Sashe 53
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nuriyya na daya daga cikin su, ganin karshe da yai mata yana NDA ne, kuma daga lokacin sai labarin aurenta ya samu.
Bai sake sakata a idanuwan shi ba, tunaninta kuma bai sake fado mishi ba.
Sai yanzun, duk shekarun nan kusan, basu nuna a jikinta ba, tana nan yanda yasan ta, sai dai wata irin wayewa da ta shigeta, da sauri ya sauke idanuwan shi yana neman yafiyar Allah a cikin zuciyar shi na tsayawa da kare mata kallo da yayi.
"Hamma....
Ina kwana"
Ta fadi, muryarta na sauka kunnuwan shi da wani irin yanayi da bai taba tunani ba.
Idanuwan shi har lokacin suna kasa ya amsa ta
"Lafiya..."
A taqaice, kamar yanda yakanyi tun da can, ita kanta Nuriyya batayi tunanin ganin shi ba, watan aurenta shidda kenan da mutuwa, taje gidan Waheedah sosai a tsakanin, dan tunda ta gama iddarta take yawo sosai da sosai.
Ba zatai karya ba, ganin kwanciyar hankalin da Waheedah take ciki a duk lokacin da takan je gidanta yana tsaya mata a rai, shi yasa ma ta kusan wata daya yanzun bata taka gidan ba.
Yanda Waheedah ta samu duk wani abu da take mafarkin samu na tsaya mata.
Miji mai kudi, ga gidanta da ita kanta dinta, ga yaronta da takeji kamar ta sace saboda yanda yake mata kyau.
Duk da bai kai hasken fatar Waheedah din ba, yaron yafi su dukan su kyau.
Ko a wayar Waheedah ta so ganin AbdulKadir din, ta ga yanda ya koma.
Haka kawai ta tsinci kanta da son sani, amman bata samu damar hakan ba, Waheedah kuma ko da wasa batai mata zancen shi ba, bata ga fuskar da zata sakko mata da zancen ba ita kuma.
Dan sosai Waheedah ta canza, ba wai ita Nuriyyar ta canzawa ba, ita dince gabaki daya ta canza.
Dan duk wani sirrin aurenta da taso ji ta kasa, tana mata kyauta kamar da, su sha labarin duniya dai, amman hirar halin da aurenta yake ciki, ko wani sirrinta sam bata ji ko daya ba.
Abin kuma ya tsaya mata.
AbdulKadir din take kallo, ya kara girma, dan sai ta ganta yar karama a gaban shi, ya aske gashin kan shi kasa sosai, sai ta ga idanuwan shi kamar sun kara kankancewa, akwai tabbai kanana a fuskar shi, sai wani babban tabo da alamun dinkine daga gefen habarshi zuwa wuyan shi, zuwa wani waje cikin rigar shi da take son ganin iya inda tabon ya tsaya.
Shi kam bata ga alamar ya canza ba, dan yanda ya amsa mata gaisuwa, hakan yake amsa mata tunda can, a taqaice, cike da rashin kulawar da yake bata mata rai.
Gani tayi yana shirin wucewa, da sauri ta tsinci kanta da fadin
"Hamma..."
Juyowa AbdulKadir yayi yana kokarin kar su hada idanuwa, zuciyarta taji tana dokawa
"Aure na ya mutu, wata shidda da suka wuce, aurena ya mutu..."
Ta karashe, tana kallon yanda a hankali ya sauke idanuwan shi cikin nata.
Wannan karin kallonta yake, kallonta yakeyi da canjin da kalamanta suka haifar mishi, kallon ta yakeyi yanajin yanda babu shamakin igiyar auren da yake tunanin ta haramta mishi hakan.
Ba zaice ga abinda ya faru ba, yanajin wani hijabi da yake tsakanin su ya yaye, yanajin abinda yake tunanin ya binne a NDA na warwarewa.
"Me yasa?"
Ya bukata, cike da rashin fahimta Nuriyya tace
"Me yasa me?"
Saida AbdulKadir ya hadiye wani abu daya tsaya mishi a wuya, tukunna ya amsa ta
"Me yasa kika fadamun?"
