← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 94

Sashe 19

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dinner zasuyi da daren ranar, duk da Abba ya nuna duk wannan bidi'ar bason ta yakeyi ba, haka ya hakura ya kyalesu ganin sun kafe.

Dogayen riguna ne sukai anko iya su yan cikin gidan, material din wine color, yayi matuqar kyau.

Mami tai ma Nuriyya ankon da duk sauran dinkunan da taima Waheedah.

Yanzun ma tare duk suka fito da za'a tafi, yanayin dinkin ya zauna ma Nuriyya sosai, da wahala ta gitta baka sake kallonta ba, ko dan kwalliyat data sha, kusan duka yan gidansu Waheedah din Nuriyya tai musu kwalliyar su, ga kunshi ansha, kamar sune amaren.

Nuriyya ta rataya mayafinta a kafada, yanda su Zahra ma sukayi.

Itakam Waheedah fuskarta fayau take, banda hoda data murza sai Vaseline data shafa ma labbanta, daurin dankwalinta ma mai sauqi tayi, saidai kalar kayan ta amshi farar fatarta, ta yafa qaton mayafinta a kafadunta duka biyun, duk da haka wani iri takeji, wuyanta da yake a bude, itakam wannan mayafin asarar kudine, dan tasan ana gama bikin zata ajiye shi, tafi gane hijabanta.

Motar da za'a dauke su ciki ta cika tsaf, bata samu waje ba.

"Yanzun dan Allah saiku tafi kubarni?"
Waheedah ta fadi cikin sanyin murya, tana dorawa da
"Nuriyya dan Allah ki rungumeni..."
Dariya Nuriyya tayi
"Ki yamutsemun riga?

Wallahi bazai yiwu ba"
Sake marairaicewa Waheedah tayi
"Toni ki tashi in rungumeki"
Maryam, yar yayan Abba dake zaune gefen Nuriyya ta kwashe da dariya.

"A wacce cinyar zaki rungumeta?

Mansur muje dan Allah..."
Maryam ta karashe maganar tana miqa hannu ta ja murfin motar dan taga alamar in suka biyema Waheedah zasu kara bata lokaci, ba zata rasa wanda zata biyo ya kawota ba.

Kuma za'a daddawo daukar sauran mutane dole daman.

Waheedah din kanta tasan hakan, kawai dai taso ta bisu dinne tunda duk sa'anninta na cikin motar, ga Nuriyya kuma, kafin dai ta gama sanyin jiki duk sun shige, tsaye tayi a wajen tana jin idanuwanta sun cika da hawaye.

"Waheedah ke baki tafi ba?"
Taji muryar Yazid, juyowa tayi, kwalla cike da idanuwanta
"Wai ba waje..."
Dariya Yazid yayi, yarinyar bata da wahalar kuka ya kula, sai dai akwai wani abu tattare da sanyin halinta da yake ji har kasan zuciyar shi.

"Yanzun Abdulkadir zai fito, saiku wuce tare...ina zuwa zanyi abu"
Yazid ya karasa yana wucewa da sauri, aikam Abdulkadir dinne ya fito, jikin shi da shadda ruwan toka mai cizawa, ta manta ranar karshe data ganshi da manyan kaya, sosai taga yai mata kyawun da taji yasa zuciyarta ta matse waje daya.

Sai kamshi yake zabgawa, hular da take hannun shi ya saka saman kan shi yana karasowa inda take, ya miqa mata wallet din shi da agogo yana da links din hannuwan rigar
"Riqe mun..."
Hannuwanta biyu ta ware mishi ya saka a ciki, yana daukar link guda daya ya fara sakawa a jikin hannun rigar yana zabga tsaki
"Meyasa Hamma zaimun wannan hannun shirmen?"
Da sauri Waheedah tace
"Kawo in sa maka?"
Kananun idanuwan shi ya kara kankance mata
"Kin iya?"
Kai ta daga mishi, kayan hannunta ya karba, yana miqa mata dayan hannun shi, kamawa tayi tana dan rausayar da kanta gefe
"Saika dago hannun ka"
Ta fadi a hankali, gyara mata hannun Abdulkadir yayi yana kallon yanda ta nutsu tana saka mishi link din, sai yaga kamar tafi dazun yi mishi haske, ko dan kwan fitilar da ya haske mata fuskane, bai sani ba.

