← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 94

Sashe 47

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai lokacin take karewa barikin sojojin kallo, saidai saurin da AbdulKadir yakeyi ya sata maida hankalin ta kanshi tana binshi kamar wadda aka jona ma battery.

Tafiya sukayi har bakin kofar wajen tana mamakin ganin motar Yassar, dan batasan dasu da abokan AbdulKadir din akazo rakoshi ba, hotel suka kama, sun dauka rashin son hayaniya yasa AbdulKadir kama nashi dakin daban, kuma nesa da nasu, tunda gidan nashi daki biyune kuma su Anty anan zasu kwana suma.

Saida yace ma Hajja a gaya musu karsuzo, kowa yai zaman shi ta balbale shi da fada kamar yai mata laifi.

Ga gidan nan suyita kwana, shikam da matarshi a hotel zasu kwana.

Batace mishi komai ba har suka shiga motar yaja su, a gajiye take jinta.

"Hamma nagaji wallahi, jikina ciwo yake..."
Ta fadi ganin har lokacin basu kai inda zasu kai ba
"Mun kusa..."
Ya fadi yana shan kwanar da zata kaishi hotel din, shiga ciki yayi ya samu waje yai parking din motar.

Tukunna ya bude mata ta fito, a gajiyar da takeji bin AbdulKadir da yake rike da hannunta tayi duk inda yayi da ita, har suka karasa bakin wani daki ya bude yana jan hannunta suka shiga ya mayar da kofar ya rufe.

Hannun nata ya sake kamawa yajata kan gadon ya zaunar da ita, takalmanta ta cire tana kare ma dakin kallo, tana mamakin yanda batajin tsoro ko dar a zuciyarta, sanin AbdulKadir din bazai tabayin abinda zai cutar da ita ba.

Abinci taga ya dauko yana fadin
"Sakko muci..."
Kai ta girgiza mishi a hankali
"Jikina namun ciwo..."
Gira ya daga mata
"Shine ba zakici abinci ba?

Sauko kafin ranki ya baci"
Turo labbanta da har lokacin da sauran janbakin kwalliyar data wanke a jiki tayi tana saukowa, hannu yasa yana zare mayafin da taki cirewa ya ajiye shi a gefe batare dayace mata komai ba.

Itama batai magana ba ta dauki cokalin tana sakawa cikin abincin, tare sukaci, turawa kawai tayi, tagode ma Allah da bai mata magana ba.

Mikewa taga yayi ya shiga bandakin dake cikin dakin, karar ruwa ya tabbatar mata da wanka yakeyi, ya jima kafin ya fito.

Tanajin wayarshi na kara, bata ko motsa daga inda take ba ballantana tai kokarin daga wayar.

Harya fito daure da towel a kugun shi dayasata dauke idanuwanta daga kanshi, wayar ya karaso ya dauka.

Anty Talatu ce, hidimar bikin yasaka shi samun lambarta.

Dagawa yayi yana fadin
"Hello..."
Daga dayan bangaren yaji tace
"Ina kukaje AbdulKadir?

Kasan dai kowa ya kwaso gajiya ko?

Kwanciya zamuyi ka dawo da ita haka"
Kankance idanuwan shi yayi
"Kuyi kwanciyarku kawai, zamu kwana a hotel"
Ya fadi
"Hotel?"
Anty Talatu ta maimaita da matuqar mamaki a muryarta
"Hotel fa AbdulKadir..."
Dakuna fuska yayi yana fadin
"Saida safe"
Ya kashe wayar tashi gabaki daya.

In ba zasu kwanta ba su nemi motar Kano su juya a daren.

Bayason wani dogon surutu shisa ya kashe wayar gabaki daya.

Towel din ya kwance yana barin gajeran wandon dake jikinshi ya koma bandaki ya ajiye.

Kan gadon ya karasa yana shirin kwanciya kenan yaji ana kwankwasa mishi daki, tashi yayi yaje ya bude kofar yana tsayawa a bakinta ganin Yassar na sauke waya daga kunnen shi
"Daukota kayi ka kawo nan?

