Sashe 43
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aurenta zanyi..."
Numfashi Yassar yaja ta baki yana fitar dashi ta hancin shi
"Baka son ta AbdulKadir, me kayi haka?"
Kafadu AbdulKadir din yadan daga mishi
"Tana sona..."
Wata dariya Yassar yayi batare da yasani bama
"Wai ma meya faru ka sameni kanata hure-huren hanci kamar dragon...
Ba jiya kake mun maganar yanda take sona ba?"
Kai Yassar ya dafe yana sauke numfashi, sosai yakejin yanda ya kusa kwada ma AbdulKadir mari
"Da nace tana sonka bance kaje kace zaka aureta baka shirya ba"
Gyara zaman shi AbdulKadir din yayi
"Eh haka Abba yace ba'a aure babu shiri, shisa ba za'ayi nan da sati biyu ba, tare da nasu Hamma Mubarak za'a hada, wai za'ayi su lefe...
Zanje inma Hajja maganar ma...
Zan tara kudin in shaa Allah, albashina da dan yawa...
Zai isa idan na tara..."
Ciwon kai Yassar yaji ya saukar mishi, abinda yake nufi daban, abinda AbdulKadir yake fahimta daban, ba shiri na hidimar aure yake mishi magana ba, shiri na zaman aure da yake bukatar fiye da soyayya.
"AbdulKadir...
Baka son ta"
Dakuna fuska AbdulKadir yayi
"Tana sona Hamma..
Me yasa bazai ishe mu ba?"
Ya karasa maganar yanajin ranshi ya soma baci, baiga dalilin da zaisa Yassar ya dinga maimaita mishi magana daya kamar itace abu mai muhimmanci a maganar auren, ya tambayi Waheedah tace tana son shi da aure, shima kuma a shirye yake yai zaman aure da ita, bai kuma san meye yafi wannan muhimmanci ba.
"Bacci nake ji...
Dan Allah kabarni nikam.
Na rigada nagama magana da Abba, auren nan zai faru...
Maganganun duk da muke din nan basu da wani muhimmanci tunda ba zasu canza komai ba"
AbdulKadir yai maganar yana komawa ya kwanta hadi dajan mayafi ya rufe jikin shi.
Kai Yassar yake girgiza mishi yana dana sanin furta mishi cewar Waheedah nasan shi, har ga Allah bai taba tunanin ba soyayya suke ba, da yasani da bazai taba tayar ma fa AbdulKadir da maganar ba, amman lokaci ya kure.
Kamar yanda AbdulKadir din ya fadane, maganganun shi ba zasu canza komai ba.
"Dan Allah karka cutar da ita, karkai amfani da soyayyar da take maka ka cutar da ita AbdulKadir, marainiyace, karka cutar da ita..."
Yassar yai maganar da wani irin yanayi a muryarshi, a kasan zuciyarshi yana addu'ar kar AbdulKadir din ya taba dana sanin auren Waheedah din, dan yanajin ya yanke hukuncin aurenta cikin gaggawa, ko da ya shirya zaman aure da ita, yayi gaggawa yagane hakan a jiya kawai.
A wani bangaren yana fatan akwai wani bangare a kirjin AbdulKadir din da yake dokama Waheedah batare daya sani ba.
"Ka jamun kofar inka fita"
AbdulKadir ya amsa kamar baiji maganganun da Yassar din yayi ba.
"Allah ya tabbatar da alkhairi..."
Cewar Yassar yana ficewa yajama AbdulKadir din kofa, idanuwan shi ya lumshe, dan bashi Yassar zai saka tunani ba, bacci mai karfi ya dauke shi.
Ba zatace ga yanda satika biyu suka wuce mata ba, tasan dai a cikinsu abubuwa da dama sun faru, harda maganar da Mami tai mata kan auren AbdulKadir din itama kamar Abba tana son karin tabbaci ne.
Data samu din kuma addu'a tai musu
"Allah yasa alkhairin juna ne ku, Allah yasa muku albarka a tafiyar dake gabanku Waheedah, Allah ya yafe ma mahaifinka ta kyautata makwancin shi"
Ko ita kadai ta zauna addu'ar Mami kan sanyaya wajejen da batasan suna mata zafi ba.