"Dayan hannun..."
Cewar Waheedah tana jin wani gajimare na mata yawo a kanta.

Miqa mata Abdulkadir yayi yana ware mata tafin hannun shi ta dauki link din.

Saka mishi tayi, sai ya tsinci kanshi da miqa mata agogon, karba tayi ta daura mishi, wallet din ya miqa mata, yasan yana da aljihu a wando da rigar kayan da suke jikin shi, kawai yanajin bata ta riqe mishi ne.

"Kin shirya?

Muje?"
Ya tambaya, tana daga mishi kai, harya numfasa yai mata maganar ta bude bakinta ta amsa shi, saiya tuna Waheedah ce, ta saba amsa mishi magana da kai, saboda shiya saba kyaleta duk idan tayi.

Wucewa kawai yayi tana bin bayan shi, saida suka karasa tukunna taga dayar motar Abba ce zasu fita a ciki, zagayawa Abdulkadir yayi yana bude motar ya shiga, harya kunna baiga alamar Waheedah zata shigo ba, numfashi ya sauke yana rasa kalar Waheedah, kafin ya miqa hannu ta ciki ya bude kofar, yana ganin tayi baya tana murza hannunta da alamar ya bugeta.

"Sai nace ki shigo?"
Ya bukata a fadace, yanajin gajiyar da baisan daga inda ta fito ba.

Idanuwanta take ware mishi, dan taji ba cayai ta shiga din ba, tambayar ta yayi, kai ta girgiza mishi a hankali, da alama tana jiran ya bata umarni ta shiga din tukunna, numfashi ya sake saukewa a karo na farko, bayajin zai iya masifa
"Shigo Waheedah..."
Ya fadi da gajiya a muryarshi, shigowar tayi, tana rufe murfin kofar, tana jin yanda kamshin da yake ya cika motar...!
*#TeamAbdulKadir*
*#TeamWaheedah*
*TeamNuriyya*
*#AnaTare*7/27, 1:13 PM] +234 816 124 4732:
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Idan akwai abinda yakeyi a nutse a rayuwar shi bai wuce tuqi ba, ko Yassar daya koya mishi tuqin idan zasuje wani waje yakan ce mishi
'Abdulkadir kana taka mota kaman zata cijeka.

Dan Allah ka kara gudu'
Shikam baiga saurin da yake ba.

Yanzun ma a nutse yake tuqin shi, kamar yanada duka lokacin da yake bukata.

Waheedah kuwa ta nutsu a gefe tana wasa da wallet din shi da take hannunta, zuciyarta na doka mata a kirjinta kamar zata fito waje.

Ga shirun da yake cikin motar da take jin kaurin shi kamar tasa hannu ta dangwalo yai mata yawa.

Rasa abin yi yasata balle maballin da yake jikin wallet din tana wasa dashi.

"In kika lalata mun saina zane jikin ki"
Abdulkadir yai maganar hankalin shi nakan tuqin da yakeyi, dan yanajin yanda maballin yake bas bas duk idan ta bude ta sake rufewa, yasan wasa take dashi.

Badan ba zaiyi abinda yace din ba, ya zaneta tasan ba wani abu bane, ba zai zama ma farko ba, bata dai san dalilin da yasa maganar shi ta bata dariya ba.

"Na zama sa'anki ko?"
Ya buqata jin sautin dariyarta, bata amsa ba, bai kalleta ba kuma har lokacin, amman yasan kai take girgiza mishi.

Bata mayar da maballin jikin wallet din ba, hakan yasata budewa tana sa hannu ta shafa wajen da taga alamar I.D card dinshi ne, hannu tasa ta janyo tana kokarin ganin hoton da yake jiki, sai lokacin Abdulkadir yadan juya ya kalleta, yana mayar da hankalin kan tuqin da yakeyi, yaga yanda take daga I.D card din wajen gilas din kofar dan tagani, hannu ya miqa ya kunna fitilar dake cikin motar yana sata rufe idanuwanta ta sake budesu da wani yanayi dayake nuna bata tsammaci hasken daya gauraye gaban motar ba.

