Sashe 76
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gyara zaman shi yayi yana kokarin saka hannuwan shi duka biyun wannan karin, ture su ta sakeyi da dukkan karfinta tana mikewa, wani irin kallo take mishi da yasa shi jin kamar an watsa mishi ruwan kankara
"Ka kyaleni, kaje ka taba fuskar Nuriyya"
Da mamaki AbdulKadir yake kallonta, kafin shima ya mike yana son hade space din dake tsakanin su, baisan abinda ya kamata yace mata ba, kuma lallashinta yake sonyi, taki bari ya tabata, gabaki daya komai ya cunkushe mishi
"Dan Allah kiyi hakuri Waheedah..."
Ya fadi yanajin shima gab yake da nemo kuka duk inda yake, kilan in ya taga hawaye a fuskar shi sai tagane abinda nata hawayen yake mishi, takawa ya sakeyi, ta dago hannuwanta tana kokarin ture shi, kama hannuwan nata yayi yana sa karfi ya rike su
"Karyewa kike son yi shisa zaki tureni ko?"
Kiciniyar kwacewa takeyi zuciyarta na wata irin tafarfasa
"Nace kiyi hakuri...Dan Allah kiyi hakuri, ba zan kara ba wallahi"
AbdulKadir ya karasa maganar muryar shi na karyewa, har lokacin yana rike da hannuwan Waheedah da take kallon shi kamar tana shirin rufe shi da duka, ga hawayen da bayaso sunki daina zubar mata
"I'm sorry"
Ya fadi da harshen turanci yana dorawa da fadi cikin harshen larabci
"Ana Asif..."
Sosai yake kallonta, tunda yake baisan yanda hakuri yake fitowa daga zuciya ba sai yanzun da yake a gabanta, hannunta daya ya dago ya dora shi a kan kirjin shi inda zuciyar shi ke dokawa kamar zata fito waje saboda tashin hankali
"Su kadai ne yarukan da nake ganewa, idan akwai wani kalar hakurin ki fadamun....nace bazan kara ba, idan akwai abinda nayi miki banda mari ki fadamun duk sai in hada in baki hakuri"
AbdulKadir yake fadi yanajin a wannan gabar kome take so shidin zaiyi indai zata hakura ba zata kara furta mishi kalmar ya saukake mata auren shi ba, hannuwanta take kiciniyar kwacewa, sakar mata yayi, yana kallo tasa ka bayan hannu ta goge fuskarta da har ta kara ja saboda kukan da takeyi
"Kinga fuskar ki harta kumbura, kiyi hakuri kar kanki yayi ciwo Wahee..."
Kallon shi take, tanajin wani tuquqin kishi naban mamaki yana taso mata
"Bakayi tunanin kaina zai ciwo ba ka kara aure ban sani ba?"
Maganar ta dirar mishi cikin kunnuwa tana daukar wasu dakika kafin ta karasa cikin kan shi tana rarrabuwa zuwa inda zai fahimta
"Da kayi auren ka ban sani ba kamar na isa in hanaka, sai ka zabi ka dauki wata daya kafin ka gayamun ta text...Text"
Waheedah ta maimaita maganar cikin gunjin kukan da yaji ya samu wajen zama a zuciyar shi yana daskarar dashi tsaye a wajen, wannan karin ita ta taka tana hade space din dake tsakanin su, cikin fuska take kallon shi
"Bakayi tunanin abinda zanji ba ko Sadauki?
Banda darajar da zan san ka yanke hukuncin da ba rayuwarka kawai zai canja ba harda tawa....
Bai isheka ba sai da ka sake nuna mun duk abinda zanji a kai ba matsalarka bane, ka fadamun ka kara aure ta text!"
Wannan karin da hargowa ta karasa maganar tana ture AbdulKadir din duk da ko motsi ya kasayi, tsaye yake kamar bishiyar da ta samu dashe mai kyau, kalamanta yake ji na saukar mishi da wani irin yanayi da bashida kalaman dora su, kuka Waheedah takeyi mai sauti, zuciyarta na ciwo kamar zata rabu da kirjinta, numfashi take ja tana fitar dashi a wahalce, sai dai kalaman takeji na tunkudedeniya da juna wajen fito mata, tagaji da rike su, tagaji da rike komai
"Da ka fadamun ta text, ko kadan hankalin ka bai baka ka fadamun kawata ka aura ba ko?
Saboda kai ne, AbdulKadir da babu wanda ya isa, darajar kowa a kasan taka take shisa baka fadamun ba sai da ka dauko ta ka kawomun ita cikin gida na....Kawata Sadauki...
Kawata ka aura, idan kaso ka kasheni zaka iya..."
Waheedah take fadi numfashin ta har barazanar tsayawa yake saboda kukan da take tana kuma magana a lokaci daya, amman ta kasa shiru, AbdulKadir din take turewa ko motsi ya kasayi
"Bakayi tunanin ya zanji ba ko?
Shisa duk matan Kano....matan duk da suke Kano.
Me yasa sai ita?
Me yasa zaka sa in raba komai naka da ita?"
Ta karasa maganar wannan karin kamar wadda ta sami tabin hankali, jikinta ko ina bari yake da kukan da take, hannun AbdulKadir din guda daya ta kamo da duka nata biyun tana dorawa akan kirjinta
"Kaji?"
Ta tambayeshi wasu sabbin hawayen na wanke mata fuska tana sake ware hannun shi akan kirjinta inda zuciyarta ke mata ciwo kamar zata fado, wannan karin muryarta da rauni ta fito tana kuma sauka can kasa
"Tun bansan menene so ba zuciyata take doka maka, baka bani dalili ba, ban taba bukatar wani dalili na son ka ba, saboda kaunar ka bata bani wannan zabin ba, dan ban taba fada maka ba shisa bakayi tunanin ina kishin ka ba?"
