Sashe 31
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Farar hodar da take shafawa ta dauka ta zazzaga a jikin soson hodar Amatullah dan ba zata tuna ko tana da soson hoda ko bata dashi bama.
Murzawa tayi a fuskarta ta ajiye tana sake dubawa.
Kayan kwalliyar da banda farar hodar da wasu cikin turarukan dukan su sauran na Amatullah ne take dubawa.
Rasa wani abu da zata dauka tayi amfani dashi tai.
Ko a gida zata zauna bata tunanin zatayi wata kwalliya fiye da wadda take fuskarta, ballantana fita zasuyi, su dukan su suke zuwa masallacin idi a gabatar da sunnar da take cikin zuwa sallar idi.
Fuskar mace kan shiga cikin al'aura, wato abinda ya kamata ya zama a rufe duk lokacin da ta tsara mata kwalliya, sharadin saka niqab ya fada akanta koda batada kyawun dazai karya alwalar maza.
Tana yawan tunasar da Amatullah da Nuriyya, amman biris suke da ita, wasu lokuttan ma Nuriyya kan ce mata ita ta cika tsawwala lamurran addini.
Sai dai tasan zunuban da yawancin mutane kan dauka kanana, sune suke taruwa a hankali har suyi girman da mutum bazai iya dauka ba. kwalli ta hango ta dauka ta sakama idonta, tana ganin yanda fuskarta ta sake fitowa.
Da gaskiyar Mami, kwalli na mata kyau.
Mikewa tayi ta dauki turare ta tuna fita zatayi, ta mayar ta ajiye.
Hijab dinta da take a linke ta dauka ta warware tana sakawa a jikinta.
Doguwa ce har kasa, sai dai babu hannu a jiki, tana kuma sane ta dauko dan kunshin da yake hannuwanta.
Kafafunta ma safa ta saka musu, batai kunshi dan mazan da ba muharramanta ba, tayine dan kwalliya.
Dogayen takalmanta da suke ajiye ta saka.
Amatullah kan mata tsiya cewar tana saka dogayen takalma ne dan bata da nauyin da zata dinga gurdewa.
Dariya kawai Waheedah kan yi, ta riga ta sabane da dogayen takalman tun yarinta, gashi kuma hijabanta wani lokaci suna dan jan kasa, idan ta saka dogayen takalman sai taga sunfi kyau.
Bata ga Mami a gidan ba, har dakinta ta leqa bayan ta fito, tana da tabbacin suna bangaren Hajja danyin hidimar bikin sallar da suke haduwa su duka hudun suyi.
Dan haka ta fice daga gidan itama, yau dai ta shirya da wuri, badan gugar da taima Yazid bama da tuni ta jima da shiryawa.
Babu mai mata mita ta cika sanyin jiki.
Takawa tayi har inda ake ajiye motocin gidan tana samun guda daya ta tsaya a jikinta, saitin da zata iya hango bangaren su Abdulkadir, dan shi take so tagani tunda ta tashi.
Tafi minti biyar a tsaye kafin ta hango shi ya fito, jikin shi sanye da farin yadi da hula rike a hannun shi cikin yanayin da yasa bugun zuciyarta karuwa.
Dago kai taga yayi yana tsayar dashi akanta.
Bata hango idanuwan shi daga inda take, murmushi ya kwace mata.
Sosai take murmushi da yanda mazaunin idon AbdulKadir din kawai take iya hangowa daga inda yake.
Hakan yasata sauke kallonta daga kan shi, zata rantse idanuwanta kawai ta sauke tana kallon takalmanta, ta sake dago su taga Abdulkadir din tsaye a gabanta yana kankance mata idanuwan shi, zuciyarta taji cikin makoshinta inda tai tsaye tana ci gaba da dokawa.
"Murmushin me kike?"
Ya tambaya yana tsare ta da idanuwa, dan shi baiga abin nishadi a safiyar ranar ba, kan shi ciwo yake.
