Sashe 37
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Lokutta da dama yakanji kamar harda laifin shi a abinda take fuskata na zama da Abdulkadir, yakanji a kaso dari ma aurenta da Abdulkadir yana da hannu cikin kashi tamanin harda doriya.
Musamman watannin baya haka yakejin duk laifin shine, amman yanzun ta fara rage mishi nauyi.
Duk da can kasan zuciyarshi bazaiso mutuwar aurenta ba, amman hakan bazai hanashi goyon bayan gaskiya ba.
Wannan karin son Abdulkadir baizai rufe mishi idanuwa ba.
Batare dayace komai ba yabi bayanta.
Bazai ce ga yanda yakai gida ba, nutsuwar shi bata taba kwacewa akan tuqi ba sai wannan karin.
Bangaren Waheedah ya wuce yana shiga har dakin baccin su, wannan karin takalman shi ya cire bayan ya zauna kan gadon tukunna ya kwanta.
Pillow dinta ya dauka yana rikewa a jikin shi, kamshin turarukan ta ya shaka yana lumshe idanuwan shi.
Yakanyi kewarta duk idan yazo ya koma wajen aikin shi.
Bai taba tunanin zai kewarta yana gida ba, amman ya fara, cikin kasa da awa biyu komai ya birkice musu.
'Sadauki zaka karyani...'
Yaji muryarta cikin kanshi data saka shi bude kananun idanuwan shi, kafin ya sake mayarwa ya rufe su yana kara matse pillow din a jikin shi, sanyin shi na sake tunasar dashi cewa ba ita bace ba
"Ba zakimun haka ba, Waheedah ba zakimun haka ba..."
Ya furta a hankali yanajin an kwankwasa kofar dakin, wata irin dirowa yayi daga kan gadon
"Nasani, nasan ba zaki iya nisa dani ba...
Nasani"
Yake fadi yana karasawa ya bude kofar, Nuriyya yagani, a karo na farko da yaji baiso ta kasance a bakin kofar ba.
Rigarshi ce a jikinta sai wandon da ko cinyoyinta bai rufe ba.
Ta kama gashinta da yake a kwance ta kulle shi a tsakiyar kan nata.
Kwalliya ce a fuskarta sosai, da alama tayi wanka bayan fitar shi.
Sosai yake kallonta yana neman samun nutsuwa koya take daga hakan.
"Naji motar ka..."
Nuriyya ta fadi, tana jin zuciyarta tayo tsalle zuwa wuyanta da yanayin dake fuskar shi, zatai karya idan tace bataji tsoro ba daya bude kofar, saboda taga wani abu kamar disappointment shimfide kan fuskar shi, kamar ba ita ya tsammaci gani a tsaye a gaban shi ba, sosai hakan ya tsoratata.
Ganin ya kankance idanuwan shi yana kallonta har lokacin yasata fadin
"Ya jikin Waheedah din?"
Tanajin dacin dora sunan nata kan harshenta, wani irin tuquqin kishi na danne kirjinta da yanda zai kasance sunan Waheedah zatai amfani dashi yau dan tai nasara kanshi
"Da sauqi"
Ya furta can kasan makoshi, kai tadan jinjina tana shagwabe mishi fuska
"Abinci fa?"
Saida ta kira abinci tukunna yaji cikin shi ya murda mishi da yunwar da yakeji, numfashi ya sauke, duk ranar baici komai ba, Waheedah ko damuwa da cikin shi batayi ba.
Yanda baya jure yunwa idan yana tare da ita har mamaki yake bashi.
"Ki dafa koma menene"
Yai maganar yana shirin rufe kofar a fuskarta, kallon shi Nuriyya takeyi tanajin cikinta ya murda mata da yunwar da takeji itama.
Ba zatace ga rana daya datai wani girki kwakkwara ba tunda tazo gidan.
Da tace mishi
'Abinci fa?'
Batana nufin me zata dafa bane, tana nufin me zasuci ya fita ya siyo musu dan ita yunwa takeji ta fitar hankali, biscuit ne kawai a cikinta duk yinin ranar.
