Sashe 99
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read
...Bana fushi dake Allah ya shiryeki kasancewar yau Friday su Aysha Da Ummy sunzo Ummy da d'anta Khalil har an yayeshi Daukarshi Mamy tayi ta ce "To mai Gidan ina Goron Juma ata" Murmushi sukayi suka gaisheta Aysha ce dai har yanzu bata haihuba da ta samu ciki yake b'arewa sau Ukku tana bari kenan Hakan yasa hankalinta duk ba kwance ba danma dangin mijinta suna sonta basu tab'a ko gora mata ba haka mijinta bai damu da hakan ba yasan haihuwa ta Allah ce kuma idan da rabo suma zasu samu ga tunanin halin da y'ar uwarta da take ciki da ta sanya a ranta Suma Duka saida amma ta nuna musu hoton twins suma sosai yaran suka burgesu ga mamakin su na kamannin yaran da Arman ranar duk saida suka jajinta Rashin Aira a tattare dasu Amma da Aysha hada kukansu Ummy cema tayi hawaye kawai Sosai Aira da Amma suke chat batare da Amma ta gane Aira ba Dan bata yi mata voice koda wasa ko video call ta kira twins kawai take haska mata bata yarda ta ganeta a yanzu Twins Nada shekara guda Wanda Mummy ta kawo musu ziyara kwanakin baya tayi one week ta koma tuni sunfara Dan cin abinci ta tafiya jefi jefi ga dumur dumur da kyau da Yaran suke karawa sosai Aira take Kara samun followers Dan yanzu yaran tuni sun baza duniya duk mahalukin dake tiktok tofa yasan da zaman Naila_da Nihal har yanzu Arman baisan Aira tana d'ora masa yara a duniya ba. Da misalin Sha d'aya na rana Twins na wasansu a palour su janyo wannan sun janyo wancen an baje musu kayan wasa a palourn saiyi suke suna Dariya Iyayen ko na like da juna Suna Zuba love d'insu Yanda ya kamata wajen 12 sukaji Nihal ta k'walla k'ara ta zube a wajen cikin rud'u Suka nufi wajen cikin fitar hankali Arman ya sungumeta ya na jijjigata ya ce "Lafiya meya sameta " kafin ya rufe bakinsu Naila ma ta fara kakkarwa da kakkafewa ihu Aira ta fasa ta ce "Na shiga ukku meya samesu ta fad'a tana sungumarta da take kakkafewa Arman bai sauraretaba makullin mota ya d'auko Ya figa suka tafi Asibiti yaran a hannunsu a rude Suna zuwa cikin gigita sukayiwa dr bayanin abunda ke damunshi amsarsu yayi cikin gaggawa tare da wucewa da su Emergency durk'ushewa a wajen Aira tayi tana matsanancin kuka Kar dai wani Abu ya samu twins din nata " Suna zaune Dr ya fito Cikin gaggawa ya ce "Ana buk'atar Kara musu jini nawa za a d'auka" Cikin Sauri Arman ya ce "nau mana Dr Dan Allah ka taimakamun kar wani Abu ya samu yarana " Cikin gaggawa aka Auna jinin Arman akaga Yayi daidai Nan aka d'auka Inda likitan ya bawa su Naila Gado ya sanya musu a lokacin duk sume suke Shi kanshi yayi mamaki ace jinin yara ya zuke haka lokaci guda gashi yaran baiga Alamun Rashin jini a tattare dasu ba wani tunani ne ya fad'o masa Tabbas yaga yanda ake dora yaran nan a media Dan ya sansu shi kanshi farin sani Tabbas y'an shan jinine suke neman Shanye musu jini dayake musulmi ne Wani malaminshi ya kira Akan Dan Allah yazo yayi wani taimako ta Cikin wayar yayi mushi bayani da yake malamin mai taimakone ya ce gashinan zuwa su Aira sunyi jugum jugum sai risgar