← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 94

Sashe 72

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kayan data shiga bandaki ta fito, hijab kawai ta dora a saman su, ta dauki jakarta tana zuba duka kudin data ciro na hidimar gida a ciki, ta saka wayarta da bata da wani amfani yanzun a wajenta ta dauki jakar, takalma ta karasa ta zira a kafafuwanta, batare data kula na wanka bane.

Lokaci zuwa lokaci take share kwallar dake bin fuskarta.

Maiduguri zataje neman shi, batasan ina yake a Maiduguri din ba, amman zaifi mata zaman da zatayi cikin gida batare da sanin halin da yake ciki ba.

Fita tayi daga gidan, tana tsaye tana kulle gidan da rashin nutsuwa yasa ta kasa saka mukullin a mazaunin shi harta rufe gidan, ga idanuwanta da suke cike taf da hawaye, a cikin kanta kawai ta kasa yarda tayi tunanin cewar wani abu ya sami AbdulKadir din.

"Wahee...."
Taji muryarshi cikin kanta, dan jim tayi na wasu dakika, kafin ta share wasu hawaye masu dumin gaske da suka zubo mata, jin muryarshi cikin kanta ba bakon abu bane ba, yau dinne tajita kurkusa sosai.

"Waheedah..."
Ta sake ji ya kira, juyawa tayi tana sauke idanuwanta akan AbdulKadir dayake tsaye, duka hannuwanta biyu ta saka wannan karin ta share hawayen fuskarta, tsaye yake cikin uniform harda hularsu ta sojoji, hana sallah a saman kan shi, hannun shi daya rike da jaka.

"Yanzun kuma gizo kake mun Sadauki?"
Ta furta wasu sababbin hawayen na sake zubo mata.

Kai AbdulKadir ya girgiza mata, yana jin da akwai sauran hawaye tattare dashi babu abinda zai hanasu zuba, ya riga ya fitar da rai da sake ganinta, tashin hankalin da ya gani a watannin bai dauka zai fito da ran shi ba, inya fito da ran nashi ma bai dauka batare da wata nakasa ba.

Duk da akwai tabbai na tsofin ciwuka da sababbin da ko warkewa basu gama yi ba, dan dinkine waje hudu a fuskar shi, akwai wasu guda uku cikin kan shi da hular da ya saka ta boye.

Sai jikin hannuwan shi da cikin shi.

Sai dai ganin Waheedah ya saka duk wani radadi da zugi da yakeji bace mishi.

"Waheedah"
Ya kira a karo na uku, yana kallon yanda ta ware mishi manyan idanuwanta cike taf da hawaye, kafin ta soma kokawa da numfashinta cikin yanayin da yasaka shi karasawa yana riko damtsen hannunta, amman har lokacin kokawa take da daidaiton numfashinta, da gaske AbdulKadir din ne a gabanta, ba gizo yake mata ba, jikinta ko ina bari yake, batasan ta yarda jakar da take hannunta ba, tana saka hannunta kan fuskar shi cike da son tabbatar ma kanta shine.

"Sadauki..."
Ta kira wani irin kuka me sauti na kwace mata, hannuwan shi AbdulKadir din ya zagaya yana riketa gam, batare da damuwa da yanda katon cikinta yake tokare shi yana hana mishi riketa yanda ya kamata.

Kuka take da yasa ko ina na jikinta bari.

"Babu abinda ya sameni Waheedah....

Gani...

Babu abinda ya sameni"
AbdulKadir yake fadi yana jijjigata, kukan da take yana taba zuciyarshi, sai da ya tabbatar jikinta ya daina bari tukunna ya dauki jakarta, har lokacin tana jikin shi, da dabara ya jasu yana bude kofar suka shiga cikin gidan, jakunkunan ya ajiye, yana kama hannun Waheedah da take sauke ajiyar zuciya ya zaunar da ita a kasa, yana kallon yanda sai da dabara ta samu ta zauna.

