Sashe 28
Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ba yanzun naso zuwa ba"
Cike da rashin fahimta Waheedah take kallon shi, idanuwan shi daya sauke cikin nata na saka wani abu tsirga mata har tsakiyar kanta
"Hamma..."
Ta furta muryarta can kasan makoshi, kai Abdulkadir ya dan daga mata, da gaske yake har zuciyarshi, baiyi niyyar zuwa gida ba sam, saboda tunda ya tafi Nuriyya na manne a wani waje tare dashi, duk kokarin dayai na ganin ya cirota daga duk inda take maqale dashi ya kasa.
Bakon abune a gurin shi, tun tasowar shi abinda duk yasa ranshi sai yayi shi yakeyi, ko da su Hajja zasu karya shine kuwa.
Shisa kasa cire Nuriyyan yake bata mishi rai.
Suna shawowa kwanar gida shi da Yassar da yaje ya dauko shi komai na sake danne shi.
Saima daya fito daga mota yana sauke idanuwan shi kofar gidansu, da zuciyarshi a makoshi saboda dokawar da take ya shiga gida.
Har yanzu kuma ranshi a bace yake jin shi, saboda bayason fara tunanin abinda mannewar da Nuriyya tai mishi yake nufi, sam bayaso, babu abinda hakan zai haifar mishi banda raini.
Yana ganin yanda waje kadan Nuriyya take jira ta samu ta raina shi, ba sai an fada mishi ba, a yanayinta da fuskarta ya karanci akwai wannan halayyar a tare da ita.
Shikam a duniya raini ne babban abinda bayaso, ko wanda suke da tazarar shekaru a tsakanin su bayaso su raina shi, shisa yake bala'in rike girman shi.
Watan shi biyu da komawa Kaduna yaji yanda kwata-kwata bayason komawa Kano.
Koda zai koma din banan kusa ba, a qalla ya kara daukar wasu shekara biyun tukunna, wataqila hoton Nuriyya ya disashe mishi daga cikin kai.
Amman duk idan ya kwanta ya rufe idanuwanshi baya ganin komai sai fuskar Waheedah da alkawarin da yai mata na cewar zai zo hutun sallah.
'Da gaske zaka zo?
Dan Allah kazo Hamma, kaji...
Kazo dan Allah'
Shine abinda yake mishi yawo duk lokacin dayai tunanin kin zuwa hutun sallar, ran shi a bace yake, baisan wazai dorama ba, shisa ya zabi ya raba bacin ran da ita, tunda itace dalilin sakashi dauko kafafuwan shi daga Kaduna zuwa Kano.
"Ke kika sa nazo...alkawarin danai miki yasa ni zuwa.
Jibi zan koma"
Yai maganar, kallon da yake mata nasaka tajin wani radadi a kirjinta da ba zatace ga daga inda yake fito ba.
Kallon ta yake yana dora mata laifin zuwan dayayi, duk da hakan bai hana zuciyarta jin dadin zuwan nashi ba, koba komai tagan shi.
Amman ita bata ce yai mata alkawarin zaizo ba, batasan me yasa yake kallonta ba.
"Ki bani abinci nikam"
Abdulkadir yace yana dauke idanuwan shi daga kanta, bayason ganin yanda take kallon shi kamar tana son sanin dalilin dayasa yake dora laifin zuwan shi akanta.
Bayan ita ce dalilin da yasa shi zuwan tun daga farko, da bata kalle shi da idanuwanta din nan ba, da bata kalle shi da farar fuskarta tasa shi alkawarin da yake dana sani ba, babu abinda zai kawo shi Kano.
Sai dai bacin ran da yake ciki bashi da alaqa da abinci.
Bai taba fushi da abincin ba, cikin shi daban, abinda yake faruwa dashi daban.
Plate Waheedah ta dauko ta dauraye, gabaki daya wake da shinkafar ta juye mishi, tana kallon shi ya dauko cokali kafin ta gama zubawa.
Mika mishi plate din tayi ya karba, yana shirin juyawa tayi saurin fadin
"Hamma..."
