← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 94

Sashe 34

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana jin yanda bata da wani wajen saka kowa a zuciyarta, Abdulkadir ya cike ko ina
"Ina son shi Nuriyya, ina son Hamma, wani irin so da bana tunanin inda zai kaini, saboda bansan ko zuciyar shi zata dokamun yanda tawa take doka mishi ba, amman ina son shi, ban damu ko zai soni ba shima..."
Dariya Nuriyyar tai mata lokacin tana tambayarta ko a film din Hausa taji kalaman, to a watannin nan ma sam bata ma Nuriyya zancen Abdulkadir din.

Dan hankalinsu ba'a kwance yake ba.

Tunda satin bikin ya kama, Nuriyyar ma tayi wani irin sanyi naban mamaki, ko magana batayi sosai.

Kamu kadai zasuyi washegarin ranar juma'a, ran asabar a daura aure hadi da yinin biki, kawayensu na islamiyya duk sunzo, harda kawayen Nuriyya na FCE dinsu duk sunzo suma yin lallen da Anty ce ta dauki nauyin shi.

Abba kam Allah kadai yasan me yayi musu, dan data shiga gidan Mama na mata godiya sosai.

Mami ta siyi kayan kitchen masu yawan gaske, tunda aka saka ranar take siya tana ajiyewa a hankali a hankali.

Duk da a yanayin da auren yazo ma Nuriyya bai hana Waheedah jin dadin yanda danginta suka hidimtawa Nuriyyar ba.

Kusan duka hidimar bikin Waheedah ce tsaye akai.

Daga kan dinkunan da Nuriyya zata saka, itace mai zirga-zirga wajen tela, haka sauran hidindimun da za'ayi.

Tunda satin ya kama kuma rabon da suyi magana da Abdulkadir.

Har wayar shi ta kira a karo na farko, tajita a kashe.

Duk sakkonin data tura mishi a whatsapp basu je ba.

Tana fada mishi hidimar bikin da sukeyi.

Yanzun ma Whatsapp din ta sake budewa tana bashi labarin zirga-zirgar da tayi, da kunshin da za'ayi musu, da yanda take tunanin zaman kunshin.

Saida ta ajiye wayar tukunna take tunanin saida satin bikin ya kama tukunna take fada mishi.

Yazid ne ta fadama da suka gaisa kamar yanda sukanyi lokaci zuwa lokaci.

Sai taga kamar Abdulkadir din.

A kasan zuciyarta take addu'ar Allah yasa lafiyar shi, shirun nashi ya fara mata yawa, inda tana ganin sakkoninta sun tafi ya karanta, tasan yana lafiya, amsata ne kawai baiyi ba.

Kunshin akai mata itama, suna dan hira da kawayen Nuriyya, dan ita ta lafe a gefe daya tana kallon kunshin dake hannunta, tana jin kamar bata cikin gangar jikinta, kamar ruhinta ya fita daga jikin ya koma gefe yana kallon abinda yake faruwa da ita, abin yana mata kamar mugun mafarkin da zata iya farkawa daga shi kowanne lokaci.

Bata hango ma kanta auren Anas ba kona minti daya, inda tasan hakan zai faru da ta jima da sallamar shi ta hakura da kwadayin hidimar da yake mata.

Tasan Baba fiye da kowa, idan ba mutuwa tayi ba baza'a fasa auren ba.

Amman tana jin da gaske mutuwar zatayi idan aka daura auren.

Ba zata iya zama da Anas ba, bata hango rayuwar aure dashi ba, ko bikinta ba haka ta hasasoshi ba.

Saboda ta hango auren hamshaqin maikudi, biki irin na alfarma, gida tanqameme da iyayenta ba zasuyi tunanin kayan daki ba.

Duk da taji Baba na fadawa Mama cewar Abban su Waheedah ya siyi kayan daki, katifa kawai zasu siya.

Tana kuma da tabbacin masu kyaune, za'a saka mata kayanta a gidan da bai cancanta ba.

Gyara zama Nuriyya ta sake yi, sosai takejin abin kamar a mafarki.

Waheedah da take ta hira da kawayenta suna dariya take kallo, tana jin wani nauyi a kirjinta.

