← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 94

Sashe 81

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gidansu Waheedah tace ta sauketa, lokacin gab da magriba, dan anan Hauwa tayi magriba tana ta sauri
"Yau zan sha fada nasani Wallahi"
Hauwa ta fadi hankalinta a tashe, bakomai Yassar yake magana a kai ba, amman Allah yai mata son yawo, shikuma ya tsani taje unguwa tayo dare, tasani kawai taurin kaine irin na mata, dariya Waheedah ta dinga mata, har bakin mota ta rakata tukunna ta koma ciki tana samun Mami a dakinta, gefen gado ta zauna tana fadin
"Mami zan koma"
Numfashi mai nauyi Mami ta sauke
"Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, karkiyi wasa da addu'a, kinsan in kina da matsala waya kawai zaki dauka ki kirani ko?"
Kai Waheedah ta jinjina mata, addu'o'inta Mami ta sakeyi musu tana kara binta da nasiha mai ratsa jiki, tukunna ta dauki Hijab dinta tana barin Ikram ta wuce bangaren Abba, shisa ta kirashi kar yaje gidan Yassar zata taho gida itama.

Da sallama ta tura kofar tana shiga falon Abban da murmushin dake fuskar shi ya nutsa wani abu a zuciyarta
"Abba..."
Waheedah ta fadi cike da farin ciki, bata taba tunanin zata kaunaci wani da jinin shi baya yawo a jikinta da yawa haka ba, tana son Abba da dukkan zuciyarta.

Babu jinin shi a jikinta, amman kaunar shi na ciki ta gauraye, karasawa tayi ta zauna a gefen shi kan kafet bayan sun gaisa
"Kina lafiya ko?"
Abba ya bukata, yana jin dadin ganin murmushin da yake kan fuskarta
"Ina lafiya Abba..."
Numfashi mai nauyi Abba ya sauke
"Kin yi magana da AbdulKadir din?"
Kai ta jinjina ma Abba a kunyace, murmushi yayi ba saita fada mishi ba, yasan sun shirya da A
bdulKadir din, tsakanin mata da miji daman ance sai Allah.

"Babu inda hakuri ya tashi a banza Waheedah, kar wani ya taba sa kiji hakurin ki yayi yawa.

Karki bari halayen kowa ya canza naki masu kyau.

Da yawan lokaci rashin kirkin mutane na gurbata na masu kirki....karki bari hakan ya faru dake kinji?"
Kai ta sake jinjina wa tana furta
"In shaa Allah"
Numfashi Abba ya sauke yana cigaba da fadin
"A lokaci daya kuma karki bari hakurin ki yaja miki raini, ko da zaki yafe in an miki kuskure ki nuna hakan, ba saikin yi da hayaniya ba, tunda ba halinki bane, kiyi a nutse, karki barshi a cikin ki zai cutar dake.

Allah yai miki albarka, Allah ya shirya miki zuri'arki"
Da wani yanayi a muryarta tace
"Amin Abba, Allah ya bamu aron rayuwa mai tsayi tare da kai"
Da murmushi a fuskar shi ya amsa ta da
"Amin..."
Yana dorawa da
"Ba gidan ki zaki koma ba?"
Kai ta sake sunkuyar wa cike da kunyar shi data lullube ta, hakan yasa Abba fadin
"Kije ki shirya ki fito in kai ki"
Mikewa tayi dan ji take kamar zata nutse a wajen saboda kunya.

Babu abinda zata dauka banda Ikram, Fajr na wajen Hajja, kunyar Hajja din takeji dan dazun batasan bakinta ya subuce ta mayar mata da magana ba.

Duk gidan itace ta farko da ta sameta har gidanta bayan taji Nuriyya ta tare ta bata hakuri, ita ta fara nuna mata ko kadan bada son ranta akai auren AbdulKadir din da Nuriyya ba, duk da a lokacin ta nuna ma Hajjan babu komai, bata kwana uku bata kirata taji lafiyarta ba, matar bata nuna mata komai banda kauna ba.

Sallama tayi da Mami tana goya Ikram, ta samu Abba harya fito ma yana motar shi a zaune.

