Sashe 6
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zufa taga yana yi, a hankali jikin shi ke bari, tasan yana cikin duniyar mugayen mafarkan dakan hana mishi samun wadataccen bacci.
Ganin yanda yake zabura yasa takai hannun ta kan fuskar shi tana shafawa a hankali.
"Sadauki..."
Ta kira a tausashe, hannunta taji ya damqa kamar zai karyata kafin ya bude idanuwan shi yana sake matse riqon dayai ma hannunta da saida ta runtsa idanuwan ta saboda azaba, sosai ta dauka ya karyata yau dai.
"Sadauki hannu na..."
Ta fadi, tana saka shi dago fuskar shi daga kan cikin ta yana karema dakin kallo, kafin da sauri ya saki hannunta yana fadin
"Bansan sau nawa zance ki daina yo kusa dani inkin ganni a yanayin nan ba..."
Dayan hannun ta mai daure da ruwa ta dago tana murza wannan din, idanuwanta harsun tara hawaye
"Yau dai ka karyani, kayi maganarka ta karshe a bakin yan Amin, an amsa, ka karyani Sadauki..."
Karamin murmushi yayi yana kamo hannun nata data fisge, karfi yadan saka ya riko hannun
"Kokawa zakiyi dani?"
Ya tambaya yana daga mata girar shi guda daya.
Turo mishi labbanta tayi, hannun yake dubawa, farar fatarta tasa hannun ya fara tara jini, shafa mata wajen yayi
"Ban karyaki ba, in kina tabani ina bacci dai zai faru wata rana, na fada miki bakyajin magana"
Fisge hannun ta tayi tana murzawa.
"Ina yarana?"
Ta buqata a hankali, tana jin kewarsu na danneta
"Fajr na tare dasu Mami nake tunani, Ikram na wajen Anty...bari in karbo miki ita..."
A hankali ta girgiza mishi kai duk da hakan take so, batasan lokacin data dauka a kwance ba, tasan yarinyar taji yunwa ba kadan ba, amman a karbota daga wajen Anty, abin ya mata nauyi.
Abdulkadir bai saurareta ba ya miqe yana nufar kofar dakin ya bude ya fita, Anty yagani zaune tana danna waya, da alamar game ne daya kalli screen din.
"Ta tashi Anty, ki bata Ikram wai..."
Batare da tace mishi komai ba ta ajiye wayarta a gefe tanaa kama goyon yarinyar ta kwance ta mika mishi ita, karbarta yayi yana kallon ta, idonta biyu, ta tsoma hannuwanta guda biyu a bakinta tana tsotsa.
Gyara mata zama yayi a hannun shi daya tukunna ya bude kofar yana shiga yana mayar wa ya rufe, sai da ya saka Ikram a hannun Waheedah din tukunna ya zauna inda ya tashi, yana kallo ta miqe zaune tana jingina bayanta da abin gadon, tukunna ta gyarama Ikram din zama sosai tana soma shayar da ita.
Dago kanta tayi tana kallon shi, zuciyar shi yaji ta doka ganin yanayin nan baibar idanuwan ta ba.
"Kai nake jira..."
Ta furta a hankali, kallon ta yake yana son fahimtar ma'anar kalaman da ta furta mishi.
"Abinda na fada maka dazun, bana ce ka saukake mun auren ka ba?
Ko baka jini ba in sake maimaitawa?"
Yanzun ya gama tunanin ta dawo hayyacin ta, ashe bata dawo ba har yanzun, wacce irin buguwa tayi haka.
Dole zai magana da likitocin nan, inma barin kasar ya kama Allah ya mishi rufin asirin da baya tunanin zai gagare shi.
"Kayi shiru..."
Waheedah ta fadi tana sake tallabo Ikram din jikin ta, wani irin yanayi taje ji da batasan yanda zata misalta shi ba, har wani kaikayi take ji a jikinta da son jin ya furta mata kalaman da zasu datse igiyar da ta qulleta dashi.
"Kin buga kanki da yawa..."
Abdulkadir ya fadi can kasan makoshi, shine kawai bayanin dazai fassara abinda yake faruwa yanzun.