Tukunna ta kalli Abdulkadir din da idanuwan shi suke kafe kan titi, numfashin da batasan dalilin shi ba ta sauke tana mayar da hankalinta kan ID card din da yake hannunta taci gaba da dubawa, dan yatsanta babba na shafa kan hoton shi da yake manne a gefe.

Mayar mishi da ID card din zatayi wajen data ciro shi taga dan qaramin hoto a wajen tasa hannu ta zaro tana karema hoton da alamu suka nuna bai jima da daukar shi ba, dan askin da yake kanshi yanzun shine a jikin hoton.

Wani abu dayai mata tsaye a makoshinta take kokarin hadiye wa amman yaki tafiya
"Hamma..."
Ta kira muryarta can kasan makoshi, saida tai tunanin bazai amsa ba tukunna yace
"Menene?"
Dan yaji ta kira sunan shi, bai amsa bane yana jiran taci gaba da magana, jin tayi shiru yasa shi amsawa, yasan zasu iya kaiwa inda zasu kai batai maganar ba tana jiran saiya amsa ta.

Dan gyara zamanta tayi tana kallon Abdulkadir din, gudun zuciyarta na karuwa da tambayar da take shirin yi mishi, kafin ta tattaro duk wani kwarin gwiwar da zata iya tace
"In dauka?"
Dan daquna fuska yayi duk da bai kalleta ba, yanayin nasa idanuwan shi qara kankancewa
"Meye?"
Numfashi taja a hankali tana sauke shi da fadin
"Wannan hoton?"
Sake rage gudun motar yayi yana dan kallon hoton da ta nuna mishi, dan yasan akwai qananun hotuna da yawa a cikin wallet din tashi, baisan kowanne take cewa ta dauka ba, hoton ya kalla, da alamu a kafadarshi da yake nuna yana therma III yanzun a NDA, hoton bai dade ba, kafin ya taho din nan ne ya dauka, shine hoton shi na karshe dayai zuwa yanzun.

Fuskar shi har lokacin a daqune take, kan titi ya mayar da hankalin shi yana kara gudun motar yanda yake da kafin ya rage.

Ba tambayarta bace ta bashi mamaki, baiga me zatayi da passport din shi bane ba, hoton dako kyau baiyi ba.

Zuciyarta take ji ta dawo makoshi saboda gudun da take, amsar shi take jira, in yace karta dauka zata mayar ta ajiye mishi, tun da daga farko ma batasan meyasa ta tambaye shi ta dauka din ba, ta ciro hoton kuma taji tana son kasancewa dashi, tana son samun wani abu daga wajen shi kafin ya sake tafiya, tunda ba ranar dawowa gare shi ba.

Wani abu da zai riqeta harya sake dawowa.

Batasan kalaman da zatai amfani dasu su fassara dalilinta ba, kusan hakan dai shine abinda take ji.

"Kaji Hamma...

In dauka?"
Ta tsinci kanta da sake fadi, dan daga mata kafada Abdulkadir yayi yana juya steering wheel din ya sha round din dake gaban shi, jitai wani abu na narkewa a zuciyarta da batasan akwai shi ba, yanayin shi da abinda yai da kafada nasa numfashin ta yi mata barazana.

Dakyar ta iya cewa
"In dauka?"
Wannan karin Abdulkadir dinne ya sauke numfashi
"Komai ne sai nayi surutu?"
Dan murmushi tayi
"Baka ce in dauka ba ai...haka kayi da kafadun ka"
Ta karasa tana daga nata cikin son nuna yanda yai da nashin.

Kai kawai Abdulkadir ya girgiza dan sun karaso wajen da Yazid din yai mishi kwatance za'ayi dinner.

Baiyi tunanin zai gane ba, sai dai yawon da suke sha a garin Kano ba dan kadan bane ba.
Chapter 19 · 0% Book details