Saurin me kake AbdulKadir?"
Dakuna ma Yassar fuska yayi
"Ina da ikon dauko matata in kaita duk inda yaimun"
Ya ba Yassar din daya dafe kai amsa
"AbdulKadir...

Oh Allah na, ka tashi ka mayar da ita...

Meyasa zaka daukota?

Kasan surutun da zaka jama Hajja kuwa?

Me yasa baka da kunya ne"
Hamma AbdulKadir yayi dan bacci ne a idanun shi
"Wallahi bazan mayar da ita ba, ai nace ma Hajja karsu zo, kar suzo saboda za'a takurani, za'a shiga rayuwata, bata fada musu ba.

Ni kabarni..."
Baki a bude Yassar yake kallon shi kafin yace
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
Kallon shi AbdulKadir yakeyi
"Ka daina yi kamar anyi mutuwa fa...

Ba zaisa in mayar da ita ba.

Da ka wuce ka kwanta zaifi maka alkhairi..."
Ya karasa maganar yana rufe kofar a fuskar Yassar da yake tsaye.

Cikin dakin ya shigo inda ya samu Waheedah a zaune tanajin duk wata kunyar duniya ta tattarar mata waje daya, batajin zata iya komawa gidan nan ta hada idanuwa dasu Anty.

Amman batasan ya zatayi da AbdulKadir bane ba.

Yanzun ma hannunta ya kama yana mikarwa ya dora kan gadon.

Hawa yayi shima yana kai hannu ya kashe musu kwan dakin, kwanciya yayi yana jan Waheedah ya kwantar da ita kan kirjin shi yanajin wata irin nutsuwa na saukar mishi.

Yanda yakejin bugun zuciyarta a kirjinshi yasa murmushi kwace mishi
"Baki da hankali Waheedah...

Kiyi bacci nima bacci zanyi..."
Yai maganar yana kara gyara mata kwanciya a jikin shi, da gaske yake mata baccin zasuyi.

Bayajin yin bacci shi kadai ne shisa yaje ya dauko ta, addu'a yayi tana jinshi ya tofa musu, amman ta kasa koda runtsa idanuwanta ne balle bacci ya dauketa, saida taji numfashin shi ya canza alamar bacci yake da gaske tukunna ta sauke wata irin ajiyar zuciya da batasan tana rike da ita ba.

Hannunta daya ta dora kan kirjinshi tana gyara kwanciyar ta, tana godema Allah daya nuna mata zama matar shi.

Kanta ta gyara kan kirjinshi, bugun zuciyar shi na nutsar da wani abu a cikin nata kirjin har baccin gajiya yai gaba da ita...!
*#TeamAbdulKadir*
*#TeamWaheedah*
*#AnaTare*
*#SonSo*
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
"Waheedah..."
AbdulKadir ya sake kira a karo na hudu, fuskar shi dauke da murmushi, baisan kalar gajiyar da tayi ba, sallar asuba ma daya tasheta kallon shi ta dingayi kamar ya kwace mata wani abu, daya jasu sallar suka idar, yana kallonta taja jiki takoma kan gado, ko hijab bata cire ba.

Yanzun ma hannun shi da yake kan kafadarta take turewa tana shagwabe mishi fuska
"Me zanyi?"
Ta tambaya muryarta cike da bacci, har lokacin idanuwanta a rufe suke, murmushi yayi har hakoranshi suka fito.

Gyara zaman shi yayi gefenta yana saka hannuwan shi duka biyun ya dagota hadi da girgizata
"Ki tashi Waheedah....

Hamma zai kasheni inya dawo bamu shirya ba, idan mukaje gida sai kiyi baccin..."
A hankali take bude idanuwan ta, tanajin kanta kamar an dora buhun siminti, duk wata gaba da take jikinta ciwo take mata, bata taba gajiya irin wadda tai daga satin bikin zuwa wayewar garin ranar ba.

Kallon fuskar AbdulKadir da yake mata dariya tayi, tana tunanin inda take kafin komai ya dawo mata.

"Hamma..."
Ta kira tanajin kunyar duniya ta tattaru ta rufe ta.