Saurin dafe kofar tayi
"Masoyi..."
Ta fadi tana tattaro duk wata kissa da zata iya ta nade muryarta da ita.
Numfashi Abdulkadir ya sauke, bacin ran da yakeji a kusa yake.
Da Waheedah ce data gane gab yake da fashewa, ko bata bashi space din da yake bukata ba zata kama hannun shi ta zaunar dashi, zata dora kanta a kafadarshi su zauna shiru har sai yadan nutsu.
Amman da alama Nuriyya bata karanci ranshi a bace yake ba.
"Naga yamma tayi, na dauka ma ka siyo mana..."
Tai maganar tana kallen shi fuskarta a shagwabe.
Numfashi ya sake saukewa yana dorawa da
"Idan ba zaki dafa ba ki barshi..."
Da mamaki a fuskarta take kallon Abdulkadir, bai taba mata magana cikin yanayin dayai mata ba yanzun
"Masoyi..."
Ta kira
"Kinjini ai"
Ya fadi yana rufe kofar a fuskarta ya koma kan gadon ya kwanta.
Wani bacin ran na sake danne shi.
Dan yasan ba laifinta bane ba, ba ita ta bata mishi rai ba, bai kuma kamata ace ya sauke akanta ba.
Yagani a fuskarta yanda hakan ya tabata, ba Waheedah bace ba, ita kadai ce a duniyar shi yake saukewa bacin ranshi ko da ba tada alaqa da hakan, saboda tabarshi, saboda ta nuna mishi bakomai dan yayi hakan, ta fahimta yana son saukewa a wani waje, dan ya zabeta bai dameta ba.
Karamin tsaki yaja.
Ko kadan bayason yawan tunane-tunane, Waheedah tasan hakan ta zabi ta sakashi cikin tunani.
Nuriyya ta kai mintina biyar a tsaye a bakin kofar, ranta idan yayi dubu a bace kowanne yake.
A rayuwarta batason wulakanci koya yake, idan akai matashi takanji kamar an mata hakanne dan a nuna mata ita din bakomai bace, amman tunda can idan wulakancin ya kasance daga bangaren shine takanji kamar zata hadiye zuciya ta mutu.
Yanzun ma haka takeji, kirjinta har zafi yake mata.
Batasan me akai mishi a waje ya bato mishi rai ba, dan ita tasan batai mishi komai ba.
Yunwar da takeji na karasa bacin ran ya hade mata, wucewa tayi ta koma bangarenta tana nufar kitchen.
Fridge ta bude tana rasa abinda zata dafa, akwai kaza a ciki danya.
Abdulkadir na kokari sosai wajen kula dasu tasani, kajine da yawa a nata fridge din, Waheedah kanzo har bangarenta ta kawo mata, bata cika amfani dasu bane shisa suka taru, randa taji kwadayi ya kamatane take daukowa ta soya.
Yanzun ma kulli daya ta fito da ita duk tayi kankara, ta rufe fridge din tana sakata cikin abin wanke-wanke ta bude fanfo.
Tukunya ta fito da ita tana ajiye, kazar da take a yayyanke ta kwashe ta zuba cikin tukunyar, ruwa ta zuba a ciki ta dora kan gas tana kunnawa.
Wajen fridge din ta karasa tana dubawa taga ko tana da cefane.
Gani tayi babu, tunda ba girkin takeyi ba, bata kula ba.
Fita tayi zuwa bangaren Waheedah ta shiga kitchen din nata tana bude fridge, akwai kayan miya a cikin robobi a ajiye wajen roba biyar.
Na farkon ta fara dauka ta wuce ta koma, diba tayi ta zuba cikin kazar, sosai take ganin ya mata yawa, dan robar nada girma,a fridge dinta ta saka dan ba mayarwa zatai ba, koda zata sake amfani dashi.
Maggi tazo ta bare ta watsa, taliya zatayi jalof.
Tana gama zuba maggin taji kiran sallar la'asar.
Daki ta koma tayi alwala, zani kawai ta daura saman kayan jikinta ta saka hijab ta gabatar da sallar.
