← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 94

Sashe 54

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ki kula da ku"
Tukunna ya kashe wayar, ya sauketa daga kunnen shi, yana duba lokaci, karfe sha daya har da rabi, saqo yagani a saman na Waheedah da shine karshe.

'Hamma...'
Dubawa yayi da mamakin ko waye, ba zai wuce Zahra ba, dan itace sarkin sake lamba, kullum cikin yarda waya take.

Budewa yayi yana ganin tana online, da sauri ya amsa
'Na'am..."
Fara typing yayi da shirin tambayarta ko lafiya?

In yaji lafiya ne sai ya sauke mata fada da tambayar abinda takeyi online da daren nan.

Hannuwan shi yaji sun daina rubutun a yake ganin sakon da ya shigo
'Nuriyya ce'
Daquna fuska yayi, sannan ya kankance idanuwan shi, badan baigane ta ba, sai dan mamakin dalilin da yasa take mishi magana da tsakiyar dare haka.

Tun randa yaganta tana manne da ranshi kamar yanda takanyi tun lokacin da take budurwa, lokacin farko da zuciyar shi ta fara doka mata, ba bakon yanayi bane a wajen shi, shisa bai dame shi ba balle ya hana shi hidindimun shi.

'Ok.'
Ya rubuta mata, yaja data din shi ya kashe, ya ajiye wayar a gefe ya gyara kwanciyar shi, addu'ar bacci yayi ya lumshe idanuwan shi, Nuriyya manne da zuciyar shi, ba sai me zaice mata ba shisa ya kashe data din shi, baima san ko yana so yai hira da ita din ba.

In ya riga ya gama waya da Waheedah baya son jin muryar kowa kuma, ko yin magana da wani.

Dan ko Yassar ya kira shi yakan daga da fadin
'Nafa yiwa Matata sallama Hamma, kana kirana kuma, na gama jin muryarta yanzun ina jin taka'
Yassar yakan amsa shi da
'Wallahi da bani da aure, kai zaka sa dole in fara nema, sai kace kai kadai ne me mata a duniya'
Dariya kawai AbdulKadir zaiyi, amman har ranshi bayaso kowa yai mishi magana in yayi sallama da Waheedah.

Baiqi ta zamo farko da karshen wadda zai wa magana a duk ranakun shi ba.

Da wannan tunanin a ran shi bacci mai nutsuwa ya dauke shi.

Wayarta take kallo, ta tsammaci ya tambayeta inda ta samu lambar shi, tun jiya ta kasa samun sukuni, so takeyi ta kirashi, amman ta kasa samun karfin gwiwar yin hakan.

Har ranta tana shakkar shi, kwarjinin da yake mata da, ganin shi da tayi ya ninku.

Batasan me take tsammanin zai faru ba.

Amman tana son mishi magana din, sai yanzun da ta kasa bacci, da tunanin shi fal ranta tukunna ta yanke hukuncin ta duba shi a whatsapp.

Hoton dake kan display picture din shi ya fara saka zuciyarta daukar wani irin zafi, hoton shine, sai hannun Waheedah da yake rike cikin nashi, yatsunsu lankwashe cikin na juna, AbdulKadir din ya dago hannuwan ya sumbata.

Wani irin abu takeji, inda tana da karfin ikon sake hoton, ta cire hannun Waheedah ta saka nata a ciki, zatayi hakan, tun ranar farko da taje gidan Waheedah takejin son samun abinda duk take dashi.

Dp din AbdulKadir ya saka shi cikin lissafin abinda take son samu iri daya da Waheedah.

'Ok'
Din shi take ta kallo ta kasa yarda da cewar baima damu da ita din bace, balle harya tambayi inda ta samu lambarshi.

"Zan sa ka damu dani Hamma AbdulKadir...