kuka take Arman shinema mai k'arfin halin Lallashinta Suna tsaye sukaga wucewar Malam Cikin office d'in Dr d'in binshi sukayi Dan sungaji da jira A tare suka shiga cikin kuka Aira ta ce. "Dr kar yarana su mutu Dan Allah Dr ina sonsu wlh ka taimaka mana" kallonsu Malam din yayi ya ce "Karku damu Kuyi musu addua Sannan ya kalli Dr Bayan sunyi musabaha ya ce " Ina yaran suke"Mikewa Dr yayi ya ce "Bari muje d'akin da suke a tare suka shiga d'akin harsu Aira Hango yaran nata yashe gadon marassa lafiya karasawa tayi ta fashe da kuka tana sabbatu Dak'yal Arman ya tadota Kallon Dr yayi yaa ce " akawo ruwa a cup"miko masa akayi ya jima yana tofa adduo'i a cikin ruwan kafin ya k'arasa Inda yaran suke ya yayyafa musu Nan take suka kawo numfashi tare fara kikkifewa Rikesu Malam yayi Inda ya shiga tofa musu Adduo i da karatu yayi minti Talatin a kansu dayake Babban malamine su Aira duk sai kallon ikon Allah suke Chan sukaji sun tashi tare da Fara tari sai kuma suka fara kuka "Cikin farinciki aira taje ta rungumesu tace " Alhamdulilla Allah nagode maka"Ajiyar zuciya Malam ya sauke ya ce " Alhamdulilla a Gaskiya yaran nan sun Auna arziki wlh inbanda dr kayi tunanin gane kan matsalar da Saidai wani ikon na ubangiji masu shan jini ne suka kamasu suka fara Shanye musu jini amma sun sakesu yanzu insha Allahu Saidai a cigaba da musu adduo'i Sosai sannan a kiyaye da yawa iyayen yanzu kuna sakaci da Yaranku saikiga yaro gashi bud'e ko anyi kitso yayi kyau an bud'e ko kaga ana d'ora yara social media Wanda hakan duk ba dacewa bace ta wannan hanyarce har ire_iren mutanen nan suke samun daman Shanye jinin Yaranku ku daina Sakaci da Addua Allah ya kiyaye gaba "Ameeen dr da Arman suka fad'a sosai suka shiga yiwa malamin Godiya Inda ARMAN ya bashi check din one million da farko kin karba yayi ya ce Ai aikin Allah ne yayi Dak'yal dai ya samu ya amsa Inda ya rubuta musu Adduo i sosai Wanda zasu dinga yiwa yaransu dasu kansu na tsaro. Bayan barin Malam wajen Kallon Arman Dr yayi ya ce " Bro Gaskiya Ku daina d'ora Yaranku a media baki da ido yayi musu yawa "da mamaki Arman ya ce " media kuma dr ai yaran nan bama Dorasu media Ko what's app ba Dorasu mukeba ko Ya fad'a yana kallon Aira dake feeding d'in yaran gabantane ya bada daram shikenan yau asirinta ya tonu"Kasa da kanta tayi gabanta na fad'uwa Lalubo Wayarshi Dr yayi ya shiga shafin Oum twins Naila&Nihal nan take Abubuwan yaran suka bayyana mik'awa Arman Wayar Dr yayi ya ce "Wannan ba su bane " Da mamaki Arman ya amsa Inda ya shiga Dubawa Tabbas sudinne Post d'insu yafi d'ari Ukku Kome suke ana d'auka ana dorawa Hatta shigarsu ta yau da safe yaga an d'ora sosai ranshi yayi mugun b'aci"idanunshi da har sun sauya launi ya kalli Aira datayi kasa da kanta ya ce "Uban waye yake doramun Yara a tsinannan abunnan " kasa tayi da kanta gabanta na fad'uwa ta kasa magana "Tsawa ya daka mata da ta mance rabon da yayi mata ya ce " nace ubanwa Yasa ki dinga doramun y'ay'a a duniya tallarsu nake ,ko me Da izininwa kika bud'e tiktok ?tuni Aira harta fara hawaye Cikin rud'u ta ce "Dan girman Allah yaya kayi hakuri?zuciyar ARMAN banda tafarfasa ba abunda take sosai ta bata masa rai to yanzu da yaranshi sun mutu fa a saboda dorasun da take har y'an shan jini zasu kashe musu yaya Tabbas saiya d'auki mataki bazai kyaletaba (hakan yana Faruwa sosai wlh Iyaye a dinga kiyayewa Allah ya kara kiyayewa ameeen)Tsawa ya daka mata ya ce " Ajemun yara na "Cikin rudu tana hawaye ta mik'e Dan baitab'a mata haka ba tsawon rayuwarsu tare da Jan baya hanyar kofa ya nuna mata ya ce " Get out."Yay....tsawar da ya daka mata ya sanyata saurin barin dakin hada tuntube tana kuka waje ta samu kofar D'akin ta durkushe tare da fashewa da kuka itakam ta bani Kenan yanzu da masu shan jini sun kashe mata yara bata tab'a tunanin hakanba ga ARMAN yanda taga yayi mugun fushi kuka take sosai Tana danasanin d'ora Yaranta da take Arman ko zuwa yayi ya Rungume yaran daman sunsaba da Daddynsu hakan yasa sukayi shiru jikinshi suna wasa da gemunshi yana musu wasa a haka har jinin ya k'are Inda Dr d'in yazo ya cire tare da rubuta musu magani Godiya sosai Arman yayiwa Dr d'in Inda ya amshi number shi Shima yayi mashi alkhairi sosai Rungume Naila datayi bacci a kafad'arshi yayi tare da d'aukar Nihal da idonta biyu ta lafe jikinshi yayi a haka ya fito Kallon Aira yayi data hade kai da guiwa tana kuka ya ce "Wuce mu tafi" cikin Sauri ta mik'e tana kuka ta ce "Dan Allah yaya....d'aga mata hannu yayi ya ce " banson jin komai daga bakinki Goge hawayenta tayi tare da bin bayansu zasu shiga mota mik'a masa hannu tayi zata amshi Naila tsaki yaja tare da kallonta ya ce "Ai bazaki Kara daukarsuba tunda bakya sonsu ni inason abuna kuma zan kula dasu daga yanzu kika k'ara daukarmun yara duk abunda na maki ke kikaja" Jan bakinta Aira tayi tana Hawaye Dan tasan sahibin nata yayi fushi sosai da ita a baya ya kwantar da Naila Inda ya na rik'e da Nihal ya shiga matuk'ar driver ya sanyata gabanshi yana tukawa ganin zai tada motar ya sanya Aira saurin shiga gaba tare da rufewa harsuka isa gida baice uffan ba itama sai hawaye take suna isa ya zagaya ya d'auki Naila da ta tashi ta fara kukan yunwa a palour suka baje Inda ya had'a musu madararsu ya basu daman suna sha sosai nan suka shiga sha a lokacin kasancewar magriba ya sanyashi Zaunar dasu yasa musu abun wasa yaje yayi alwala ya tada salla Yana gamawa yaje ya lalubo turaren da goggo ta taba basu basu taba amfani dashi ba na miyagu da iska nan ya hada boner ya sanya take dakin ya bide da kaurin maganin inda daya bayan daya ya turare yaran saida yaga sun fara tari alamun hayakin ya fara musu yawa tukwana ya dauke Aira ya kalla da duk tayi jugum tana hawaye ya ce "Bani wayarki ?Jikin charge ta cirota Dan daman tana chaji suka tafi mik'a masa tayi Daman ba security Tiktok din ya shiga ya shiga bincikawa yaga itadince duk gashinan ta daddora Wasu frnds d'inta yabi Wanda suma suka d'ora yaga wata Rahama ta d'ora yafi sau goma sai lemart da yaga ta d'aura sau Ukku sai wata Jannat Abuja Itama ta d'ora so biyu duk saida ya k'ara biccinkawa yaga su kadai suka d'ora Kallonta yayi fuska