Tun yan gidan na mamakin maganar auren suma har sun daina, dan Zahra ma saida tace mata
"Lallai ma, ki rasa wa zaki aura a duniyar nan sai Hamma AbdulKadir?
Ya gama zaneki ya lallabo kuma zaki aure shi...Tafdin..."
Dariya kawai takanyi, Mubarak ma da yakai ta makaranta a cikin satikan saida yai zancen
"Zuciyarki bata kyauta miki ba Waheedah...
Ta rasa wa zata janyo muku sai masifaffen nan.
A kafa aka dauramun AbdulKadir saina tsinke nayi takaina..."
Shima dariyar tai mishi a kunyace.
Ba zasu taba fahimtar yanda take son AbdulKadir din ba, ita kanta ba zatacr ga yawan soyayyar da take mishi ba, halayenshi kaf babu wanda ya taba damunta balle ya daga mata hankali, fadanshi kan tsaya mata a rai duk idan yai matashi wasu lokuttan, tana kuma tsoron fadan nashi, sai dai bai taba zama dalilin da zai hanata tunkararshi da kowacce irin magana ba, kuma bai taba sa taji soyayyarshi ta yi ko alamar dishewa ba.
Tana son shi da duk wani abu da yake tattare dashi.
Kwata-kwata tun satin farko take neman wayar Nuriyya bata samu ba, sau biyu ta biya ta makarantarsu bata samunta, sai a sati na biyune ta sameta a waya ashe batajin dadine, har gida taje ta dubata take kuma fada mata sa ranarta da AbdulKadir, tayi mamakin da
'Allah yasa alkhairi'
Kawai Nuriyya ta furta, saidai Waheedah tai mata uzurin cewar dan batada lafiya ne, tadai gyara mata gidan da yai kamar yayi wata baiga tsintsiya ba, ga tarin wanke wanke, kusan duk wani abu da yake kitchen din bashida kyau.
Ko ina ta gyara mata tsaf, har girki tai mata tukunna sukai sallama tabar gidan.
A satin kuma saida ta koma dubata har sau biyu, zancen bikinta dai bai sake hadasu ba, zatai karya wannan karin in tace ranta bai mata wani iri ba.
Ta dai sake mata uzuri da rashin jin dadin auren Anas da takeyi har lokacin, hankalinta baiyi kwanciyar da zatai rawar kafa kan nata auren ba.
Ranar lahadi ce, ba makaranta ke akwai ba, takanje islamiyya a ranakun hutun karshen mako, amman ranar AbdulKadir zai wuce, an tura shi Minna.
Yace mata ba dawowa zaiba sai bikinsu, bazai tafi bata ganshi ba, text dinshi tagani a wayarta
'Ina wajen motar Hamma Yassar'
Mikewa tayi zuciyarta na dokawa kamar zata fito waje.
Hijab dinta ta dauka ta saka, tukunna ta dauki ledar dake ajiye kan gadon, addu'a take kartaci karo da Mami a falon dan batasan kalar kunyar da zataji ba.
Ita da AbdulKadir din ba wani lokaci suke samu su kadai ba tun bayan maganar, yanzun takan samu ya amsata dai-dai a WhatsApp, wani lokacin kuma yana kira, duk da hirar ita zatai mishi, ko in tana mishi a WhatsApp zai kirata yace bacci yake ji ta karasa mishi labarin zai gani da safe.
Wasu lokuttan kuma in tana makaranta yace karta taho ta jira shi zaije ya daukota.
Banda wannan babu abinda zatace ya canja, in sun hadu zata gaishe shi kamar da, zai satai mishi abu kamar yanda yakan satai mishi a baya.
Allah ya amshi addu'arta bata samu Mami a falon ba, kamar marar gaskiya haka ta fice da saurinta.
Wajen harabar motocin ta same shi ya jingina bayanshi da motar, jikinshi sanye da rigar saqi ta sanyi marar nauyi, dogon hannune amman yaja hannuwan rigar sosai, sun tattare daga wajen damtsen shi.
