← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 94

Sashe 18

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ubanka ne, nace ubanka ne ya kunna"
Abdulkadir yaji muryar Yassar cikin kunnuwan shi, kafin yaji hannun Yassar din kan wuyan shi dayai ma wani irin riqo da yasa Abdulkadir din riqo hannun Yassar daya kasa banbarewa
"Hamma zaka kasheni...me yasa kakemun hakane a gaban yara...

Ka sakeni dan Allah"
Abdulkadir yake fadi, yana raina karfin shi da yake tunanin ya karu saboda yanayin horon daya samu a makaranta.

"Daga zuwan ka, shisa babu wanda yai kewar ka"
Cewar Yassar daya saki wuyan Abdulkadir din yana tallabe mishi bayan kai
"Dan banzan yaro kawai"
Idanuwa Abdulkadir ya sauke kan Salim da yake kallon shi yana murmushi
"Idan na karaso saina tabbatar labbanka sunyi kumburin da zaka kwana biyu bakai murmushi dasu ba"
Mikewa Salim yayi yana wucewa dakinsu, ba akan shi Abdulkadir zai fara sauke kurar NDA daya kwaso ya shigo da ita ba.

Dariya Yassar yakeyi, Abdulkadir din ya wuce bayan ya watsama duk wani da suka hada ido dashi a cikin dakin harara.

Dakin shi ya wuce yana murda kofar yaga ta bude.

Shiga yayi da takalman shi, dakin a share yake, sai dai akwai kaya kan gadon, juyowa Abdulkadir yayi da nufin zuro kai yaji wanda ya shigo mishi daki ya zuba mishi kaya akan gado.

"Nine, ni nake kwana a dakin da aka fara hidimar biki..."
Yassar ya fadi muryar shi dauke da gajiya da rikicin Abdulkadir da baya karewa.

Yana yawan zuwa dubo shi a makarantane, tun ranar farko da yaje yaga halin da yake ciki, yasha wani irin duka ga zazzabin da yake da tabbacin dukanne yasa mishi shi, gashi ya rame sosai, daya dawo gida har kuka yaima Abba da fadin yaje ya dawo da Abdulkadir din, tunda zama sojan ba wahayin shi aka saukar mishi ba.

Dan yana da tabbacin rashin kunya da bakin shi zaisa su mishi dukan da zai ajalin shi wata rana.

Abba yace shi yaji zai iya, abar shi, kilan sanadin sojan yasashi fara ganin kan mutane da gashi.

Amman hankalin Yassar din ba'a kwance yake ba, bazaiki ace kullum yaje ya duba halin da yake ciki ba, yaji dadi ma yanzun da wayar hannu ya yawaita, ko bakaje kaga mutum ba, zakaji muryar shi, amman zai karya idan yace baya addu'ar kar Abdulkadir yai abinda zasuyi mishi dukan mutuwa a NDA din nan, dan yaga alama abin babu sauqi.

"Kaine mutum na farko da zan kulle ko kwana biyune Hamma, saboda kana mun abinda kake so a gaban yara"
Abdulkadir ya fada babu alamar wasa a muryarshi, hannu yaga Yassar ya kawo, da sauri ya rufe kofar yana dariyar daya manta rabon da yayi irin ta.

Kan gadon ya karasa yana kwanciya, kafafuwan shi a kasa, duk da ba takalman bane suka hana shi dora kafafuwan kan gadon, ra'ay
in kwanciyar a haka kawai yake ji.

Iskar gida kanta daban take data NDA, gyara kanshi ya sakeyi, farar rigar Yassar dake gefe nasa Waheedah fado mishi, badan kalar nata farin iri dayane da rigar ba, ko kusa basuda alaqa, kawai ya tsinceta a ranshi ne, yafi alaqanta hakan da jiran da yake ta kawo mishi abinci, dan yunwa yake ji ta fitar hankali.

