← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 94

Sashe 85

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nuriyya doyar ta samu wani waje ta rage, tana rage man ma, ta sake kunna gas din, ta soya ta ciki da kwan jiki duk ya nadi mai, ta kwashe ta saka wadda ta rage din itama ta soyata, doyar nayin wajenta kwan ma yanayin wajen shi.

Zuwa lokacin shidda harda kwata.

Dan AbdulKadir ya wuce daki dan ya daura alwala, yana so ana kiran sallah ya fara saka wani abu a cikin shi tukunna ya fita masallaci ko zai samu natsuwar yin sallah.

Nuriyya kettle ta dauka da nufin dora ruwan zafi su sha shayi, shaf ta manta da man da ya zube a kitchen din, ga kuma ruwan da ta zubar dan ta cika kettle din, ta kuma takashi tana nufar inda socket zaiyi, ta taka man tana wata irin zamewa, sai da tai sama, kettle din ma tayi sama tukunna su duka suka sauka kusan a tare, kettle din a gefe da ruwan ciki daya mungule gabaki dayan shi, ita kuma aka mazaunanta tayi warwas a kasa.

Ta dauki wasu dakikai tana sauke numfashin wahala kafin taja kafafuwanta ta mike.

Jikinta take kakkabewa duk ta nade ruwan a doguwar rigar dake jikinta, kettle din ta dauka ta tari wani ruwan, tana kokarin mayar da hawayen da suka cika mata idanuwa taf.

Gabaki daya duniyar ta hautsine mata a cikin kankanin lokaci.

Kettle din ta jona tana kunnawa.

Sannan ta sa abin goge-goge na tsaye ta fara aikin goge kitchen din, tanajin kiris take jira ta fashe da kuka.

Tana gama gogewa ta sake mayar da miyar kan wuta ta bata mintina biyar tukunna ta kashe, ko tayi ko batayi ba a haka zataci.

Tana nan tsaye ruwan ya tafasa, kettle din ta kashe kanta, ta dauko flask tana juyewa taji kiran sallah.

Ta karasa ta rufe, ruwa ta dauko a fridge sai ga AbdulKadir ya shigo kitchen din, ya karbe robar daga hannunta yana budewa yai Bismillah ya kafa bakin shi, Nuriyya na bin shi da kallo harya sauke robar hadi da wani irin numfashi, ruwan ya mika mata ta karba itama tasha, yana dirar mata ciki da wani yanayi mai sanyi.

"Kibani wani abu inci in fita masallaci"
AbdulKadir ya fadi yunwa yakeji har kan shi na mishi ciwo.

Kular doyar ta bude mishi, a tsaye ya saka hannu yana dauka ya saka a bakin shi duk da ta mishi zafi, yanajin ta kamar babu gishiri, kuma kwan bai kama ba, Waheedah harda tattasai take saka musu in zata soya.

Baiyi magana ba, saboda yau daya ga azumi, bazai dora alhakin fadansu akan shaidan ba, asalin halayen sune zasu bayyana.

Ficewa yayi daga kitchen din zuwa masallaci, jikin shi har kyarma yake sanda aka idar ya taho gida.

Bangaren Waheedah ya wuce yana jin kamshin daya hade waje daya baisan kona menene ba, amman ya kara mishi yunwa.

Kan darduma ya sameta a daki tana azkar ne da alama.

"Sannu da shan ruwa"
Ya fadi yana kallon yanda fuskarta tai wani sanyi.

Murmushi tayi mishi tana idar da addu'ar ta
"Sannun mu"
Ta amsa shi tana mikewa ta ninke dardumar da take kai.

Kallon ta AbdulKadir yake tayi yana kallo ta fita daga dakin, tana dawowa da apple a hannunta ta gutsura tana taunawa, Ikram ta dauka a gefen shi tana samun waje ta zauna, yarinyar ta gyarama zama itama a jikinta dan ta bata tasha, taci gaba da cin apple dinta, cikin shi da yaji yayi wata irin murdawa yasa shi mikewa, dan da alama Waheedah ba zata bashi abinci ba, ta daina son shi yanzun...!

