← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 94

Sashe 73

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duka cikin su babu wanda yasan da maganar auren AbdulKadir din, Nabila ce taje gidan ta dawo musu da labarin, ita Anty tafi awa daya a zaune jin Nuriyya ce AbdulKadir ya aura, kafin daga baya taje har bangaren Mami tana sauke takaicinta a can, dan ca tayiwa Mami lokacin suje su taho da Waheedah din tunda AbdulKadir bashida hali ballantana kunya, murmushi kawai Mami tayi duk da a idanuwanta zakaga tsantsar damuwar da take tattare da ita.

Kawaici irin na matar har mamaki yake ba Anty.

Shisa take ganin girmanta ba kadan ba, dan da Waheedah yarta ce ikon Allah ne kawai zaisa ba zata kashe aurenta da na AbdulKadir ba, tunda farko ma bataga dalilin da zaisa ta dauki yarinya ta bashi ba, musamman mai sanyin hali irin na Waheedah.

Numfashi Anty ta sauke
"Bansan me kikai ta bari a ranki har zuwa lokacin nan ba, ni bazan baki hakuri ba Waheedah, amman kije gida kiyi magana da Maminki, nasan kawaici ba zai barta furta komai ba, kije taga kina lafiya ba wai a waya ba"
Hannu Waheedah takai tana share hawayen da taji sun zubo mata.

Cikin sanyin murya tace
"Idan gidan zaki koma bari mu wuce tare"
Kai Anty ta jinjina mata, ba gida zata koma ba, amman hidimarta zata jira, inta sauke Waheedah din saita sake fitowa.

Hijab dinta ta dauko, sai jakar goyon Ikram din ta sakata a ciki tana goyata ta gaba ta tallabe, Fajr zata tasa Anty ta hanata, sabar yaron tayi a kafadarta, wayarta kawai Waheedah ta saka a jaka ta rike a hannu, mukullin da Hauwa ta bata na gidan guda daya, ko da zata fita ta dauka, sannan tabi bayan Anty.

Kulle gidan tayin suka nufi motar Antyn, a cunkushe Waheedah takejin kanta da zuciyarta gabaki daya.

Da tunani fal a kanta suka nufi gida.

Har suka karasa gida Waheedah batama sani ba, sai da taji Anty ta bude mata kofar motar ta bangarenta, saukowa tayi da Ikram tallabe a kirjinta.

Fajr ya tashi bata ma sani ba, jakarta ta dauka tana ratayawa ta kama hannun shi, ko sallama bataiwa Anty ba ta wuce tana nufar bangaren su, Antyn ma mota ta koma ta fice daga gidan, zuciyarta cike da tunanin Waheedah din.

Da sanyin jikinta ta karasa gida tana shiga da sallama, a falo ta samu Mami a zaune, Fajr kam bai bita ciki ba ya wuce bangaren Hajja, ita ma batabi ta kan shi ba.

Sallama tayi tana cire takalmanta ta karasa, tunda Mami ta amsa ta taji idanuwan ta sun cika da hawaye.

Kan kujera ta zauna kusa da Mami tana sauko Ikram ta kwantar da ita a gefe, hijabinta ta cire, tana saka dan yatsa ta share kwallar da ta taru a gefen idanta, kallon ramar dake kasan idanuwanta Mami tayi, zatai karya idan tace bata kwana da yarinyar tana tashi da ita a rai, kwanakin nan yinsu kawai take badan suna mata dadi ba, duk da Yassar kullum da safe saiya kira ya hadata da Waheedah din sun gaisa, baccin kirki ma ba sosai take samun shi ba, haka takan raya daren da salloli tana yima Waheedahr addu'a.

"Waheedah..."
Mami ta kira tana rasa ta inda zata fara mata magana, maganar cewar bata taya Waheedah jin abinda Nuriyya tai mata ba baima taso ba, har kasan zuciyarta taji zafin abin, musamman ita da tafi kowa sanin yanda Waheedah ta dauki Nuriyyar, amman rayuwar haka take tafiya, wanda yafi kusa dakai shi yafi kowa samun damar cutar ka, yanzun mutanen kirki basu bane wanda zasu dauki abu su baka, mutanen kirki sune wanda zakuyi tarayya tare dasu basu cutar da kai ba.

Auren da AbdulKadir din yayi bai saba addini ba, ya taka matakai da yawa na rashin kyautawa ne kawai a al'adance.

Taso yima Waheedah maganar sai tace mata
'Babu komai Mami, ya rigada ya faru, ki mana addu'a Allah yasa hakan alkhairi ne'
Duk da tabar zancen, wani abu a kasan ranta saida ya fada mata Waheedah na boye kishin da tasan yana damunta ne, ta kuma jima tana tsoron rana irin wannan.

Tana kallon yanda Waheedah take kai hannu tana share kwallar da take tarar mata lokaci zuwa lokaci, numfashi Mami ta sauke
"Waheedah..."
Ta sake kira a tausashe, wannan karin kamar hakan Waheedah take jira wani irin kuka mai sauti ya kwace mata, jikin Mami ta kwanta tana kukan da takeji yana fitowa daga kasan zuciyarta inda yake mata ciwo na gaske.

Kuka take da bata tabayin irin shi ba a rayuwarta, kukan ranar da AbdulKadir ya fada mata ya kara aure ta text saboda bai darajata ba, kukan ranar da ya shigo mata da kawarta, Nuriyya da ta dauka yar uwa a matsayin kishiya, kuka take da duk ranar da Nuriyya ta rike AbdulKadir din a gabanta, kuka take daya kamata tayi shi watanni takwas da suka wuce, ta jima tana rike da shi a ranta, yanzun da ta fara bata san ya zata daina ba, muryarta a karye cikin wani irin kuka ta dago daga jikin Mami tana fadin
"Ma...