Wannan karin tata zuciyar taji ta doka, ita kanta ba zata ce ga asalin dalilin da yasa ta fada mishi ba, kawai taji tana so yasani ne, bada tunanin komai ba.
"Ina so ka sani ne kawai"
Kai ya girgiza mata, ya rabata ya wuce yana jin yanda take bin shi da idanuwa, yana kuma jin yanda da duk takun da zaiyi da canjin da kalamanta sukai mishi.
Machine ya tare zuwa gidan Yassar din.
Har cikin gida ya shiga, ya samu Yassar ya fita shi da Fajr din, hakan yasa shi juyawa, ko zama baiyi ba, duk yanda Hauwa ta tabbatar mishi da cewar ba nisa Yassar din yayi ba.
Gida kawai yake son ya tafi, wajen Waheedah ko zai daina jin abin da yake ji.
BAYAN KWANA BIYU
Baccin da bata samu a kwanaki biyun da AbdulKadir yazo bane take ramawa, dan dakyar ta kai Fajr makaranta, bata tashi ba sai da azahar, masallaci ma suna raka'ar karshe, a daddafe tayo alwala ta gabatar da sallah, jin yanda jikinta yai nauyi har lokacin yasa ta sake watsa ruwa, atamfa ta saka, riga da zani tana daura dankwalin a kanta, ko mai bata shafa ba, tunda AbdulKadir din baya nan, bataga wahalar da kanta da zatayi ba.
Falo ta fito ta kunna kayan kallon ta ganin da wuta.
Tunanin AbdulKadir din zai iya kiranta kowanne lokaci yasa ta tashi ta dauko wayarta daga daki.
Text ta tura mishi
'Ya hanya?
Allah ya tsare ya saukeku lafiya'
Ta ajiye wayar, duk da kallon da takeyi bai hanata tunanin wanke-wanken da yake jiranta a kitchen ba.
Kwankwasa kofa taji anayi
"Shigo..."
Ta fadi, tana tuna cewar ta rufe kofar da mukulli, tashi tayi ta karasa ta bude, murmushi na kwace mata ganin Nuriyya.
"Sannu da rashin kirki"
Waheedah ta fadi tana mayar da kofar ta rufe, dariya Nuriyya tayi suna karasawa suka zauna.
"Ina ta so inzo Allah....
Ban samu lokaci bane ba"
Hararta Waheedah tayi
"Haka zaki ce daman, kingama sai kimun kitso, kan ya isheni wallahi"
Kai Nuriyya ta jinjina mata, suna gaisawa sosai, Nuriyyar ta dora da fadin
"Fajr ana makaranta?"
"Wallahi kam, tunda na kaishi na dawo na kwanta.
Babu abinda nayi a gidan nan.
Bari inyi wanke-wanke dai, me zakici?
Akwai shayi, ko in tafasa mana taliya tunda ina da miya"
Dan jim Nuriyya tayi kafin tace
"Taliyar dai, bama yunwa nakeji ba, ki gama aikin ki a nutse..."
Kitchen Waheedah ta wuce tana barin Nuriyya a falon.
Kwanciya tayi ta dauki remote tana canza tashar zuwa Arewa24, wani film din Hausa sukeyi 'Bakin alkalami'.
Shi ta nutsar da hankalinta tana kallo, kafin taji wayar Waheedah din na ihu kan kujerar, daga kitchen din Waheedah tace
"Nuriyya dan Allah taimaka mun da wayata, Sadauki ne ina jin..."
Mikewa Nuriyya tayi daga kujerar tana daukar wayar, aikam shi dinne, ga sunan nan a rubuce, haka kawai sai taji zuciyarta tana wata irin dokawa, lambar ta nutsar da hankalinta akai, komai na AbdulKadir daban ne, lambar kanta bamai wahala bace ba, hanyar kitchen din ta nufa da wayar, ta mikama Waheedah, da sauri ta dawo ta dauki tata wayar, gabanta ke wata irin faduwa lokacin da ta saka lambar AbdulKadir din a wayarta tana saving da 'Hamma AbdulKadir'.