Please, biko, dan Allah show me love, subscribe to my YouTube channel.

Ina bukatar aqallah subscribers dubu daya.

Nagode
https://youtu.be/WwocHslDAYk
#LubnaSufyan
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
#AnaTare[7/16, 9:56 PM] +234 802 111 7692: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Kan kafet ya zauna yana jiran Nuriyya ta fito daga daki ta dauko musu kular doya.

Ko yaji bata dashi, ta ajiye tana samun waje ta zauna tare da fadin
"Masoyi ko yaji bamu da shi, in karbo mana wajen Waheedah?"
Tun kafin ta karasa AbdulKadir yake girgiza mata kai.

Bada shi za'ayi wannan danyen aikin ba, ba zata ja mishi jangwam daga dan samun natsuwar shi ba.

Kai Nuriyya ta rausayar tana sake mikewa, kofina ta samu guda biyu, a kitchen din ta hada musu tea ta fito dashi tana ajiyewa AbdulKadir na shi, dauka yayi ya kurba dan ya kora doyar da tai mishi tsayuwar mashi a makoshi.

Yana dan bata rai jin kamar akwai abinda ya kamata ya kasance cikin shayin da babu, ya saba da Waheedah na saka kayan kamshi a shayinta, yanzun kam ruwan zafine sai madara da milo, ko lipton din ma bai samu a ciki ba.

"Wacce irin doyace wannan Nuriyya?

Babu kwai fa"
AbdulKadir ya fadi yana saka Nuriyya hadiye doyar dakyar, gashi tayi mata wani irin salaf, shi baiga kokarin da tayi ba, ko da bata soyu kamar yanda ya kamata ba, sai ya duba kokarin da tayi yai shiru
"Na saka kwai ni dai"
Tai maganar tana saka AbdulKadir din kankance idanuwan shi a kanta
"Bana gani ne?

Ya zaki cemun kin saka kwai?

Kafafuwa yayi ya rabu da doyar kenan"
Yai maganar a fadace saboda yanda yaji zuciyarshi na tafasa, ga yunwa yanaji ta fitar hankali, amman rabon shi da abinci makamancin mai munin wannan tun wani aiki da yaje Makodi, shima wajen abinda duk ka samu shi zaka aunawa cikinka.

Amman ko wannan din zakaji alamun gishiri a jikin shi.

Ganin tayi shiru yasa shi jinjina kai kawai, bazai karar da dan karfin shi akan doya da kwai ba.

Haka ya dauka yana turawa sai ya danna da shayin ya hadiye.

Iya inda yaji cikin shi ya cika ya tsaya yana karasa kurbe ruwan shayin ya mike, dai-dai lokacin da yan nepa suka zabi su dauke wutar su.

Dogon tsaki AbdulKadir yaja, yayi niyyar ya biya ya siyo mai dazun, kwana biyune bai damu daya kunna gen din ba shisa.

Daman indai ya biyewa Waheedah ba kunnawar zai dingayi ba, zatace ita babu abinda zatayi da wutar tana da charge, kuma tama fitilar ta ma, sai dai in ana zafine dan su kunna fankoki.

Da fitilar wayar shi yayi amfani zuwa daki ya dauko ma Nuriyya tata wayar yana kunna maya fitilar ya ajiye kan kujera ya kama hanya yana ficewa daga gidan batare da yace mata komai ba.

Tana jin shi harya fita bata dai dago bane ba, wani irin kunci naban mamaki ya cika zuciyarta fam, ba zata tuna ranar karshe da wani abu yazo wuyanta yai tsaye ba haka.