Wallahi nafi karfin wulakancin ka..."
Ta fadi a fili, kalaman na zauna mata, tanajin yanda take a shirye da tayi komai indai zata same shi, kwanciyar hankalin da Waheedah take ciki, shigar alfarmar da takeyi da komai nata, take son samun irin shi.

Kwanciya tayi tana lumshe idanuwanta, muryar Anas na dawo mata
'Saki kike so ko Nuriyya?

Tunda na aureki hankalina bai kwanta ba, ke kanki baki bari naki ya kwanta ba, balle kibari nawa ya kwanta, saboda kina hangen abin duniya.

Ba baki na miki ba, amman wallahi ba zaki taba samun kwanciyar hankali ba, alhakina bazai barki samun wannan nutsuwar ba.

Bawai zan sakeki dan kin isa bane, zan sakeki saboda ina bukatar samun kwanciyar hankali...'
Tashi zaune tayi tana girgiza kanta cike da son batar da tunanin Anas daga ranta, karya yake yace alhakin shi zai kamata.

Ta yarda farkon auren su ta bashi wahala, bala'in yau daban na gobe da ban, inda take so tafiya take ko ya barta ko bai barta ba, abinci kuwa sai dai inya dawo ya dafa, har gyaran gidan shi yakeyi.

Amman ta karfi da yaji Anas ya karbi mutuncinta, a cewar shi abin nata bana kare bane ba.

Daga lokacin kuma tashin hankalinta ya fara itama, dan Anas daina raga mata yayi, saiya daina kawo abinci, duk idan ta fita batare daya barta ba, saita kwana ta yini da bakar yunwa, komin zagin da zatai mishi.

Hakkin shi inya tashi karba baya tausaya mata, karfi yake nuna mata.

A haka ta samu shigar cikin farko, a shekarar auren su, lokacin ya fara nuna mata wani irin gata da soyayya, kome tace tana so sai yai mata, amman ba wannan bane a gabanta, da rana daya bata tabajin soyayyar Anas ba, kullum tsanar shi kuma gaba takeyi a zuciyarta.

Kudin da ta dinga karba a wajen shi sanadin cikin, da su tayi amfani aka cire mata shi.

Dan ba zata hada jini da Anas ba, balle yara su sakata zama dashi.

Idan ance mata zata shekara hudu da Anas zata karyata, ko shekara bata hango ba, ciki biyar ta zubar a gidan shi, na karshen ne yagane, kuma shine yai sanadin sakin da yai mata.

Har gida yazo ya samu Baba ya bashi hakuri, ya kuma yi mishi bayanin duk abinda ya faru.

Taga tashin hankalin da bata taba tunani ba, dan Baba ca yai saita koma ko ya tsine mata, kafin yaji saki Uku Anas din yai mata.

Ko kadan Baba baiji dadin zancen ba, hausawa kan ce ka haifi yaro baka haifi halin shi ba.

Haka Nuriyya ta zame mishi.

Badan yana duba abubuwa da yawa da korar Nuriyya daga gidan zai haifar mata da shi ba, da babu dalilin da zaisa taci gaba da zamar mishi a gida.

Amman duniya ta nuna mishi ta zaba fiye da darajtasu da mijin aurenta, idanuwa su Baba ya dauka ya saka ma Nuriyya, yabarta da duniyar da yake da tabbaci zata gyara mata zama.

Mama daman ba darajar kirki take dashi a idanuwan Nuriyyar ba tun da can, balle yanzun da take ganinta dai-dai da kowa.

Ganin babu mai mata fada yasa take duk abinda taga dama.

Kullum yawon gidajen kawayenta tun na FCE da yawancin su yan duniya ne na asali.

Maza kuwa kala-kala take tarawa a kofar gidan su.

Yanzun ne takejin lokaci yayi da zata tsayar da hankalinta kan kudirinta.

Dan duk a cikin masu zuwa mata da maganar aure bayan ta kare iddarta, talakawa ne, masu kudin da maganar banza sukan zo mata.