Sai dai sauran kalaman sun maqale mata, batama san me take shirin ce mishi ba, gashi ya kafeta da kananun idanuwan shi da suke rikita mata lissafi, kanta ta sauke kasa tana kallon kafafuwanta.
Yakai mintina biyu a tsaye, ganin batada shirin magana yasa shi juyawa.
Mami daya gani a falon zaune ya kalla da fadin
"Sannu da shan ruwa"
Da fara'a ta amsa shi tana dorawa da
"Abdulkadir.
Saukar yaushe?"
Duk yanda yaso yayi murmushi ya kasa, ranshi a bace yake har lokacin, a gajiye yace
"Dazun..."
Kai Mami ta jinjina sanin halin Abdulkadir, wucewa yai abin shi, har ya kusa kofa yaji Yazid na tambayar
"Yaushe kuka karaso?"
Juyowa yayi yana kankance ido yace
"Meka sa a kunnen ka?"
Kai Yazid din ya girgiza mishi
"Bansa komai ba"
Ya amsa cike da rashin fahimtar tambayar Abdulkadir din
"Me yasa kake tambayata abinda na amsa yanzun to?
Salon in magana kace na maka rashin kunya?"
Murmushi Mami tayi tana mishi addu'ar shiriya a ranta kafin ta mike tabar wajen.
Ba za'ayi koma menene a gabanta ba.
Hannuwa Yazid ya daga cikin nuna alamun saduda
"Allah ya baka hakuri..."
Juyawa Abdulkadir din yayi da shirin ficewa daga dakin, yaga Nabila tsaye a bakin kofa, taga alamar ranshi a bace yake, shisa tai tsaye dan kar ya sauke tambotsan akanta
"Ubanki kike a bakin kofa?"
Ya tambaya yana watsa mata harara, juyawa tayi da niyyar komawa inda ta fito, wani dogon tsaki Abdulkadir din yaja ya fice daga dakin yana nufar bangaren su.
Nuriyya na manne dashi ya rasa yanda zai ya cirota, haushin kowa yake ji, komai yaci karo dashi qara bata mishi rai yake.
Kofar dakinsu yagani adan bude, dubawa yayi yaga takalmine ya tokareta.
Tsugunnawa yayi, plate dinshi a hannu daya, yasa dayan hannun ya dauko takalmin yana juyawa yai cilli dashi, kiris ya make Yasir da yake tahowa
"Anzo an ajiye wani banzan takalmi salon sauro ya cika mana daki"
Yake fadi shi kadai yana sauke numfashi.
Karasowa Yasir yayi yana kallon ikon Allah
"Kai kuma kaida wa?
Kake ta huci kamar kububuwa"
Batare da Abdulkadir ya juyo ba yace
"Ban sani ba..."
Ya wuce yana shigewa cikin dakin.
Yasir baisan meyasa yanayin Abdulkadir din ya bashi dariya ba, dariya yake sosai a bakin kofar daya kasa karasa shiga ma.
Har cikin ranshi Abdulkadir yake jin dariyar Yasir din, kofar dakinshi ya tura yana shiga hadi da rufeta da karfin gaske.
Idan harya koma yaima Yasir magana fada zasuyi, yanda yake jin ranshi a bace, kan wanda zai huce yake nema.
Abincin yacinye tas yasha ruwa, ganin idan ya zauna tunanin da baya buqata zai danne shi, fitowa yai ya tafi masallaci abinshi.
Kirjinta take ji kamar an dora dutse, tana isha'i ta wuce daki ta kwanta abinta, daya daga cikin hoton Abdulkadir din da yake cikin qaramin pillow dinta ta saka hannu ta zaro tana dubawa, shigowar Amatullah dakin yasata saurin mayar da hoton inda ta dauko shi.
Waje Amatullah ta samu gefen gadon ta zauna tana ajiye robar dake hannunta a kasa tana fadin
"Hajiya Adda ai saikin sauko kasa ko?"