Mami duk mata...

Duk matan garin Kano da inda aiki yake kai shi...

Mami baiga kowa ba sai Nuriyya....me yasa Nuriyya?"
Waheedah ta karasa maganar tana kai hannu ta dafe kirjinta da yake wani irin ciwo kamar zai tsage.

Kishi takeji har wani duhu-duhu take gani.

Riketa kawai Mami tayi, tasan kukan ma Rahma ne, amman har ranta take jin shi, duk karfin hali irin nata hawaye takeji cike taf da idanuwanta, yanzun tagane kishi ne yake cin 'yar tata
"Kuma Nuriyya ta aure shi, ni bazan taba mata haka ba, bai haramta ba, amman bazan auri mijinta ba...me yasa zata auri nawa?

Mijina Mami, Sadauki ta gani duk fadin Kano...."
Waheedah take fadi batare data sani ba, dan yanda take maganar tana wani irin kuka kasan ba a cikin hayyacinta take ba, sosai take kuka tana sambatun da ba zatace ga daga inda suke fitowa ba, riketa kawai Mami tayi tana jijjigata kamar karamar yarinya.

A jikin Mamin tayi kuka har bacci ya dauketa, banda ajiyar zuciya babu abinda take saukewa, a hankali Mami ta zame Waheedah kan kujerar tana dauke mata Ikram.

Bacci tayi har azahar, lokacin da ta tashi wani irin zazzabi ya rufe ta ruf, dakyar taja jiki ta wuce dakin Mami tayi alwala, sai da taba Ikram tasha dan duk hakurin yarinyar harta fara kuka, tukunna ta samu tayi sallah.

Duk yanda Mami ta lallabata kasa cin abinci tayi, shayi ta hada ta samu tasha rabin kofi, da idanuwa Mami take binta duk inda tayi, har saida ta gama jijjiga Ikram tayi bacci, Mami ta karbeta ta saka zani ta goyata.

Waheedah din na zaune kan kujera, tanajin kamar ta shige ciki dan gujema magana da Mami din.

Cikin sanyin murya Mami tace
"Na dauki ido na saka miki ne tun farko saboda nayi tunanin in har kina da matsala ina da kusancin da zaki sameni da ita.

Bazance miki hakuri ba abu bane me kyau, duk da akan ce idan yayi yawa yana zama cuta.

Babu inda hakuri yake yawa, a zamantakewa ta yau da kullum, ko a zamantakewa ta aure, musamman ma ta aure..."
Gyara zama Waheedah tayi, tanajin yanda hawaye suka cika mata idanuwa, magana Mami ta cigaba dayi
"Ba hakuri bane yake yawa ya zama cuta, rashin yafiya ne, akwai banbanci tsakanin ai maka abu ka hakura bakace komai ba, da ai maka abu ka hakura ka yafe.

Yafiyar itace take saka duk yawan lokuttan da kai hakuri kake samun riba, idan har zaka hakura ba zakayi magana ba kabar abin a ranka bashida wani amfani, gara ka fito da shi kawai..."
Mami ta karasa maganar tana sake sauke muryarta da fadin
"AbdulKadir halin shine ya fito fili, shisa babu wanda ya tambayeshi me ya faru, babu ma wanda yai tunanin yaji nashi uzurin, kowa laifi ya dauka ya dora mishi.

A karo na farko koya dace ko bai dace ba Waheedah, ko da za'a ce nayi son kai zan fadi raina ya sosu da auren Nuriyya da AbdulKadir yayi, bai taka addini ba, amman banji dadi ba ko kadan, saboda halin da zaki shiga nayi tunani"
Wannan karin Waheedah bata koyi kokarin share hawayen dake zubar mata ba, yanda muryar Mami take a karye kawai na kara taba zuciyarta, ita kanta Mamin kokarin tarbe hawayen da suke ta mata barazana take, yanayin Waheedah din na gwada karfin zuciyar ta fiye da yanda ta zata.

"Mutuwar aure tafi yin shi wahala, duk yanda ake ganin da kalamai kawai za'a yita.

Ban taba ganin inda uwa taso mutuwar auren yarta ba Waheedah, ko ya kaddara ta rubuto hakan, ni shawara kawai zan baki a wannan matakin, bazanyi kokarin haramta miki abinda addini ya halarta miki ba, abu daya zance miki, kiyi magana da AbdulKadir..."
Kai Waheedah take girgiza ma Mami wasu sabbin hawayen na zubar mata, har ranta tagaji da auren shi, tanajin idan ta koma komai zai iya faruwa, ciki harda tarwatsewar zuciyarta, ba zata iya daukar wani ciwon bayan wanda taita dauka ba
"Wallahi Mami nagaji, nagaji har raina..."
Waheedah ta fadi cikin kuka, kai Mami ta jinjina mata
"Bance wani abu ba nima, kiyi magana da shi, magana ta fahimta, lokutta da dama aure kan samu tangarda ne saboda rashin tattauna matsala har a samu maslaha, kowa naganin laifin dan uwan shine, babu kuma wanda yake kokarin sauke girman kai ya saurari dayan har a gano bakin zaren, ki fada mishi matsalar ki, ki saurari uzurin shi"
Shiru Waheedah tayi tana share kwalla
"Kina jina?"
Mami ta fadi, kai kawai Waheedah ta iya daga mata, tana sake shigewa cikin kujera.

Numfashi Mami ta sauke, komai baya mata dadi sam, kitchen ta wuce badan tana da wani abu mai muhimmanci da zatayi a ciki ba, sai dan inta ci gaba da kallon Waheedah din hawayen da take ta boyewa ne zasu zubo.
Chapter 73 · 0% Book details