Har yunwar da takeji ta nemeta ta rasa, kwashe kwanonin tayi tana mayarwa kitchen, acan ta tsaya dakyar ta shanye ruwan shayin tanaji kamar zata kama da wuta saboda bacin rai.

Shinkafarta data dora ta duba taga ruwan ya tsane, ta kashe gas din tana barinta a cikin tukunyar ta wuce dakin bacci, alwala ta sakeyi jin har ana kiran isha'i.

A daddafe tayi sallah tana idarwa ta janyo wayarta tana bude whatsapp ta lalubo chat dinsu da Asma, ita kadai ce kawarta da zatace suna maganar komai a yanzun, kuma bazawara ce, a FCE suka hadu.

Ita Nuriyyar ma ce ta manne mata saboda ganin yanda tafi kowa wayewa da kudi a ajin.

Har suka zama kawaye, dan Nuriyya na bala'in so ace tana tare da manyan mutane.

'Asma mutumin nan bashi da kirki wallahi, kinsan dai yanda azumi yake bani wahala ko da nayi sahur balle yau da muka makara, dakyar na soya doya kinji masifar da ya sauke mun'
Kafin kace meye Asma harta karanta sakon
'Ya dauko miki yar aiki kema, kina auren mutum kamar wannan zaki zauna kina shiga Kitchen, ke banzar ina ce, narkewa zakiyi saiya dauko miki yar aiki"
Numfashi Nuriyya ta sauke, duk yanda zata misaltama Asma halin AbdulKadir din ba zata fahimta ba
'Kika san magana nawa nai mishi?

Taurin kan shi yafi karfina, yace ba zai dauko ba fa, kuma nasan ba zai dauko din ba'
Kawunan mamaki Asma ta turo mata tana dorawa da rubuto
'Lallai ma, saiki zauna kina kwasar bakin ciki ai, shisa kinganni, auren nan ya gama fita kaina wallahi, tunda na tungule aurena na biyu naji ko zanyi wani ba nan kusa ba, bazan zauna wani katon banza na batamun rai ba.

Ga mutane nan kaca-kaca suna lallabani, sha'anina kawai nakeyi.

Kudi na shigomun ta ko ina'
Shiru Nuriyya tayi tana tauna maganar, da gaskiyar Asma, kafin igiyar aure ta daureta da AbdulKadir free take jinta, babu nauyi ko tunanin kowa, inda take so nan take zuwa, amman yanzun tana iya tambayar AbdulKadir zataje waje ko baya gari yace ba zata ba, iya wannan ta kasa sabawa dashi, dan auren Anas mayafi take dauka in yana nan tace mishi ta fita, idan baya nan tayi gaba abinta.

Balle kuma yanzun ga maganar girkin nan da sauran ayyuka, ta shiga wani irin matsatsi cikin kwanaki kadan da bata taba hangowa ba, ko kafin kwanakin nan, zasuyi waya da AbdulKadir, zasuyi chatting ko yayane, zaizo suyi hira tana kwance a jikin shi.

Amman tanajin wani abu can kasan ranta da ta rasa menene.

Sai yanzun takejin farin cikine cikakke bata dashi, ba zatace ma ga asalin yanda yake ba, dan inta taba shigar shi a bayama ta manta.

Yanzun ne kuncinta ya karu, rayuwar a cunkushe take jinta.

Data dinta ta kashe batare da ta amsa Asma ba.

Ta ja jiki ta haye gado ta kwanta, gara ko bacci ta samu tayi watakila zuciyarta zatayi mata sanyi-sanyi.

Tana nan kwance taji shigowar AbdulKadir din ya wuce bandaki kan shi tsaye, ruwa ya watso ya fito ya saka gajeran wando dan baiga towel din shi ba
"Nuriyya ina towel dina?"
Ya bukata, kai ta dan dago, bata ganin shi sosai saboda ta kashe fitilar wayarta, tashi kuma ya ajiye a bandaki, tadan hasko dakin kadan.
Chapter 85 · 0% Book details