Idan ba kanta ta buga ba Waheedah ba zata nemi saki a wajen shi ba, karma azo maganar saki ba zata kalle shi cikin ido tana mishi magana da yanayin rashin kunya haka ba.
"Ban buga kaina ba, sakina nake son kayi..."
Ta fara bata mishi rai, yana jin yanayin na barazana da hakurin shi.
"Kibar mun maganar nan, ki bari, nace kin buga kanki da yawa ne..."
Ya karasa yana jan kujerar shi baya ya miqe tsaye
"Ina zaka je?"
Dan dafe kanshi yayi yana sauke hannun shi
"Zan magana da likita..."
Wani murmushi Waheedah tayi, tana rasa meyasa kalamanta suke mishi wahalar fahimta haka.
"Kayi magana dashi, idan ya tabbatar maka lafiyata kalau, saika dawo ka saurareni"
Kallon ta Abdulkadir yake yi, maganganunta na zauna mishi, a hankali ya girgiza kai, idan ya zaman bata buga kanta ba, idan ya zamana tana cikin hayyacinta baisan me zaiyi ba, baisa ina take so ya ajiye kalaman ta ba.
Babu shiri ya koma ya zauna yana kiran sunan ta
"Waheedah..."
Kallon shi kawai tayi batare data amsa ba, wani abu daya zo wuyan shi ya tsaya yake kokarin hadiyewa amman hakan ya gagara.
"Saboda hakurina ya kwace a karo na farko a zaman mu yasa kike furta mun kalaman nan?"
Kai ta girgiza mishi a hankali
"Kamun abinda yafi nayau, kasani kuma, nayau dinne dai zai zamana na karshe In shaa Allah..."
Wata gajeriyar dariya yaji ta kubce mishi
"Kin san girman kalaman da kike furta mun?"
Ikram ta janye daga jikinta dan hartayi bacci, tana gyarawa tukunna ta jinjina mishi kai.
"Ba zai yiwu ba to, idan ma da gaske baki buga kanki ba, ba zai yiwu ba Waheedah..."
Ya fada da wani yanayi a muryar shi da yasa ta tambayar
"Meye bazai yiwu ba?
Sakin nawa?"
A hasale Abdulkadir yace
"Waheedah...kina son sake gwada hakurina ba?"
Cikin idanuwa ta kalle shi
"Meye zai faru?
Zaka sake dagamun hannu ne yanda kayi?
Nace idan na gwada hakurin ka zaka sake dagamun hannu ne Abdulkadir?"
Yanda taja sunan shin kamar ta kafa abin gurza kwakwa a zuciyarshi taja haka yaji ta karce wajaje da yawa a cikin kirjin shi.
Ko a mugun tunani bai taba hango Waheedah zata taba yi mishi rashin kunya ba, mamaki yake har kasan ranshi daya kai karshe wajen baci, ya mata kuskure bawai bai mata ba, amman hakan bashi bane dalilin dazai sa ta kalli kwayar idanuwan shi tana fada mishi son ranta, bai tsaya kalmar neman saki ba, harda rashin kunya tana daga mishi murya.
"Saukake miki a hannuna yake ko?
Ba zai faru ba to, kina jina bazai faru ba"
Wasu hawaye taji masu zafin gaske suna zubo mata, ji take wani abu yana yamutsawa cikin kanta, rashin hankalin da yake mata tunanin take ji yana gab da cimmata idan bai saukake mata auren shi ta huta ba yau.
"Wallahi baka isa ba"
Ta fadi muryarta na karyewa da kukan da takeyi, kujerar shi yaja baya yana mikewa, wani irin tuquqin bacin rai yake ji har idanuwan shi ke lumshewa
"Ki kalleni..."
Ya furta ta tsakanin hakoran shi, kukan ta taci gaba dayi
"Ki kalleni Waheedah!"
Ya fadi cikin wata irin murya data sata sauke idanuwanta da suka fara rinewa da kuka cikin nashi
"Na isa...Ni Abdulkadir Ahmad Bugaje na isa har nayi yawa.