Dariya yayi
"Ki tashi ki watsa ruwa mu tafi..."
Kai ta daga mishi tana bin hannuwan shi da suke rike da ita da kallo, hakan yasa AbdulKadir sakinta, ta dayan bangaren ta ja jikinta ta sauka, kanta a kasa ta wuce shi zuwa bandakin tana rufo kofar, wani numfashi da batasan tana rike dashi ba ta sauke.

Ruwa ta watsa tana mayar da gabaki daya kayan da ta shiga dasu, tukunna ta fito.

AbdulKadir na zaune inda tabarshi yana danna wayar shi, sai lokacin ta tuno da tata wayar tana gida cikin jaka.

Hakan kuma na tuna mata da su Anty Talatu da suka bari da yanda zata fara hada ido dasu yanzun.

"Hamma..."
Ta kira cikin tashin hankali, dago da idanuwan shi yayi yana kankance su akanta
"Ina zamuje?"
Ta bukata, da mamaki yake kallonta
"Gida..."
Ya amsa a taqaice, kai ta girgiza mishi, tana sashi daga mata gira cikin alamar tambaya
"Su Anty na nan, ban san me zance musu ba..."
Bude baki yai da niyyar amsata, kwankwasa kofar da akayi ya hanashi.

"Wallahi badan Waheedah ba da tuni mun tafi...yanzun ma bazan sake magana ba..."
Yassar ya fadi daga wajen dakin, da alamun ranshi a bace yake, mikewa yayi yana daukar hijab din Waheedah ya karasa inda take tsaye, juya hijab din yayi zuwa dai-dai tukunna ya juyo da wajen kan yana saka mata, damtsen hannunta daya ya rike yana jinshi kamar kara a cikin hannun shi, gyara mata zaman hijab din yayi sosai, ya juya ya koma ya dauko dankwalin kayan nata, hannunta ya sake kamowa ya saka a ciki, kallon shi kawai takeyi
"Sadauki su Anty na nan....

Dan Allah...

Bansan me zance musu ba"
Waheedah take fadi muryarta a karye, ko inda take AbdulKadir bai kalla ba, wayarshi da wallet ya dauka ya saka a aljihu, yazo ta gabanta ya wuce, saida ya zira takalman shi tukunna ya dauko mata nata yana ajiyewa a gabanta.

"Hamma..."
Idanuwanshi ya kankance mata
"Ki zabi abinda zaki cemun guda daya..."
Da sauri ta amsa shi
"Sadauki..."
Kai ya jinjina mata yana dorawa da
"Kisa takalmanki, idan Hamma yaimun fada raina zai baci, naki zai baci kema saboda na shirya tun dazun ke kike batamun lokaci"
Takalman ta saka, idanuwanta na cika da hawayen da batasan dalilinsu ba.

Gaba AbdulKadir yayi tana bin bayanshi suka fita daga dakin, tsaye tayi ya kulle kofar, kanta a kasa yake, koda ya kama hannunta binshi kawai takeyi, inda duk ya cire kafarshi nan takw saka tata, daya tsaya bada mukulli ma a reception, tsayawa tayi batare data amsa gaisuwar da matar tayi mata ba, asalima ko dagowa batai ba balle taga kalarta, tana tunanin da idanuwan da zata kalli su Anty Talatu ne.

Har bakin motar Yassar suka karasa, yana tsaye daga waje, addu'a Waheedah takeyi kar Yassar yai mata magana, shima ganin kanta a kasa yasa shi kin ce mara komai, Allah ya hadata da wani irin miji da sukai hannun riga shida kunya.

Shi kanshi Yassar din tayata jin kunyar abinda AbdulKadir yakeyi.

Wata irin harara Yassar ya watsa ma AbdulKadir yana f
"Wallahi da ka kara minti biyar da saidai ku nemi abin hawa..."
Dakuna fuska AbdulKadir yayi yana amsawa da
"Na tashi lafiya Hamma, thank you, fatan kaima ka tashi lafiya?"
Wata hararar Yassar ya watsa mishi dan yasan gatse yai mishi, zagayawa yayi ya bude motar ya shiga.
Chapter 47 · 0% Book details