Ko dardumar bata linke ba ta cire hijab din da zanin tana watsa su kan gado ta koma kitchen din, yunwa takeji ta fitar hankali, budewa tayi taga ya tafaso, amman wani karni ya daki hancinta dan kazar ko wankuwa batai ba, kuma kayan miyar babu albasar kirki a markaden su.
Dauka tayi ko dan bata karasa dahuwa bane ba, ludayi tasa taji ko kazar tadan yi laushi, rufewa tayi ta tsaya kamar minti biyar a kitchen din, har lokacin ranta a bace yake, tukunna ta bude daya daga cikin locker din dakin ta dauko taliya guda daya.
Kakkaryawa tayi ya zuba cikin tukunyar tana jujjuyawa tukunna ta koma falo ta zauna.
Gara ko kallo ne tayi ta rage zafi.
Tana kunnawa ta dauki remote suna dauke wutar su, wani dogon tsaki taja
"Tsinannu..."
Ta furta a fili tana mikewa.
Kitchen din ta koma taga tsaliyar harta fara laushi dan kanana ce, da tana gidan su takan jima bataci taliyar turawa ba, filawa Babansu yakan siyo a kado musu taliyar Hausa, ita ko lokacin sai tayi sati biyu bata dora tukunya ba, tun Mama na mata fada harta gaji ta hakura, idan ta matsa mata abincin ba za'a ga dai-dai ba, garama idan da mai da yaji ne, ko wake da shinkafa ce wani lokacin waken a tsai-tsaye za'aci shi.
Bai gama dahuwa ba, shisa ta daina sakata, tunda ba wadatar abincin suke dashi ba da za'a dinga barnar shi.
Taga alamar taliyar ta kusan dahuwa, amman sosai ruwan yayi yawa.
Abin kama tukunya da bangaren Waheedah ta dauko shi bata mayar mata ba ta saka tana dauke tukunyar daga kan gas din, rage ruwan tayi cikin abin wanke-wanke tukunna ta sake mayar da tukunyar kan gas.
Tunawa tayi bata zuba mai ba, shisa taga taliyar ta mata wani iri, dubawa tayi ta dauko man a cikin roba, da yake na 'ya'yan itatuwa ne suke amfani dashi.
Tana ma da man gyada da Waheedah ta bata yakai kwalba biyu, a cewarta kanwar babanta ce ta kawo mata da tazo gidan.
A ludayi ta tara man tana zuba ludayi biyu ta cakuda, gani tayi kamar bazai wadata ba, ta kara ludayi daya tukunna ta rufe tana mayarwa.
Jujjuya taliyar ta sakeyi, ta daddaga ludayin a hannunta ta dan-dana.
Gishiri ta dauko ta zazzaga dan taji kamar bai mata ba, hannunta ya kubce kuwa, cikin hanzari tai kokarin saka ludayi ta kwashe amman duk ya narke dan abincin nata tafasa, tsaki ta sake ja, komai baya tafar mata dai-dai.
Dabara ce tazo mata, ta dinga kwaso romon da ludayi tana zubawa cikin wajen wanke-wanke tukunna tadan dibi ruwa ta kara ciki, gani tayi cefanen naso yai mata kadan, ta zaro taliya daya ta saka a bakinta, duk da hakan gishirin nason mata yawa, kuma bataji cefane kamar yanda ta Waheedah kanyi ba.
Robar ta dauko ta kara dibar wani ta zuba ta cakuda, sai taga tadan mata kyau a ido.
Kamshine kawai baya tashi.
Faranti ta dauka tana zuba musu ita dashi a hade, kusan duka naman ta kwashe ta saka musu a ciki.
Dauka tayi zuwa falon ta ajiye ta koma ta dauko cokulla masu yatsu ta saka a ciki, tukunna ta taka zuwa bangaren Waheedah da batasan me yake acan din ba tunda bata nan, a falo ta same shi zaune.
"Ka taso muci abinci"
Ta fadi tana kallon shi harya mike ya taka ya wuce ta batare dayace komai ba.
Yunwa ke cin shi sosai da sosai.
Bayanshi Nuriyya tabi har falonta.