← Book details Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 94

Sashe 87

Abdulkadir Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ki kirasu a kawo miki shi"
Kai ta girgiza mishi
"Ni kunya nakeji ai"
Dan murmushi yayi
"Lallai yarinyar nan, nine sarkin rashin kunya ko?"
Dariya Waheedah ta tsinci kanta dayi tana girgiza mishi kai
"Haka kike nufi mana, ba zanje ba to, in kina kewar shine ki kirasu da kanki"
Ya karasa maganar yana juyawa dan bacci zaije yayi daman zai duba ya suka tashine.

"Dan Allah ka dauko mun yarona"
Juyawa AbdulKadir din yayi yana harararta ya fice daga dakin yaja mata kofa, dariya take sosai, har ranshi tasan harara ce yake ganin yanayi, amman idanuwan shi basuda girman da zasu juyu har suyi hararar, bata taba gaya mishi bayayi dai-dai ba.

Sai dai tasha dariyarta kawai.

Ikram ta dauka tana cire mata kaya, dan wanka zatayi mata, itama tayi, sai suzo suyi baccin.

Bacci yayi har wajen sha biyu sannan ya tashi, ya watsa ruwa ya fito yana zaune bakin gado, Nuriyya na kai tana danne-danne waya, dan group dinsu an turo wasu laces masu bala'in kyau.

Kuma duk wanda yake cikin group din yace yana son guda daya, ita kadai ce batace a ajiye mata ba, dan taji Hajiya Kaltume mai siyar da kayan tace kudi hannu ne, ba zata bayar da bashi ba wannan karin, da sai ta dauka sai karshen wata.

Gashi kowa sai magana yakeyi ita ba zata siya ba, tana ta kallon sune batasan me zatace ba, kar a rainata.

"Masoyi"
Ta kira cikin sanyin murya, tana saka AbdulKadir din kallonta
"Kaga wani lace"
Ta fadi tana nuna mishi wayar, kallo yayi yana jinjina mata kai
"Yayi kyau"
Ya amsa a taqaice yana daukar tashi wayar da take ajiye a gefe.

Murmushi Nuriyya tayi dan taga alamar zatayi nasara
"Dubu arba'in da biyu"
Kai kawai AbdulKadir ya jinjina mata baice komai ba yaci gaba da danna wayar shi, da sauri tace
"In dauka zaka biya kudin?"
Dago idanuwan shi AbdulKadir yayi yana kallonta kamar bata da hankali
"Wai me kika daukeni ne Nuriyya?

A bishiya nake tsinko kudi kome?

Kin manta kudina da kika kashemun, kin sani saida na taba wasu dana ajiye dan wani abin, har kina mun maganar in sai miki abin dubu arba'in da biyu.

Ina nagan su?"
Kallon shi take dan in jikinta zai zama kunnuwa ba zata taba yarda bashida su ba, da cayai mata ma bazai bayar ba sai yafi mata saukin yarda.

Wayar shi AbdulKadir yaci gaba da dannawa yana nemo text din albashin shi ya ajiye wayar kan gadon yana turama Nuriyya data dauka
"Bansan kallon me kike mun ba, amman ni ba wasu kudi gareni ba, kinga albashina nan duk watan duniya, a ciki nake duk hidimata, katon gidan nan kudin allowance ne na wasu ayyuka, haka motata, bawai albashina bane, sukuma sai ayi shekaru ba'a same su ba.

Idan ban taba fada miki ba yau kisani, ni bamai kudi bane, cikin layin masu rufin asiri ma a tsakiya za'a sakani"
AbdulKadir ya karasa yana mikewa ya fisge wayar shi daga hannun Nuriyya yana ficewa daga dakin yabarta a zaune gabaki daya jikinta ya gama mutuwa.

Tabbas yau kallon kitse ake ma rogo ne ya tabbata a kanta, wannan albashin na AbdulKadir sam-sam bashi bane burinta ma hamshaqin mijin da take son aure
"Tafdin..."
Ta fada ranta a jagule, kwata-kwata yanda ta hango AbdulKadir ba haka yake ba.