Gashi komai baya mishi dadi, kai ta girgiza mishi tana saka shi fadin
"Taqabbal Allaahu minna wa minkum"
Ya dora da
"Ba'aimun dinkin sallah ba"
Cikin yanayin da ya saka wani murmushin kwace mata, dan yanda yai maganar kamar karamin yaron da akaima gagarumin laifi ya sakata jin tamkar tana kan lilo.
Komai nashi ya mata, komai a tattare dashi.
Amsa gaisuwar sallar da yai mata tayi a hankali har lokacin tana murmushi
"Ba abin murmushi bane ba, kayan Hamma Yassar na saka, basumin dinkin sallah ba, kowa an mishi banda ni"
Abdulkadir din ya fadi yana rasa dalilin da yasa yake gaya mata.
Kawai ya tsinci kanshi da son gaya mata ba'ai mishi dinkin sallar ba, yana kuma jin son gaya mata duniyar ma bata mishi dadi, baisan ta inda zai fara ba.
Idan tana kusa dashi yakan tsinci kanshi dayin abubuwan da baisan dalilinsu ba.
Abu daya yake gani a fuskarta, zai iya yin komai a gabanta, ba zata taba raina shi ba, bai taba ganin hakan a fuskar kowa ba sai tata, ko Yassar bakomai yake iyayi a gaban shi ba, a hakan ma ya raina shi dan yana ganin ya bashi wasu yan shekaru, shisa yake kokarin ganin ya kama girmanshi a gaban Yassar din.
Dayan hannun shi ya dago ya bude mata shi, links ne a cikin tafin hannun nashi.
Hakan yasata tattaro hijab din jikinta ta fito da hannayenta da Abdulkadir din yabi da kallo, zuciyarshi na fada mishi bai taba ganin hannuwa masu kyau irinsu ba.
Links din ta saka hannu ta dauka, Abdulkadir na rike hannun nata
"Kunshi kikayi"
Maganar ta fito daga kasan makoshin shi lokacin da ya dago dayan hannun shi yana kamo dayan hannun nata dashi hadi da duba kunshin nata da yakejin na kwance wasu kusoshi cikin kanshi.
Wani irin yanayi yake ji da bazai fadu ba.
Motsi yaji a bayan shi, amman bai juya ba, asalima bayason ya dauke idanuwan shi daga hannuwan Waheedah din, a karo na farko da ko kadan tunanin hasken fatarta baizo mishi ba, baya ganin komai sai jan lallen dayai wata irin fitowa a hannunta.
Tun daga nesa Yazid ya hango su, yana jin zuciyar shi kamar zata fito waje, dan zazzabi ne a jikin shi ruf, dakyar ya iya fitowar ma, baisan kafafuwan shi sun motsa ba lokacin dayaga Abdulkadir din ya rike hannun Waheedah sai da yagan shi tsaye a bayan shi, amman daga Waheedah din har Abdulkadir sunyi kamar basu san yana wajen ba.
Musamman Waheedah da yake ganin tsayuwar duniyarta akan Abdulkadir din ta cikin idanuwanta, tana saka shi tuna duka lokuttan da yake ganin hakan a idanuwanta idan Abdulkadir na wajen, yana sakashi tunanin kalar sakarcin shi wajen kasa fahimtar abinda yake faruwa a tsakaninta da AbdulKadir din, dan yana tunanin tayi yarinta ta fahimci wani So ballantana harta fada cikin shi.
"Waheedah..."
Yazid din ya kira yana saka zame hannuwanta daga cikin na Abdulkadir tadan kalli bayan shi inda Yazid yake tsaye
"Hamma..."
Ta fadi tana saka Abdulkadir din juyawa ya kalli Yazid din shima
"Taqabbal Allaahu minna wa minkum"
Abdulkadir ya fadi yana mikama Yazid din hannu, karba yayi ya amsa yana kuma yi musu murnar sallah a bisa tsarin addinin musulunci tukunna ya zagaya ta bayan motar ya tsaya, dan kirjinshi yake ji kamar zai bude.
Juyawa Abdulkadir yayi yana mikama Waheedah hannuwan shi.