Budewa tayi ta shiga gaba ta zauna tana mayar da murfin ta rufe.

A kofar gida Abba yayi parking yana kiran wayar AbdulKadir din, da ya fito ko takalma babu a kafafuwan shi, kamar baiga Abba a tsaye ba yace
"Waheedah..."
Yana kasa boye farin cikin shi, kunya tasa Waheedah raba AbdulKadir din ta wuce cikin gidan da sauri.

Sai lokacin AbdulKadir ya kalli Abba yana fadin
"Abba...

Ina wuni"
Harar shi Abba yayi
"Sai yanzun kaganni?"
Dan sosa kai AbdulKadir yayi yana karasawa wajen motar Abban ya jingina, yanajin tsakuwoyin da yake takawa da suke tunasar dashi bai ko saka takalma ba.

"Ba yaro bane kai da zan zauna ina maka fada akan duk wani abu na rayuwa, ya kamata ace ka hutar dani haka AbdulKadir, kasan wasu abubuwan sun kamata ko basu kamata ba, bansan me kai mata ba wannan karin, ban kuma san inda ta sami karfin zuciyar yafe maka ba.

Amman banajin ni zan yafe maka idan ka sake taba ta haka, Hajiya Safiyya tace mun Fajr ya fada mata ka ture Waheedah harta fadi, ya kuma yi kankanta ya shirya karyar da baigani ba haka"
Kan shi AbdulKadir ya sadda kasa yanajin maganganun Abban na shigar shi sosai
"Bansan inda ka sami tarbiyar dagama matar aurenka hannu ba, nikam badaga wajena ka dauka ba..."
Abba ya karashe maganar cikin sanyin murya kafin yace
"AbdulKadir..."
Yana saka AbdulKadir din dagowa ya kalli Abba
"Ranar da duk ka sake dagama yarinyata hannu, ka kalli fuskata ba wasa nake da kai ba, wallahi ka daki aurenka"
Rufe fuskar shi AbdulKadir yayi da hannuwan shi biyu yana budeta, kirjin shi na daukar dumi kamar ana gobara a cikin shi, muryar shi a karye yace
"Abba nima dan ka ne...

Itama kace mata idan nayi mata abu ta dinga fadamun ina bata hakuri, kace mata ta daina bari a ranta babu kyau.

Abba ka kalli yanda duk ka tsoratani"
Ya karasa yana goge zufar da take tsatssafo mishi a goshi, amman fuskar Abban babu wani alamar wasa, shikam yanzun kowa yagane raunin shi, rabuwa da Waheedah ne raunin shi, shisa suke son kashe shi duk su huta, yasan da yayi abu zasu dinga mishi barazanar rabashi da Waheedah din tunda sun san hankalin shi tashi zaiyi
"Itama in kirata kace mata a bakin aurena idan tana qullata ta"
Mota Abba
ya bude ya shiga yana mayar da murfin ya wuce, ya yarda akwai mutanen da duk shekarun da zasuyi a duniya rashin hankali bazai taba barin su ba, ciki harda AbdulKadir.

"Kaji Abba..."
Baiko kalle shi ba, ya tayar da motar, murmushi AbdulKadir din yayi
"Nagode Abba...

Zan kiyaye in shaa Allah, zan kiyaye"
Ya sake jaddadama Abban, kafin yaja motar shi ya wuce.

Numfashi AbdulKadir ya sauke yana wucewa cikin gidan.

Shima da magriba Yassar ya dawo dashi, dan asibitin kin sallamar shi sukayi sai da suka karasa mishi wani ruwan da allurar da ta sakashi bacci har kusan magribar, bai jima da dawowa ba, wanka kawai yayi tunda sunyi sallah a hanya.