Daga halayen shi har kudin shi, ita da bata hango ckarta shekara daya a gidan batare da tayi motar kanta ba.

Da wannan yagalgalallen albashin yaushe harya tara kudin da zai siya mata mota.

Wani kunci takeji yana taso mata tun daga yatsan kafarta yana mata zaune a kirjinta.

Harma fada mata yake shi ba kudi yake dasu ba dan karta sa ran zai mata wani abin arziqi.

Har ranta take jin babu wanda ya cuceta sai Waheedah, babu babbar makira irinta, ita ta dinga nuna mata kamar tana cikin daular rayuwa, ita kuma ta dinga mata hidima kamar AbdulKadir din wani hamshaqin mai kudine, ita taja mata duk wannan abin da take ciki, dan ita ta haska mata AbdulKadir din taga kyallin shi harta kwadaitu da auren shi, amman da duk mintina take ganin abinda bataso a tattare dashi.

Gani tayi bakin ciki zai mata katutu, ga whatsapp din data bude harta private Hajiya Kaltume ta mata maganar siyan lace din nan, hankalinta ya kara tashi, hakan yasa ta janyo system dinta, drawer din gefen gado ta janyo ko ta saka earpiece dinta a ciki, taga wata leda da batasan ta ajiye ba, dagota tayi taga kudine a ciki, sai da zuciyarta tai wata irin dokawa, warware ledar tayi tana zazzago kudin kan gadon, ganin su tayi da yawa sosai, da sauri ta tashi ta saka mukulli ta kulle kofar ta dawo, kudine masu yawan gaske dan ba'a dauresu ba, hakan ya sata tunanin da alama ana zararsu ne.

Tasan AbdulKadir din kan ciro kudi ya ajiye ana diba, dan tasha zara kuma bai taba ganewa ba tunda bai mata maganar ba.

Duk da zuciyarta na dokawa, wani abu kasan ranta na fada mata kar tayi, dubu arba'in da biyu ta kirga ta ware su a gefe, ko kwatar kudin bataga alama sun girgiza ba, tasan ba kirgawa zaiyi ba, da sauri ta gyaggyara su ta mayar cikin ledar tana nannadewa kamar yanda tagani ta mayar ta rufe drawer din.

Wanda ta diba din ta mike ta samu jaka ta zuba su a ciki.

Kafin ta zauna taji ana kwankwasawa, da yake ta saba dibar kudin Anas ko dar bataji ba, taje ta bude mishi kofa, baice mata komai ba ya rabata ya wuce.

'Namiji munafuki'
Ta fadina ranta, daman akance namiji bazai taba nuna maka samun shi ba, yau ta kara yarda, yanzun ya nuna mata wani alert kamar mai gaskiya, jibi kudin da ta gano.

Daman tanata tararrabi anya ace bashida kudin da take tunani.

Tana kallo ya bude drawer din ya dauki ledar ya sake zuwa ya fice, dakin ta tura.

Ta koma kan gado tana daukar wayarta taba Hajiya Kaltume amsa
'Ni banda kudi a banki, Cash ne bansan ya za'ayi ba, gashi yau bazan fita ba, ni nake da girki'
Ba'ayi mintina biyu ba Hajiya Kaltume ta amsa ta
'Kibani address din zan turo yaro yazo ya karba'
Tura mata tayi kuwa tana komawa kan gado ta zauna.

Ko da kirgawa AbdulKadir yayi yagane an diba sai ta bashi hakuri, fadane zaiyi saita toshe kunnuwanta ta kyale shi, in aka kawo lace din ta daura a jikinta zai wanke mata haushin shi da zataji na dan wani lokaci.

Ko mintina sha biyar ba aiba, taga kira yaron harya iso kofar gida.

Kudin ta dauka ta saka hijabi ta leqa ta kai mishi, saida ya kirga a gabanta tukunna ta dawo gida, tana jin wani abu yadan kwanta cikin bacin ran data shiga.