Yanda kawayenta na FCE da basu taba ganin Waheedah ba suke zancenta yai mata zafi, yanda take shiga zuciyar duk wanda yaganta lokaci daya na tsayama Nuriyya a makoshi.

Yanzun yanda take dariya na kara hada mata zafi, babu abinda take tunani sai kanta, da za'a daureta a auren Anas cikin kwanaki biyu, Waheedah zata ci gaba da hidimarta babu nauyin auren kowanne talaka akanta.

Zata iya samun maikudi ta aura, karshen abinda take si ya faru kenan.

Zata karasa mutuwa idan Waheedah ta samu Abdulkadir, shisa take addu'ar karya taba kallon Waheedah din da wannan niyyar.

Bazai taba yiwuwa a liqa mata auren Anas, Waheedah kuma ta samu Abdulkadir ba.

Sai dai ko bata same shiba, tasan zata samu wani wanda yafi Anas din kudi, zata samu abinda ita bata samu ba kamar koda yaushe.

Hakan kadai idan tayi tunani tanajin kamar zatayi hauka.

Ko kadan rayuwa batai mata adalci, Waheedah ta zama kamar kaddara ta shigo da su rayuwar junan su dan ta nuna ma Nuriyya abinda duk take son zama amman yai mata nisa.

Idanuwanta ta lumshe, alkawari taima kanta ta gama zubda hawaye akan abinda yake faruwa, tunda Anas yace yaji yagani, zata ga ko zai iya jure zaman aure da ita.

Dan ta gama shirya mishi wulakancin da zaisaka shi dana sanin aurenta.

NDA KADUNA
Wanka ya fito, daga shi sai gajeran wando, da towel rataye a wuyan shi.

Ahmad da shi kadaine abokin shi a zaman shi makarantar horar da sojojin tunda yazo ta shekaru hudu da wani abu, har yana shirin fita kuma, dan watannin daya rage musu bashida yawa.

Suna shekararsu ta karshe kenan.

Babu ruwan shi da kowa, in baka shiga lamarin shiba, sai abinda bazai iya kaucewa bane kawai zai hadaku.

Ko wajen motsa jiki, ko training, ko a aji, wani abu dai daya zama mishi dole, saboda akwai masu saurin daukar zafi irin shi.

Saidai bakowa yake jurewa hukuncin manyansu idan fada ya kaure ba.

Tun suna mamakin taurin zuciya irin na Abdulkadir harsun bari, shisa zuwa yanzun babu mai shiga sabgarshi sai ta kama, a yan Terma five kenan, balle kuma wanda suke kasan shi, har basaso wani abu ya hadasu da Abdulkadir din.

Zai dakeka kamar ya samu ganga, musamman idan ya tashi yana jin bacin rai, in ya samu wani ya huce a kan shi yakanji ya dawowa dai-dai.

"A.

Bugaje"
Ahmad yace kamar yanda kowa yake kiranshi a NDA din.

"Baka gyara wayar nan ba ashe?"
Screen dinshi ya fashe, a kwana biyu yana dan samu ya amsa kira idan ya shigo, saita kara faduwa, yaje ya gyara dinne baije ba.

Yassar ma a wayar Ahmad din yake kira su gaisa.

"Zan gyara"
Ya fadi a takaici yana karasawa kan gadon ya kwanta.

System dinshi ya janyo da take ajiye kan tebir din da yake dakin, budewa yayi, hannuwan Waheedah da kunshinta na cika screen din.

Har yau baiga kunshin da yai mishi kyau kamarshi ba
"Hannuwan nan namun kyau wallahi, ina ma in gano yarinyar da take da shi"
Ahmad ya fadi yana miqa kanshi dan yaga hango sosai.

AbdulKadir yakai hannu ya latse system din yana kasheta gabaki daya.

"Au dan bakin ciki kar ingani?"
Yai maganar yana dariya.

Har duba system din yayi baiga hoton ba, ya rasa kalar boyan da Abdulkadir yai ma hoton, idan zai mutu yana tambaya ko yasan mai hannun ne, ko yana da alaqa da ita kamar yanda yai zato da farko bazai kulashi ba ballantana ya samu amsa.