Bansan me yake damunki ba, ki kwanta kiyi bacci, bana bata lokacina akan abinda ya riga da ya wuce ke kin sani, zanyi kamar komai bai faru ba..."
Ya karasa maganar yana juyawa dan jikin shi ya soma bari da bacin ran da yake ciki
"Sadauki karka fita baka saukake mun ba..."
Waheedah ta furta kamar baiyi magana ba, kamar bata ji abinda yace ba, bai juyo ba, saboda baida tabbas kan abinda zai iya faruwa idan baibar dakin ba, yanda ya doko kofar saida ya firgita Ikram data zabura tana fashewa da wani irin kuka, riketa Waheedah tayi tana jijjigata cikin alamar lallashi dan itama kukan takeyi.
Yana fita Anty ta shigo tana kallon Waheedah dake faman share hawaye.
Dan haka ta karasa tana karbar Ikram din daga hannunta ta goya yarinyar da dakyar ta samu tayi shiru.
"Dan Allah kubi komai a hankali, kinji Waheedah?
Kinga baki da lafiya..."
Saida ta share hawayen da sunqi daina zubar mata, da wani daci a makoshin ta tace
"Ni bance wani abu ba Anty, ko a musulunci an bani damar neman saki idan naga bazan iya zama dashi ba...
Me yasa bazai mun abinda nake so ba?"
Yanayin karayar dake muryarta yasa Anty karasowa ta dafa ta, itama tana jin idanuwan nata sun ciko da hawaye dan Allah yai mata wata irin zuciya da ko bata sanka ba taga kana kuka itama tayaka takeyi, balle kuma Waheedah da hankalin yarinyar yasa take jinta har ranta.
A raunane tace
"Ku dai bi komai a hankali, karki yanke hukunci cikin fushi..."
Wasu sabbin hawayen na zubar ma Waheedah tace
"Anty ki aramun wayarki dan Allah"
Batare da wata gargada ba Anty ta cire lambobin sirrin data rufe wayar dashi ta mika mata, wajen kira ta shiga tana fara saka lambobin mutum dayan da take da yakinin shi kadaine zai iya saka Abdulkadir yai mata abinda take so, shi kadaine kuma bazai ce tayi hakuri ko abi abun a hankali ba.
Danna kira tayi tana kara wayar a kunnenta, ringing daya tayi a na biyun ya daga da sallamar data kasa amsawa sai ma wani sabon kukan da taji ya kwace mata.
Dakyar ta iya cewa
"Abbah..."
Tana jin muryar shi daga dayan bangaren ya amsa da
"Waheedah?"
Cikin son tabbatar da ita dince, kai take daga mishi kamar yana ganin ta, wasu hawayen na zubar mata
"Abbah..."
Ta sake kira cikin kukan ta
"Subhanallah...
Waheedah me yake faruwa ne?
Lafiya dai ko?"
Kai ta girgiza mishi
"Abbah kai ma Abdulkadir magana ya sauwaqe mun...
Dan Allah Abbah"
Ta karasa maganar kuka mai sauti na kwace mata, jim yayi daga dayan bangaren da alama yana juya zancen tane, kafin yace
"Hajiya Halima na kusa dake?"
Dakyar ta iya cewa
"Eh..."
"Ki bata wayar..."
Anty dake tsaye Waheedah ta miqa ma wayar, tana jan kafafuwanta ta hade su da jikinta hadi da dora kanta saman gwiwoyinta hawayenta naci gaba da zuba...!
*#Abdulkadir*
*#FWA*
*#AnaTare*
[7/27, 1:13 PM] +234 816 124 4732:
FIKRA WRITER'S ASSOCIATION
Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Tunda ya shiga gida bangaren Waheedah ya wuce, dakin baccin su ya shiga, yana zama gefen gadon.
Kan shi sarawa yake tunda ya fito daga asibitin, baisan ta inda zai fara tarar matsalar da Waheedah take son janyowa rayuwar su ba, dan baisan meya shiga kanta ba, kafafuwan shi ya janyo da nufin dorasu kan gadon yaga takalman shi dabai kwance ba.