Ita kuwa duk fitsararta bata kai nan ba, aure take son yi, soyayya bata gabanta, inda zata huta tayi abinda take so ne muradinta.

Ta kuma hango hakan akan AbdulKadir.

Komawa tayi ta kwanta, ta dauki wayar, duk da zuciyarta da take dokawa bai hanata tura mishi text ba
'Naga ka sauka, har kayi bacci?

Sai da safe Hamma.

Allah ya tsare mana kai'
Ta saka wayar a caji ko da zasu kawo wuta cikin dare tukunna ta kwanta.

Juye-juye take, bacci ya kaurace mata, tunani ne a ranta kala-kala...!
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
#LubnaSufyan
[7/27, 1:14 PM] +234 816 124 4732: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
A watanni uku babu dabarar da take tunanin tana da ita da zatayi aiki akan AbdulKadir.

Ga wata irin soyayyar shi da takeji kamar ana hura mata wuta.

Inda ance ita Nuriyya zata ajiye yanda take ji da kanta ta dauki duniya ta fadama da namiji tana son shi zata karyata.

Amman sai gata, ba sau daya ba, ba sau biyu ba, harta bace kirgan lokuttan da ta furta ma AbdulKadir din kalmar so.

A rana tana iya tura mai sakonnin text fiye da goma, tana tambayar lafiyar shi, ko yaci abinci, da sauran duk wani abu da take tunanin inta tambaye shi zai amsata.

Sai dai tun kafin ma tace mishi tana son shi din, tana iya tura mishi sakonni hamsin a whatsapp ya bude ya karanta yai banza ya kyaleta.

Sakonnin ma da alama suna zuwa, amsa ce kawai bata samu, tana iya kiran shi sau goma a jere bai daga ba.

Yanzun kuma ta tsagaita mishi da kiran wayar, tunda ya daga ya balbaleta da fadin
'Ko matata sau biyu take kirana.

Karki sake mun kiran yara Nuriyya.

Bakisan bana so a dameni ba ko?

Me yasa zaki dameni?

Ranki zai mugun baci kika sake mun kiran yara.

Idan ina son magana dake, kiran farko zan daga, idan bana kusa na zo nagani zan kiraki...'
Ko amsarta bai jira ba ya kashe wayar.

Kwana tayi tana kuka daren ranar.

Komai sai da taji baya mata dadi.

Tayi dana sanin sanayyar dake tsakaninta da Waheedah, sanayyar da tasa take kishinta, take son mallakar duk wani abu da take dashi, sanayyar da ta jefata cikin son mallakar AbdulKadir har yake mata wannan wulakancin.

A tsayin watannin kwata-kwata bata taka kafarta gidan Waheedah din ba, sai dai su gaisa a waya, ko ta whatsapp wasu lokuttan, haka tace mata tana gidan kawunta dake Bebeji, taje tadan huta.

A watannin ko fita batayi, tana gida kullum, samarin ma sun fita daga ranta, tana dan daga kiransu ne wasu lokuttan saboda ta samu katin waya.

Waheedah kuma kan turo mata na dubu daya da dari biyar duk wata, ta siyi data.

Duk da tana jin lokaci zai zo da ba zata bukaci wannan taimakon daga wajen Waheedah din ba.

Ta dai samu AbdulKadir din, satin daya gabata, har gayawa kanta tayi ta hakura dashi, tagaji da wulakancin da take kwasa, amman da safe saita tsinci kanta da tura mishi sako ta gaishe dashi.

Yau ma kamar ko da yaushe, yana online wajen karfe goma da rabi, dan ya saka hoton Fajr a status din shi, har ta bude ma tayi mishi magana
'Fajr fa yafi ku kyau'
Ko budewa baiyi ba.

Wani radadi kirjinta yake dan tasan da Waheedah yake chatting, zuwa yanzun wani irin kishi take da ita naban mamaki.
Chapter 54 · 0% Book details