Kallon shi tayi tana daukar hotunan shi cikin kanta dan ya mata kyau sosai da sosai.
"Tafiya zanyi Waheedah..."
Ya fadi lokacin da ta karasa ta tsaya a gefen shi, kai ta jinjina mishi, tana sane da tafiyar kamar tare zasuyita, dan tanajin yanda zai tafi da fiye da zuciyarta, harda kadan daga cikin ruhinta.
Ledar dake hannunta ta mika mishi ya karba yana rikewa
"Ka kula da kanka Hamma...
Banda kin shan magani dan Allah...in bakajin dadi kaje a duba ka kaji?"
Ta karasa maganar tana kallon shi, tasan yana kula da kanshi takowanne fanni banda lafiyar shi, saboda bayason magani, bata taba ganin mutumin da bayason magani irin shi ba.
"Kibarni ba yaro bane ni..."
Yai maganar yana tsareta da kananun idanuwan shi, ita kadai take tsira shi da maganganu haka, take mishi kamar yaro batare data nuna alamar ta raina shi ba.
Yanda take nuna tsoron shi yakan ga hakan har cikin idanuwan ta, amman baya hanata fada mishi duk abinda tayi niyya.
Ledar dake hannun shi ya bude dan bazai iya jira saiya karasa daki ba, inya karasa dinma jakarshi zai dauka Yassar yakai shi tasha.
"Ba anan zaka bude ba Hamma..."
Waheedah tai maganar da murmushi a fuskarta
"Saboda me?"
Ya tambaya yana saka hannun shi cikin ledar
"Saboda haka kowa yakeyi"
Agogo yaji cikin ledar ya dauko yana fitowa dashi hadi da fadin
"Ni ba kowa bane ba"
Ya karasa maganar yana mika mata agogon ta karba, hannun shi ya miqa mata, akwai wani agogon a daure, na sojojine ma, kwance mishi agogon tayi ta daura mishi wanda ta siya din, dubawa yayi yana jinjina kai, nashi agogon ta mika mishi tana jin zuciyarta ta matse waje daya.
"Ki ajiyemun, idan na dawo zan karba..."
Ya fadi, yanayinta yasa shi son yabar mata wani abu, agogon ne kawai abinda yake dashi a yanzun.
Koda bata bashi wani ba yai niyyar cirewa ya daura mata, ganin tayi tsaye tana kallon agogon kamar ya bata wani bangare na zuciyarshi yasa shi karbar agogon daga hannunta, dago idanuwanta tayi tana ware su kan fuskarta.
Bai manta kashedin Yazid na cewar ba muharramar shi bace, ya daina tabata, kawai yayi watsi da kashedin ne ya kamo hannunta yana zagaya agogon a jiki hadi da daurawa.
Dariya yayi har hakoran shi suka fito, ta jima bataga hakoran shi haka ba inba magana yake ba.
"Wahee..."
Ya fadi yana sa tsikar jikinta miqewa
"Wanne irin hannune wannan?"
Yai maganar da dariya a muryarshi ganin agogon na yawo, kwancewa yayi yana saka shi cikin tafin hannunta ta dumtse
"Ki kula da kanki Waheedah..."
Kai kawai ta iya jinjima mishi, kafafuwanta kamar an kwance abubuwan da suke daure dasu saboda sanyin da taji sun mata.
Numfashi AbdulKadir ya sauke har lokacin yana rike da hannunta da yakejin shi dan karami a cikin nashi, tsintar kanshi yai da fadin
"Kice ma duk wanda zai kulaki a makaranta mijin da zaki aura soja ne.
Ki fada musu Second Lieutenant A.
Bugaje ne, yana da kishi fiye da tunani"
Murmushi mai sauti taji ya kwace mata, duk da idanuwanta cike suke taf da hawaye, kewar shi ta fara danneta tun yana tsaye a gabanta.
Batasan hawayenta sun zubo ba saida taji yatsun dayan hannunshi ya share kuncinta.