Sashe 25
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 7 min read
......Ya ce "me ya kawo wannan gida na me take a gidana maza maza ki gaggauta barin gidannan kafin na sauya maki kamanni" Aira cikin tashin hankali ta tashi ta Ruga ta boye Bayan Mamy ta makalkaleta tare da sakin kuka ta ce "Dan Allah Abba kayi hakuri Bazan sake ba " Mama Halima ce ta ce "Kayi hakuri Dan Allah yaya bazata sake ba ka zauna muyi magana ta fahimta" Ba wata maganar fahimta Halima daman na lura yanzu dake kike d'aurewa yaran nan gindi me ya maidota gidana ta koma gidanki bani ba ita na hakura da ita ko ita kad'aice y'ar da na Haifa na hakura da ita ku gaggauta ta barmun gidana bansan ganinta"Aira kuka ta k'ara fashewa dashi ita kam ta shiga ukku dak'yal Mama da Mama Halima suka dinga bawa Abba hakuri suka samu ya zauna Mama Halima ta ce "Dan Allah yaya ka saurareni muyi magana munsan sunyi laifi amma kayi hakuri saika yanke mata hukunci cikin nutsuwa ai hannunka bai rub'ewa ka yanke shi ka yar" Abba na huci ya zauna ya ce "wani hannun tuni kake yardashi karya isheka da Wari ku maza ina Sauri ku fad'amun me ke tafe daku" Ajiyar zuciya Mama Halima ta sauke ta ce "Daman yaya akan maganar Mamana ce nazo mu baka hakuri Dan Allah kayi hakuri ka yafe mata Allah ma munayiwa laifi ya yafe mana " Ai babu wani zancen daidaitawa Nida wannan yarinyar tunda bazatabi umarni na ba to fa nima bazan sassauta mata ba Ai tunda har ta iya d'aukar kafa ta tafi har kaduna wajenki nikuma ai tafi k'arfi na ta koma wajenki da zama bani ba ita "cike da damuwa Mama Halima ta ce " wannan laifi na ne Yaya wlh ni na sanya Mujahid ya kaimun ita saboda nasan kayi fushi daman jira nayi ka huce amma kayi hakuri Dan Allah ina neman alfarma Dan Allah Dan darajar iyayenmu da suka haifemu suna k'asa ka taimakamun ka yafe mata wlh tayi nadama bazata sakeba "ta k'arasa fad'a tana hawaye " shiru Abba yayi yana daidaita nutsuwarshi na y'an sakanni.kafin ya d'ago ya ce "Wlh taci darajarki da kuma darajar iyayenmu da kika Ambata zan yafe mata ta zauna a gidana Amma saida sharuddan nan da zan lissafo guda hud'u kuma cikinsu ba d'aya da za a kuskure idan kun amince dasu to zata zauna a gidana idan kuma baku amince su ba to na hakura da ita ta koma gidanki ko kuma taje duk Inda zata na hakura da ita" Cikin Sauri Mama Halima tace "munyarda zamu amince insha Allahu wasu sharudda ne" Aira ko duk ta tsure tana like da Mamy sai kuka ta ke Itadai Mamy batace uffan ba Yaya Umar ma saurara kawai yake Dan baisan case d'inba daga Mama Halima sai Abba kadai suke magana "Abba ya ce " sharad'i na farko shine "zata zauna a gidannan bazata k'ara lek'a ko bakin get ba hatta ko Tahfex na cireta bazata k'ara zuwa ko ina ba sannan zata dawo nan part din ko bangaren Inna nayi mata iyakar shiga kun yarda da wannan?Ajiyar zuciya Mama halima ta sauke ta ce " Mun yarda,na biyu kuma "Babu zancen jonawarta Makaranta Kamar yanda ko wani d'ana nake tsaye musu harsu kammala Degree d'insu kuma shine Babban burina da tsarina tundaga kan yayyinta to banda ita ko Diploma bazatayi ba " Kallon Aira Mama Halima tayi ta ce "Kinaji kin yarda " gyad'a kai Tayi tana