Kitchen ta koma, tana jinta kamar akan iska take tafiya, tanajin yanda zuciyarta ta lullube mata wani nishadi da idan tabari ya fito fili tsalle-tsalle zata fara kamar karamar yarinya, ba tana cikin kunci bane a shekaru biyun nan, sosai take zagaye da yan uwanta da suke sakata farin ciki, amman nishadin da take ji yanzun ganin Abdulkadir dinne kawai yake bayyana shi.

A litattafan Hausar data karanta taga soyayya kala daban-daban, shisa ta sakama kusancin da takeji da Abdulkadir ayar tambaya, dan har yanzun batajin yana da suna a zuciyarta.

Dan abinda takeji akan shi yasha banban da duk wata soyayya da take gani a litattafai.

Abinda takeji akan Abdulkadir batasan tun yaushe ya fara ba, kawai bude idanuwa tayi a kusa dashi taji zuciyarta na wata irin dokawa, idan sone ya kamata ta fara tunanin koshi yanajin kalar kusancin da takeji akan shi, amman har kasan zuciyarta bata damu dako yanaji ko bayaji ba, asalima tanajin yanda nata ya ishesu su biyun.

Kuma tana jin tsoron shi kamar yanda su Zahra suke jin tsoron shi. sai dai akwai wani karfi da yake tasowa daga zuciyarta koda yaushe yana danne tsoron in tana son magana dashi.

Da murmushin daya kasa barin fuskarta take zuba mishi shinkafa da miyar da Mami ta girka, ta kuma san saboda Amatullah ta dafa, dan ba zataci abincin da batasan waya dafa ba, haka zata wuni tana shan shayi, kyankyamin da yarinyar take dashi har mamaki yake bama Waheedah.

Salak ta zuba mishi a gefe da su tumatiri da ta yayyanka harda kokomba.

Batasan waye da waye baici abinci ba, amman naman dake miyar kusan fiye da rabi ta zuba ma Abdulkadir din.

"Tunda shi baqone..."
Ta furta ma kanta, Allah kadai yasan kalar abincin da suke ci acan, gara yau yasan yazo gida.

Babban faranti ta samu ta dora karamin a ciki tana rufewa, tukunna tasa cokali a gefe.

Ruwa ta daukar mishi da kofi duk tasa cikin farantin tukunna ta dauka tana ficewa zuwa bangaren su Abdulkadir din, saida ta kwankwasa suka ce ta shiga tukunna ta cire takalmanta a wajen ta shiga.

"Ina Hamma Abdulkadir?"
Tai tambayar tana kallon Naziru daya nuna mata dakin Abdulkadir din da dan yatsan shi, yana mayar da hankalin shi kan kallon da yake, dan shi kadai ta samu a falon ma, da alama kowa ya fice hidimar gaban shi.

Abinda bata sani ba shine Abdulkadir ya fito ya zare wayoyin speakers din da suka kunna kidan dashi, da yaji bai hana kidan yi ba, yaje ya raba extension din da kayayyakin suke jone da socket din dakin gabaki daya yana zubarwa a kasa ya juya ya koma daki baice ma kowa komai ba.

Yassar ne yace su hakura kawai su kyale shi, shisa kowa ya fice daga dakin, shi kanshi Nazir din sai gaban tv din ya koma sosai dan ya rage maganar tayi kasa yanda kunnuwan shine kawai zasuji.

Wucewa Waheedah tayi, tana kwankwasa dakin
"Shigo..."
Abdulkadir din ya fadi, a hankali ta tura kofar tana shiga hadi dayin sallama, tashi zaune Abdulkadir yayi yana kasa hakuri data ajiye mishi farantin, yasa hannu ya karba, a kan cinyar shi ya dora yana budewa hadi da saka cokali a ciki ya fara cakuda gefe, tukunna ya diba yana zubawa a bakin shi.

Yanda ya sauke numfashi nasa Waheedah jin da tana da iko kullum saita aika mishi abinci Kaduna.

Tasan ya kamata ta tafi, amman kafafuwanta kamar an dasasu a wajen, bayanta ma ta jingina da bangon dakin tana kallon yanda yake cin abincin da sauri-sauri.

Abinci ya mishi dadi sosai, bai damu da tsayuwar da Waheedah din tayi ba, ko kofar dakin data bar mishi a hangame.