Ta mayar da wayar cikin jakarta ta ajiye.
Ta koma ta kwanta, amman yanda gabanta yake faduwa yasa kwata-kwata ta daina fahimtar film din.
Ko da Waheedah ta fito daga kitchen din ma sai take ganin kamar zata gane abinda tayi, har wata zufa takeji ta daban, duk da fankar dakin, dakyar ta iya yiwa Waheedah kitson, sukaci abinci, tana yin sallar la'asar tace wucewa zatayi.
Tana kai Magriba ma wasu lokuttan, musamman in tazo Fajr na makaranta tunda wuni yake, hade makarantar tasu take da islamiyya.
Sai tace sai ta gan shi zata wuce, amman yau din ba'a nutse take ba.
Biscuit kala-kala da cake din da matar Yassar ta kawo mata lodi guda ta dibarwa Nuriyyan, ta bata dubu biyu, dan tasan zata kwana biyu bata dawo ba.
Yanayin kaddarar Nuriyyan na tsaya mata a rai, duk da bata tambayeta me ya faru ba, tasan da laifin Nuriyyar a mutuwar aurenta, amman Waheedah na cikin mutanen da basa yanke ma kowa hukunci batare da sanin asalin abinda ya faru ba.
Tana mata fatan alkhairi a ko da yaushe, dan har yanzun bata da wata kawar da tafita, sai dai yan uwanta.
Sukan kwana biyu basu hadu ba yanzun kuma, Amatu ma aure ya watsa ta Gombe.
Dukkan su aure yayi nisa dasu, sai wani abin ya faru akan hadu gabaki daya.
Sai dai waya ko da yaushe da sukanyi.
Anan falon tai zamanta, tana jiran lokacin dauko Fajr daga makaranta yayi taje ta taho dashi.
Wani indiyan film ta nutsu tana kallo.
LAGOS
Wanka yayi, ya kwanta, daga shi sai singlet da gajeran wando, ya ja bargo ya rufe jikin shi, saboda ruwan da akeyi, garin yayi sanyi, kuma yana jin kwiyar tashi ya kashe fanka, lokaci irin wannan yakanyi kewar Waheedah kamar ba jiya suka rabu ba, da tana nan zata kashe mishi fanka, har bargon ma ita zata rufa mishi, ko bacci yake zata lullube shi, yanda ake take gane yanajin sanyi na bashi mamaki, amman Waheedah ce, takan gane yana bukatar abubuwa da yawa a lokutta dashi kan shi bai gane yana bukatar ba.
Hoton shi ya dauka yana rufe da bargon ya tura mata a whatsapp, yana shiga tana hawa ta bude, itama nata ta turo mishi da Fajr dake bacci a kusa da ita, tana rubuto
"Muna ta kewarka"
Daga kasan hoton, hira sukeyi sosai, dan in yana hira da ita baya ma fita daga kan chat din ballantana ya duba ko wani ya mishi magana, Waheedah ma ta koya mishi chatting, kuma da ita kadai yakanyi hira mai tsayi.
Sai kannen shi in sun gaishe dashi yakan amsa, suma ba kullum ba.
Message na iya kwana biyu bai ko bude ba.
Badan yagaji da hira da Waheedah din ba, tunda kullum bata rasa labarin da zata bashi, yace mata ta kwanta, dan yasan zata tashi da sassafe ta shirya Fajr makaranta.
Sai da yaga ta sauka, tukunna, bai kai da kashe data din shi ba kiranta ya shigo.
Da murmushi ya daga ya kara wayar a kunnen shi
"Bakya jin magana ko?
Bance ki ajiye wayar ki kwanta ba"
Yanajin dariyarta ta dayan bangaren
"Zan ji muryarka ne fa, yanzun zan kwanta"
Har lokacin da murmushi a fuskar shi
"Ke kadai nake sawa abu, sai kinga dama Waheedah, in fada miki magana kiyi kamar bakijini ba..."
Dariyar ta sakeyi
"Yanzun zan kwanta Allah.
Sai da safe.
Allah ya tsare mana kai"
Amsawa yayi da
"Amin.