Har haushin Yassar yaji da yace
'Matar ka bata da hankalin da zaka wuni baka koma gida ta nemeka ba ko?'
Duk da gaskiya ce ya fada, Nuriyya din ko flashing batayi mishi ba, ya kuma ji haushi sosai, dan shi mutum ne mai bala'in son kulawa, shisa tunda ya dawo yake shashareta, ya kuma ga bata damu ba, hidimarta kawai takeyi, yayi alkawarin zai dafata a ruwan sanyi, dan bazai dauki wannan halin ko in kula din nata ba, inma ba da gangan takeyi ba, bangaren Waheedah ya shiga yana samun ta ta fito daga bandaki, da alama alwala tayi, bata ce mishi komai ba ta dauki hijab dinta, shima bandakin ya shiga ya daura alwala yana fita masallaci, zuciyar shi a nutse yake jinta har aka idar da sallah.

Ko azkar bai tsaya yiba ya dawo gida, dan so yake yagan shi a kusa da ita.

Ita kam Waheedah zafi taji ya isheta ta sake watsa ruwa tana idar da sallah, doguwar riga ta saka ta material dinki bubu, yadin blue mai haske, ta dauki hula kalar shi mai cizawa ta saka a kanta, tana jin dadin wutar da suka dawo da ita, dan fitilar waya take ta amfani da ita a dakin, torchlight dinta babu caji a jiki.

Duk da darene jambaki ta tsinci kanta da shafawa a labbanta, tana dan murza mai a hannuwanta, ta feshe jikinta da turaruka masu sanyin kamshi.

Sanda AbdulKadir ya shigo ta sauke ikram kan katifarta, tana kara gyara gadon da yake a hargitse.

Tsaye yayi a tsakiyar dakin, kamshin ta na saka shi lumshe ido, wata irin kewarta na dabaibaye shi.

Har inda take ya taka yana rungumeta ta baya ya sumbaci kuncinta, cikin kunnenta yace
"Ki yafemun Waheedah, dan Allah ki yafemun"
Tanajin yanda maganar ta fito daga zuciyar shi, zame jikinta tayi daga nashi, tana juyowa ta fuskance shi, fuskar shi take kallo sosai, tana saka hannuwanta ta rike kuncin shi, tanajin yanda sai da tadan daga kafafuwanta, girman shi harya daina bata mamaki, kallon shi tayi na wasu dakika kafin ta sauke hannunta batare da tace mishi komai ba, a shirunta yake karantar yafiya, duk yanda idanuwanta suke tabbatar mishi yana da sauran lokaci kafin ta sauka daga fushin da take, zaiyi komai, indai tana kusa dashi duk mai sauki ne.

Gadon ta karasa gyarawa, ta dauki Ikram dake ta bacci ta mayar da ita kan gadon tana ficewa daga dakin zuwa kitchen, tanajin AbdulKadir na biye da ita, mukulli tasa ta bude kitchen din tana turawa, tabar mukullin a jiki, tsugunnawa tayi tana bude kwalaye da ledojin siyayyarta, AbdulKadir na tsaye yanata binta da idanuwa kamar bai taba ganinta ba, ta mishi kyau sosai.

Da ance mishi lokaci zaizo da zaiji shakkarta zai karyata, amman yanayin dake fuskarta yasa shi hakura da duk yanda yake son sumbatarta.

Yanzun ma kasa hakura yayi ya tsugunna kamar zai tayata fiffito da kayayyakin da take ya kamo hannunta da yasha lalle yana dago shi ya sumbata.

Kallon shi Waheedah tayi tanajin yanda ko meye tasa ta lullube kaunar shi dashi yana soma budewa, hakan yasata zame hannunta daga cikin nashi
"Aiki nake Sadauki"
Ta fadi tana dauke idanuwanta daga kan shi, ta dauki ledojin maggi tana dorawa kan kantar kitchen din ta dauko robobinsu ta bude kowane tana juye shi a mazaunin shi.

Baice mata komai ba, kayan ya tayata shiryawa, suna cikin aikin Nuriyya ta karaso wajen da murmushi a fuskarta, wutar da aka kawo yasa ta fitowa falon sai taji motsin yayi yawa shisa ta fito, sosai taji sanyi a ranta na ganin Waheedah din, taliya ce ta samu ta dafa fara, tanayin miyar da ko a ido batai mata kyau ba.
Chapter 81 · 0% Book details