"Hamma kasan fa bani da lafiya, gashi ana rana, ina azumi ka fito dani"
AbdulKadir ya fadi yana mika mishi ledar kudin da sun kai kwana goma a ajiye a wajen shi, dan Yassar din yayi cinikin mota zai sake wata, tashi nata bashi matsala, daya ciro kudin sai cinikin bai yiwuwa ba, yana jin qwiyar komawa bank ya kuma san halin shi, ko Hauwa yaba ta ajiye saiya bi ya karba ya kashe.

Amman idan AbdulKadir dinne ba zai bashi ba sai dai ko in lalura.

Yanzun ma dan yace ga motar an kawone an gama komai, kudinne kawai zai basu, tashi motar ma har wanda ya siya ya dauka tukunna AbdulKadir din ya fito da kudin.

Ya daukama dakin Waheedah ya ajiye, dan yaje yana nema, ta taya shi basu gani ba, kafin ya tuna dakin Nuriyya ya ajiye.

"Kai kamar ba soja ba"
Kankance mishi idanuwa AbdulKadir yayi
"Ina gida yanzun, kabarni.

Kuma ma dan ina soja sai akace duk wahala in dinga jureta"
Kai kawai Yassar ya girgiza mishi yana karbar kudin ya basu.

Suna tsaye aka kirga
"Dubu dari hudu ne babu arba'in da biyu"
Da mamaki Yassar yace
"Bangane ba"
Dan yasan kudin shiya ciro su da kan shi
"Eh babu dubu arba'in da biyu"
AbdulKadir ya kalla yana fadin
"Ka taba kudin nan ne AbdulKadir?"
Kai AbdulKadir ya girgiza dan baima ji me suke fada ba, hankalin shi nakan wayar shi da yake duba sako
"Me ya faru?"
Ya bukata yana mayar da hankalin shi kan Yassar din
"Wai basu cika ba, babu dubu arba'in da biyu"
Dagowa AbdulKadir yayi daga jikin motar shi
"A kara kirgawa dai"
Ya fadi saboda bayason abinda ya fara zuwa kan shi ya tabbata, sam bayaso, mutumin kuwa bai musu gardama ba, wannan karin duk a tare suka kirga kudin, babu dubu arba'in da biyun.

Wallet din shi AbdulKadir ya zaro yana dauko ATM din shi ya mikama Yassar
"Kasan password din"
Wani irin kallo Yassar ya watsa mishi kafin yace
"Bana son iskancin banza da wofi"
Kai kawai AbdulKadir ya jinjina yana mayar da ATM din inda ya dauko shi, batare da yace komai ba ya bude murfin motar shi, ran shi ya dade bai baci ba irin haka.

"AbdulKadir me ya faru?

Ka fito daga motar nan muyi magana"
Yassar ya fadi ganin yanayin fuskar AbdulKadir din, amman mukullin motar shi ya murza yana tayar da ita, duk maganar da Yassar din yake mishi baiji ba ya fisgi motar yana hawa titi...!
#TeamAbdulKadir
#TeamWaheedah
#LubnaSufyan
[7/16, 9:56 PM] +234 802 111 7692: Facebook: Lubna Sufyan
IG: SufyanLubna
Email: [email protected]
Wattpad: https://my.w.tt/Fk2tdtKc43
YouTube: https://youtu.be/WwocHslDAYk
*ABDDULKADIR*
*LubnaSufyan*
To my fav Aunt (Rabi'atu).

Allah ya shiga lammuran ki.

Amin thumma amin
Tunda ta gama baccin safenta ta gyara bangaren ta tsaf, sannan tayi wanka ta shiga kitchen.

Dan wanke-wanken da take dashi tayi.

Ikram na kwance cikin kekenta tana bacci.

Fridge din ta duba taga tana da naman rago, kawai sai marmarin tuwon semo da miyar dan yar kubewa ya kamata.

Fito dashi tayi dan ya huce, yayi kankara, ta dauki Ikram suka fito ta kulle kitchen dinta.

Daki ta koma ta kira Naziru a waya tace yaje ya siyo mata danyar kubewa ya kawo mata in yazo sai ta bashi kudin.

Hakan kuwa akayi, dadewar da yayi har bayan azahar yasa ta dauka ma ya manta dan tasan shiriritar shi.
Chapter 87 · 0% Book details