Waheedah ta fadi tana sauke hannun shi daga kirjinta tana saka yatsunta cikin nashi ta dumtsa
"Duk yanda zuciyata take fadamun yanda take son ka kasance nawa ni kadai, kullum sai na fada mata kai ba nawa bane ni kadai, addini baice ka zama nawa ni kadai ba, nasani Sadauki...dan Allah me yasa ka hadani kishi da ita?
Me yasa ita?
Kawata ce Sadauki?
Ka manta kamar Amatu nakejin Nuriyya?"
Hannun shi AbdulKadir ya zame daga cikin nata yana matsawa da baya taku biyu, kafin ya juya ya sake wani taku biyun, tsugunnawa yayi yana neman iskar da yakeji ta mishi kadan kamar mai asthma haka numfashin shi yake barazana, mikewa yayi har lokacin iska yake nema tukunna ya tantance asalin abinda yakeji, abinda kalamanta suke mishi, bin shi Waheedah tayi tana sake kamo hannun shi, tana jin dumin hawayenta wani na tunkudo wani kafin tace mishi
"Ina zaka je?"
Kai AbdulKadir ya girgiza mata yana son samun wadatacciyar iskar da zai iya fito da sauti kowanne irine, zuciyar shi yakeji kamar an sa hannu a kirjin shi an matse ta ana rabata da duk wani jini da yake jikinta
"Baka duba cewar na dauki ido na kyaleka ba, sai ka dinga zuwa mun da ita kamar kana son nuna mun kawata ce ka aura, saboda ka isa, babu kuma yanda zanyi da hakan"
Waheedah ta fadi da wani irin nisantaccen yanayi a fuskar ta, kai AbdulKadir ya sake girgiza mata yana so tayi shiru ko numfashin shi zai dai-daita kan shi ya rage zafin daya dauka, nata kan take girgiza mishi idanuwanta har wani yaji-yaji suke mata, tana hadawa da jijjigawa kamar yana bacci tana so ta tashe shi
"A gabana kake rike ta, tana kwanciya a jikin ka....kana so ka kasheni tana tayaka...
Zuciyata na mun ciwo...
Sosai zuciyata take mun ciwo...
Bazan iya zama da kai ba, zaka kasheni..."
Cewar Waheedah, kafin a gajiye ta karasa da
"Ba soyayyar ka bace farko na, ba zata samo karshe na ba!"
Hannun shi daya AbdulKadir ya dago yana kama na Waheedah ya cire daga jikin dayan nashi yana dafe fuskar shi da tafukan shi, hadi da jan wani irin numfashi a wahalce, ba zai tuna ranar karshe da wani abu ya same shi yasa shi jin yana son ya ruga wajen Hajja ba sai yanzun.
So yake ya ruga wajen ta kamar yaro dan shekara uku da aka kwacewa abin wasan shi, wata kila idan ya ruga Hajja ta saka hannu ta tarbe shi in zata iya ta daga shi ta rike shi a jikinta hawaye su zubar mishi ya samu saukin abinda yake ji.
A filin duniya, a shekarun shi da Allah ya bashi aron su daga ranar farko zuwa yanzun da yake tsaya baiyi tunanin akwai tashin hankali kalar wanda yake ciki ba.
Tun kafin ya auri Waheedah duk idan ya kalleta akwai raunin da yake tare da ita da yake saka shi jin son yi mata rumfa ya kareta daga duk wani abu da yake a karkashin ikon iyawar shi, lokacin da igiyar aure ta daure su karkashin inuwa daya, bai fito daga masallacin da hakan ta faru ba sai da alkawurra masu tarin yawa, cikin su harda kokarin ganin wani abu bai cutar da ita ba, in har yana da ikon hakan.
Sai dai a tsayin zaman su duk yanda yaso kareta daga hakan, baiyi tunanin kareta daga kan shi ba, baiyi tunanin shi zai iya cutar da ita fiye da kowa ba.
Da za'a tambaye shi mutane uku da zasuyi komai saboda shi, mutane uku da zasu sadaukar da komai dan farin cikin shi, Waheedah zata zamo ta ukku bayan Hajja da Abba.
Da gaske ne ba zai ce ya bude zuciyar shi da soyayyarta ba, kafin ranar da Yassar yai mishi zancen ta, bai taba ko a mafarki hango aurenta ba.
Amman tun kafin hakan ita din bangare ce ta rayuwar shi, ko da bai aureta ba yana da tabbacin labarin rayuwar shi ba zai cika batare da ta fito a shafuka da yawa ba.
Daga ranar daya aure ta yasan cewa ba ita ya fara so ba, amman ita din ce duk wani abu da yake bukata.
Baya tunani mai tsayi a kan kowanne bangare na rayuwar shi, shisa bai taba tunanin hukuncin daya dauka shi kadai ya shafa, shi kadai zai taba harda ita ba, kuskuren farko da yaji yayi a rayuwar shi.
Yake kuma jin shi har cikin kasusuwan shi shine manta duniyar shi gauraye take da tata, manta cewar duk wani mataki da zai taka ko ya taka shi tare da Waheedah ne, abinda duk ya taba shi zai taba ta itama, kamar yanda yake jin duk abinda ya tabata shi ya taba.
Shisa yanzun ciwon da takeji ya lullube shi ruf...!
#AbdulKadir
#LubnaSufyan
#Nagode da dukkan kaunar ku.[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
Tsugunnawa yayi yana fitar da numfashi a wahale, cikin shi ke ciwo saboda hanjin shi da yakeji sun tattaru sun kulle a gefe daya.
Ko ina na jikin shi ciwo yake, har wajajen da bai taba sanin zasuyi mishi ciwo batare da zubar jini ba.