Cikin rashin fahimta Waheedah tace
"In sauko kasa in miki me?"
e idanuwa Amatullah tayi
"Lallai Adda Wahee...
Kunshin fa"
Numfashi Waheedah ta sauke, sam ta manta da wani maganar kunshi, kitso daman Nuriyya tai mata, guda goma tace ma.
Nuriyya bata saurareta ba tayi mata qanana duk da kan bawani gashin kirki yake dashi ba.
Ba zata iya bin layin wani baqin qunshi ba, amman Amatullah ta iya jan lalle kala-kala, duka yan gidan ita tai musu.
"Ni na manta da wani kunshi.
Dakin barni Amatu, jikina ciwo yake mun"
Tunda ta fara magana Amatullah ke girgiza mata kai
"Wallahi baki isa ba Adda, tunda ba takaba kike ba.
Lallena dana kwaba fa?
Waye zai amfani dashi.
Bama zai yiwu bane ba, har Mami tayi jan lalle....ni wallahi da ina da farin ki da anga lalle"
Yar dariya Waheedah tayi, Amatullah din ba baqa bace, amman kuma ba zaka kirata fara ba, tana da hasken fata irin na yawancin yaran gidan Bugaje din.
"Kifa sauko..."
A kasalance Waheedah din ta sauko daga kan gadon.
Tasan halin Amatullah idan ba'ayi kunshin ba fushi zata dauka da ita.
Tsegumi kam sai kanta ya fara juyawa, gara tayi ta huta.
Hira suke tabawa ita da Amatullah din har ta gama saka mata lallen a duka kafafuwa da hannuwanta, ita ta taimaka mata tahau kan gado ta kwanta, gabaki daya duniyar take ji ta tattaru a hannuwanta da kafafuwanta da suke a daure da ledoji.
Ita kam bataga komai a cikin kunshi banda wahala ba.
Batajin zata iya bacci da wannan ledojin a jikinta, da wannan tunanin bacci ya dauketa cike da mafarkin Abdulkadir.
Washegari kasancewar safiyar sallah, yanayin garin kanshi yayi sanyin da safiyar sallah ce kadai kan haifar.
Tunda suka tashi suke hidimar su, Waheedah bata ga kunshin taba sosai saida gari ya fara wayewa tunda babu wutar lantarki.
Kyau yai mata sosai, gashi ya kama har wani ruwan kasa-kasa mai cizawa yake.
Da gudu ta taho tana rungume Amatullah da take tsaye ta baya
"Kinsan ina son ki ba?"
Ta fadi, Amatullah din na tureta
"Soyayya da sokamun kasusuwa?"
Dariya Waheedah tayi tana sake komawa ta riqe Amatullah din dake kiciniyar kwacewa gam
"Adda Wahee mana"
Amatullah ta fadi tana samu ta ture Waheedah din, da murmushi a fuskarta, Mami ce ta fito ta gansu
"Mami kalli kunshina"
Cewar Waheedah tana daga ma Mami hannuwanta, jinjina kai Mami tayi
"Ma shaa Allah.
Yayi kyau sosai kuwa, yanzun kika zama yan mata"
Shagwabe fuska Waheedah tayi
"Me kike nufi Mami?"
Amatullah ta karbe zancen da amsa ta
"Kinfi kowa sanin me take nufi"
Numfashi Mami ta sauke
"Nikam ku matsamun ina da aikin yi"
Matsawar sukai ta wuce, suna rufa mata baya zuwa kitchen din.
Wanke-wanke sukayi ita da Amatullah din.
Sun gama kenan, Amatullah ta fice daga kitchen din, Nuriyya tai sallamar da Mami ta amsa mata tana dorawa da
"Nuriyya idonki kenan?"
Dariya Nuriyya tayi, dan kwana biyu bata shigo gidan ba, itama sunata hidimar sallah
"Wallahi Mami inata kitso ne fa.
Ina kwana"
Murmushi Mami tayi
"Lafiya kalau, ya kowa da kowa?"
Da murmushi a fuskar Nuriyya take amsa Mami data fice daga kitchen din bayan sun gama gaisawa.