Ruwa yaje ya zubo a kofi ya kawo yana bata, da sauri ta karba ta shanye tas tana mika mishi kofin, ajiyewa yayi a gefe ya zauna.

Ko takalman kafarshi bai yunkurin cirewa ba, kanta Waheedah ta kwantar a jikin shi, ya kara matsawa yana riketa a jikin shi sosai.

Idanuwan shi ya lumshe yana jero duk wata addu'a ta godiya ga Allah daya dawo dashi gida lafiya, ya bashi damar rike matar shi a jikin shi haka.

Dayan hannun shi ya dago ya dora kan cikinta, saida ya sumbaci kanta tukunna yace
"Ya kuke?"
Hannu Waheedah takai ta share wasu hawayen da tambayar AbdulKadir din ta fito dasu, muryarta a dishe saboda kukan da tasha ta amsa shi da fadin
"Ka tsorata mu, Sadauki ka tsoratani"
Sumbatarta ya sakeyi yana riketa gam a jikin shi.

Cikin kuka tace
"Karka barni, dan Allah karka barni, bansan inda zan saka rayuwata ba, banma san ta inda zan farata babu kai a ciki ba"
Shiru yayi, baya yarda bakin shi ya bude da alkawarin da bashida ikon cikawa a tsakanin su, tunda rayuwar ba a hannun shi take ba, a lokacin cikin kan shi ya roki Allah ya bashi aron rayuwa mai tsayi a tare da ita.

"Ina zaki je da?"
Ya bukata cikin sanyin murya
"Maiduguri"
Waheedah ta amsa tana saka AbdulKadir din kallonta da murmushi a fuskar shi
"Bansan me zanyi bane ba...baka barni da zabi da yawa ba"
Kai AbdulKadir yake girgizawa, Waheedah da ko bindiga ya shigo da ita gidan inta sani sai dai bindigar ta kwana wani daki, su su kwana dakinsu daban.

Itace zata bishi Maiduguri
"Baki da hankali ko?

Ta ina zaki fara nemana?"
Kafadunta ta daga mishi, itama bata sani ba, binshi dinne abinda ya fara zuwa mata a kai
"Karki kara tunanin yin wannan kasadar"
Jin tayi shiru yasa AbdulKadir dagota daga jikin shi yana kallon cikin idanuwanta
"Da gaske nake Waheedah..."
AbdulKadir ya fadi yana dorawa da
"Bambanci kowacce rana na tare da yanda take kara kusantani dake"
Dan sanin cewa tana gida tana jiran shi ya ishe shi kwanciyar hankali
"Nutsuwar da take ragemun shine sanin kina lafiya, kina gida a kwance, kina lafiya, karki hargitsamun da tunanin ko kina shirin bina inda nake.

Kullum maganarki kar in barki...

Kin taba tunanin ke idan kika barni ya zanyi?"
Yanayin dake fuskar shi yasa idanuwanta sake cika da hawaye
"Babu inda zani, bazan barka ba, mutuwa ce kawai abinda zata saka in barka"
Ta tabbatar mishi tana saka shi jinjina mata kan shi kafin ya riketa a jikin shi.

Yanzun ma hannunta ya dago yana dorawa kan fuskar shi
"Kin ce babu inda zaki barni, me yasa kika bari na yarda da hakan bayan kinsan karya kike?"
Hannuwanta take zamewa daga cikin nashi, wannan karin bai hanata ba, wata irin gajiya yakeji har cikin zuciyar shi, numfashi ya sauke kirjin shi na wani irin ciwo.

Cikin sanyin murya yace
"Fajr fa?"
So takeyi ta amsa shi, yanayin shi takejin kamar zaiyi tasiri a kanta, shisa ta zabi yin shiru.

Dan ko kusa bata tunanin komawa gidan shi, tana jin shi ya mika hannu ya dauki Ikram dake bacci, rike yarinyar AbdulKadir yayi a jikin shi, ya nutsu yana kallon yanda take bacci batare da tunani ko damuwar wani abu ba, yanajin kamar suyi musayar matsayi da yarinyar, ya kai mintina biyar a zaune a wajen, kafin ya mayar da Ikram inda ya dauketa.