Dai-dai lokacin da Yazid din ya juyo yana kallon su, links din Waheedah ta daura mishi, idanuwan shi nakan hannayenta da yake jin kamar ya yanke ya koma Kaduna dasu, ya manna a jikin bangon dakin shi, duk lokacin dayai ra'ayi ya juya ya kalla.
Hakan dayai tunani ya saka shi laluba aljihun shi ya zaro wayarshi daga ciki.
Waheedah na kallon shi, zuciyarta kamar zata fito waje.
Tana kuma kallon shi yana danna wayar, kafin ya kamo hannunta yana mikar dashi, ya kuma kamo dayan ya dora a kan dayan cikin yanayin yanda yake son yagan su, ita kam a gabanshi takan koma kamar yar tsana mai batir da remote, remote din kuma yana hannun Abdulkadir, yanda duk yake so tayi hakan yake juyata.
Idanuwanta tsaye yake kan fuskar shi, tana jin yanda yake rike da yan yatsunta, kafin ya saki yana duba wayarshi hadi da dan daga mata kai cikin yanayin da yasata sauke hannuwanta tana murza su cikin hijab, har lokacin tana jin nashi hannuwan manne a jiki.
Kanshi Abdulkadir yadan dafe daga gefe yana runtsa idanuwa, tukunna ya bude su akan Waheedah yana fadin
"Kaina na ciwo..."
Bata ce mishi komai ba yaga ta juya da sauri, yana bin takalman kafarta da kallo, ko tunanin ta fadi cikin dogayen takalman nan batayi.
Yana kuma kula da yanda kusan duka takalmanta dogayene.
Bayan shi ya jingina da motar yana duba hoton hannuwanta a cikin wayar tashi, blackberry badai camera ba, sosai hoton ya dauku, shiya mayar kan wallpaper din shi daman hoton wani lallen ne, wannan dai yafi mishi kyau.
Baisan lokacin da yasa hannu ya shafi screen din wayar ba, yana karama Yazid zazzabin da yake ji.
Dan yana kallon duk abinda yake faruwa, bai daisan haka zai mishi zafi na gaske ba.
"Abdulkadir..."
Ya kira a hankali yana saka Abdulkadir din juyawa ta bangaren da yake ya kalle shi
"Karka sake rike Waheedah, akwai haramci a hakan, kasani ba saina fada maka ba, ba muharramarka bace ba"
Dakuna fuska Abdulkadir din yayi
"Kunshi tayi Hamma..."
Ya fadi kamar hakan zai zama dalilin da zaisa ya rike hannuwanta
"Na dai fada maka, ranka zai mugun baci idan na sake gani"
Yazid ya fadi cikin yanayin da AbdulKadir din bai taba gani a tare dashi ba.
Hakan yasaka shi daga kai a hankali kawai tukunna ya juya yana hada bayanshi da motar wajen.
Ranshi bai baci ba yau, bashida wannan wajen, kunshin Waheedah ya dauke mishi wannan yau kam, bashida lokacin fada da Yazid din, duk da ya tsoma mishi baki cikin lamurran da baiga ta inda ya shafe shi ba.
Waheedah ce ta dawo da robar ruwa a hannunta, dayan hannun a dumtse, tana sake goge mishi komai da yake cikin kan shi.
Robar ruwan ta mika mishi, ya karba, idanuwan shi kafe kan hannuwanta, dan yaji suna danna mishi tunanin Nuriyya inda yake son boye shi dan karya sake dawo mishi.
Dayan hannun Waheedah ta ware mishi yana ganin Panadol guda biyu, kai yake girgiza mata, a duniya babu abinda ya tsana irin magani, ko rashin lafiya yake bayasha.
Yassar ya taba tura mishi cikin ayaba yana ce mishi ko itace yaci zaiji karfin jikin shi, kawai yana gutsura ya tauna magani a ciki, kuma ya tsare shi da saiya hadiye, har amai yayi.
"Bazan sha wani panadol ba"
Ya fadi yana kankance mata idanuwa.