Haka kawai yaji ya kasa ce mata tsayuwar me take mishi a dakin har lokacin.

Batasan meyasa takejin son mishi magana haka ba, jikinta har dumi yake dauka da yanayin son mishi maganar
"Dame kaji ciwo Hamma?"
Ta tambaya, yanda yadan tsaya, kafin yakai cokalin abincin bakin shi yana juyowa ya sauke mata kananun idanuwan shi yasa zuciyarta dokawa cike da tsoron shi da bai hanata sake fadin
"Yaushe zaka tafi?"
Abincin Abdulkadir yake taunawa a nutse, inda wani ne ba ita ba, zaiji kamar ya raina shi da yawa da har zai tsaye yana jero mishi tambayoyi, amman a muryarta yake jin yanda tsakaninta da Allah tayi tambayar, babu raini kowani abu, kawai tana son sani din, amman daga haka raini yake farawa, shiru yayi ya kyaleta yana cigaba da cin abincin shi
"Sune basa barin ku zuwa?

Ko kaine kawai kaqi zuwa?

Hamma kaga wani tabon fa har a gefen kuncinka...

Dame kaji ciwuka haka dan Allah?"
Waheedah taci gaba da jero mishi tambayoyin da take jin suna fito mata a sauqaqe, kamar sun shekaru masu yawa a tare dashi, kamar tayi sabon da zatayi labari dashi mai tsayi batare da fargabar komai ba haka take jinta, duk da a kasan zuciyarta wani abu yake fada mata ba amsa zata samu ba, itama ba tana tambayar shin bane dan ya amsata, tana tambayar ne kawai saboda tana son magana dashi ko da bazai amsa ba, indai yana jinta ya isheta.

"Ko kun fara fita aikin soja ne?"
Ta bukata, tana ware idanuwanta, zuciyarta cike da wani sabon tsoro da tunanin abinda hakan yake nufi
"Hamma kun fara zuwa yaqi ko?

Inalillahi wa ina ilaihi raji'un...oh Allah na...

Ko harbine tabon wuyanka?

Oh Allah na"
Cokalin Abdulkadir ya ajiye cikin abincin shi yana fadin
"Fitar mun daga daki Waheedah..."
A daburce tace
"Na'am..."
Dan tunaninta yayi nisa cikin kalar tashin hankalin da take gani a fina-finan sojojin da take cikin kallo yanzun duk idan ta samu lokaci.

Yazid kanbar mata laptop dinshi inya samo, saita kalla a ciki.

"Ki fitar mun daga daki kafin in watsa miki mari"
Abdulkadir ya fadi can kasan makoshi, saboda dariya na gab da kwace mishi, yana kallon tsoron da ya cika idanuwanta kafin ta fice da sauri kamar zata fadi, saida ya tura kofar tukunna wata irin dariya ta kwace mishi, yana mamakin yanda Waheedah ta kasance mai hankali kuma marar hankali duk a lokaci daya.

Hannu yasa ya shafi tabon da haukanta yake mata tunanin na bindiga ne.

"Wai yaqi..."
Ya fadi yana karayin dariya
"Wallahi Waheedah bata da hankali...

Yaqi fa"
Abdulkadir din yake maimaitawa har lokacin yana dariyar da yakejin fitowarta tun daga zuciyar shi.

Abincin shi ya karasa cinyewa tas yasha ruwa, tukunna ya ajiye farantin a kasa, gani yai uku da kusan rabi, hakan yasa shi mikewa ya kwance takalman kafar shi, tukunna ya shiga bandaki dan ya dauro alwala, fuskar shi ya kalla a mudubi, murmushin da yake bayyane a jikinta nasa shi janye idanuwan shi daga kan mudubin, dan yanayine da ya zame mishi baqo, ya kwana biyu baiyi nishadi irin nayau ba.

Tsintar kanshi yai da murmushin har ya idar da alwala ya fito, waje ya samu ya zauna yana jira a kira sallah dan ya wuce masallaci.
Chapter 18 · 0% Book details