Numfashi yaja yana sake fitar dashi, kafin ya mike, Waheedah yake kallo da taki dago fuskarta ballantana su hada idanuwa.

"Sai da safe Wahee, kiyi hakuri nikam, bazan iya fadan nan ba wallahi, dan Allah kiyi hakuri.

Zan dawo gobe in shaa Allah, ki kula da ku"
AbdulKadir ya karasa maganar yana juyawa ya fice daga dakin yana nufar hanyar da zata fitar dashi zuwa harabar gidan.

Ko da ya shiga motar shi ya dade zaune a ciki, ya hade kan shi da abin tuqin yana rasa abinda ya kamata yayi, rayuwa bata taba gwada karfin halin shi ta irin wannan fannin ba, yanzun da hakan ya faru yake gane shi raggo ne na gaske, dan kam bayajin zai iya jurewa.

Tuqi yake a karo na farko ba tare da nutsuwa ba, yanajin mutane na zagin shi, bata su yake ba, gida kawai yake son karasawa batare daya kashe wani ko wani ya kashe shi ba, daya gan shi cikin gida ma bazai ce ga yanda ya karasa ba.

Mukullin a jiki yabar shi tunda ya shigo da motar, ya wuce cikin gida, kan shi tsaye ya nufi bagaren Waheedah, bedroom ya shiga ya kwanta yana lumshe idanuwan shi batare da yasan tunanin da yakeyi ba.

Yanda taga dare haka taga rana, da safe fuskarta a kumbure ta tashi da ita, saboda rashin bacci da kuma kukan da tasha.

Dadinta daya, a satin su Fajr sukai hutun makaranta saboda gabatowar azumi.

Ikram ta fara yima wanka ko da ta tashi, ta bata tasha da taga tayi bacci ta ajiyeta taje tai wanka itama.

Saida ta fita suka gaisa da su Hauwa da suketa sauri da alama sun makara, tukunna ta koma daki, kusa da Ikram ta kwanta jin idanuwanta har yaji suke mata saboda rashin bacci.

Ta lumshe idanuwanta taji Fajr a jikinta, hannu tasa tana dagashi
"Fajr ka kwanta a katifa....

Karka dameni dan Allah"
Kallonta yayi, da alama yanayin fuskarta yagani yasa shi zagayawa ta dayan bangaren ya hau gadon ya kwanta, juya kwanciya tayi ta fuskance su, tana kama hannun Ikram da kamar tajita, ta damqe dan yatsanta guda daya.

Murmushi Waheedah tayi zuciyarta na cika fam da kaunar yarinyar, kullum sai ta dauka babu yanda za ayi taso yaranta fiye da son da take musu, sai suyi wani abin da zaisa zuciyarta cika fam da wata irin kaunar su.

Bata san lokaci na tafiya ba, baccin kuma bai dauketa kamar yanda tayi tsammani ba.

Babu komai cikin kanta daya wuce su Fajr da take kallo sun nutsu suna bacci.

Kwankwasa kofar da taji anayi ne yasata lumshe idanuwanta dan a tunanin ta AbdulKadir ne, muryar Anty taji
"Waheedah..."
Da sauri ta diro daga kan gadon tana zuwa ta bude kofar.

"Anty..."
Ta fadi cikin sigar gaisuwa tana dan matsawa Antyn ta shiga cikin dakin, mayar da kofar Waheedah tayi ta rufe tukunna ta karasa gefen gadon kusa da Anty ta zauna suna gaisawa sosai.

"Ya jikin ki?"
Dan rausayar da kai gefe Waheedah tayi
"Alhamdulillah...

Naji sauki"
Kai Anty ta jinjina, tausayin Waheedah na cika zuciyarta.
Chapter 72 · 0% Book details