Kamar yanda yanzun ma bai kulashi ba.

A gidansu Abdulkadir banda Yassar baisan kowa ba, sai Hajja dan sukan gaisa idan ta kira Abdulkadir din koshi ya kira, sai Zahra da itama suna waya, itace ma daya tambayi AbdulKadir din ko kanwarshi ce ya samu amsar
"Ban damu da ka kusa zama cikakken soja ba, zan karyaka Ahmad, da gaske zan karyaka..."
Yayi dariya sosai, kuma hakan ya tabbatar mishi da cewa kanwar Abdulkadir din ce.

Akwai yarinyar da yake yawo da hotonta a wallet din shi.

Wasu lokuttan kuma yakan cire hoton ya saka a aljihun shi, duk idan aka bata mishi rai Ahmad na kula yakan saka hannun shi a aljihun shi, kamar hoton nada wani sihiri da zai hutar da fushin shi.

Duk yanda yake so ya tambayeshi alaqar shi da yarinyar hoton saiya kasa, saboda a bayyane yake.

Tana da muhimmanci na gaske a rayuwar shi.

Bai dai taba nuna alamar yana da budurwa ko yana son wata ba.

Idan har hirarsu ta tsawaita to ta dangancin aikin da suke gab da fuskanta ne na kare kasarsu.

Sai dai watanni kusan bakwai da suka wuce, yakanga Abdulkadir din manne da wayarshi duk dare, ba daddanawa yake ba, da alama dai yana karanta wani abinne, yakan kuma ga yana murmushi shi kadai inya zauna da wayar a hannun shi.

Gashi ya bude whatsapp din da babu yanda baiyi dashi ya bude ba, yaki.

In kuma ya dauki wayar Abdulkadir din dan yai kira ko wani abu, banda yan gidansu da zaiga Hamma wanne, ko Adda wance, sai su Zahra, baya ganin kiranshi da kowa sai lambar daya sakama 'Wahee'.

Yakan kuma ga saqoninta na shigowa wasu lokuttan.

Baida tabbas, amman yana alaqanta hotonta ne Abdulkadir yake yawo dashi.

Juya mishi baya Abdulkadir yayi, yana jan pillow ya dora hannuwan shi akai, dan baya sakawa a kanshi, koya kwanta yasa pillow daya fara bacci yake zarowa ya dora hannunshi akai.

Gashi har yanzun kwanciyar jarirai yake, jikin shi a dunqule haka yake bacci.

Idanuwan shi ya lumshe, hoton Nuriyya na mishi yawo kamar koda yaushe, tun yana kokarin danne shi harya haqura yabarshi.

Ya daina kokawa da zuciyarshi akanta, zuwa yanzun ya fahimci zuciyar shi na doka mata.

Zai wani abu akai, saiya fita daga NDA ya dan samu nutsuwa, yanzun koma menene yake ji dole ya jirashi ya nutsuwa tukunna.

Lokaci irin wannan hirar Waheedah yakan karanta, har tai mishi saida safe, yakan koma baya yaita sake karantawa har saiya fara jin bacci.

Amman kwana biyu hakan baya samuwa saboda bai gyaro wayarba.

Yana kewar hirarrakinta, dan takan hana mishi tunanin Nuriyya irin haka, takan debe mishi kewar gida da gujema ganin Nuriyya ya hanashi zuwa.

Sosai surutun ta yake mishi dadi
'Hamma kasan me ya faru yau'
Yakan karanta sakkoninta da sanyin muryarta, har yanayin idanuwanta yakan gani, kamar tana cikin dakin tare dashi.

Idan an bata mishi rai yakan lumshe idanuwan shi yaji muryarta cikin kanshi
'Banda saurin fushi Hamma, dan Allah banda saurin fushi kaji'
Takan fada mishi haka a sakkoninta, tana saka murmushi kwace mishi.

Inba ita ba, babu wanda ya isa yana bashi umarni haka, ko abinci takan mishi magana yaci, karya zauna da yunwa, wata rana sunanta kawai zai rubuta, zata ce mishi ya ajiye wayar ya kwanta.
Chapter 34 · 0% Book details