki suka dawo gida zaisa cable ya zani rashin kunyar da tai mishi, ya kuma zane wadda takejin zatayi mishi a gaba.
Amman matarshi ce, baisan da wanne ido zai kalli Abba idan ta fada mishi ya mareta ba, dan a gaban shi Abba kan fadi duk namijin daya daga ma yarinyar shi hannu ya sani sai dai kaddara amman ya daki auren shi.
Sai dai ya bata hakuri, ya kamata ta hakura, ta sake bashi wata damar, kome zata ce mishi, duk rashin kunyar da zatayi mishi ba zaima kulata ba ballantana ya daga mata hannu.
Tashi zaune AbdulKadir yayi yana dafe kan shi da hannuwan shi biyun, komai yakeji ya hade mishi waje daya, baisan dame zaiji ba, ranshi dayake bace da Nuriyya da ko kadan bata kula hankalin shi ba'a kwance yake ba ta kara bata mishi rai, ko da Waheedah da ta hargitsa duk wani kwanciyar hankalin shi.