kuka Alamun ta yarda "Kallonshi Mama Halima tayi ta ce " Shima mun yarda " Na Ukku babu ita ba Yaron Chan Nayi mata katangar karfe dashi babu wace alaka ko a fili ko a boye da zata k'ara shiga tsakaninsu Shima kun yarda da shi?Mama Halima cikin damuwa ta ce "Haba yaya d'an uwanta ne fa " d'aga mata hannu Abba yayi ya ce "na fiki sanin hakan amsa kawai kun yarda eh ko a a " Kallon Aira Mama Halima tayi Ta ce "Kinaji abunda yace Amsa na wajenki kin yarda?Sosai Aira ta shiga tashin hankali amma kuma ba yanda zatayi muddin tanason zaman lafiya da mahaifinta dole ta amsa ta ce " Eh na yarda"Amma har cikin zuciyarta ba wai ta yarda zata rabu dashi d'inba ta amsa ne kawai Dan ta samu sassauci.Kallon Abba Mama Halima tayi ya ce "mun yarda " To hud'u kuma na k'arshe shine "Aure zanyi mata?Cikin tashin hankali Mamy ta mik'e ta ce " Aure kuma Alhaji Sadakarta kake nufin zaka bada ko me?Eh Aure Kamar yanda na fad'a Tunda shi take so kuma shi zanyi mata bazata daukomun magana ba sannan ko sadakar ta kama sai inbadata abunda ya dace da ita ai"Tashin hankali ba a gwada maka rana Aira ita bama zata iya cewa ga halin da take cikiba kuka kawai take " Mamy ce ta ce "Wlh Ba a isa ba Daman na lura duk cikin gidan nan ka tsani Y'ata Duka cikin Y'ay'anka wa kayiwa Aure a age d'inta sai ita Dan tsana me ta tsare maka a gidan shekarar sha 18 ma bata ida ba to Allah bazan yarda ba laifin me tayi ko cikin shege tayi ai sai haka Inbanda lalacewa akan d'an d'an uwanka ake wannan Abun laifine Dan sunyi soyayya dashi matsafine ko d'an giya ne ko kuma wani mashahurin boka ne da za a sanya mun y'a cikin wani hali dan tana sonshi ai ba sab'on ubangiji bane Ku barsu mana Suyi soyayyarsu inma Aure ta kama ni ina bada goyon baya d'ari bisa d'ari tunda suna son junansu amma wlh bazakayiwa y'ata Aure ba yanzu " ta k'arasa fad'a cike da masifa "Tashi Abba yayi ya nuna ta da yatsa ya ce " Sau nawa zan fad'a maki idan ina yanke hukunci akan y'ay'ana ki dainamun katsalandan Ke kike da iko akanta ko ni Na rantse da Allah idan ba so kike ranki yayi mugun b'aci ba na kowa ya b'aci ki k'ara shigarmun idan na yanke hukunci "ran nawan ya b'aci na kowama ya b'aci sai me ko me zakamun yau kamun a shirye nake wlh " Mama Halima ce ta kama hannun Mamy ta ce "Dan girman Allah Rahama kiyi shiru tun d'azu da muke magana bakisa bakiba yanzu ma kiyi shiru kiwa girman Allah da darajar iyayenki ki wuce d'aki "Dakyal Mama Halima ta samu Mamy ta wuce ciki " Mama Halima tace "Yaya ku rik'a sassauta zuciyarki Dan Allah kayi hakuri ka janye maganar ka ta k'arshe sauran Duka mun amince dasu na karshen ne yayi tsauri" Cikin fad'a Abba ya ce "to ku tashi ku bani wuri daman na ce muku ai d'aya bazan hakura cikin hudunnanba idan baiyi mukuba babu dole ku tashi ku barmun gida Aira da take shan kuka Muryarta harta dishe ta ce " Na amince Abba "ta fad'a tare da tashi tana kuka ta wuce Bedroom d'in Mamy tana Zuwa ta haye kanta ta fashe da kuka Kamar wacce akayiwa mutuwa " sosai kowa dake palourn saida ya tausayawa Aira sai sannan Yaya Omar yayi magana ya ce "Dan Allah Abba kayi hakuri ka janye na karshen" Na gama magana kuma babuja da baya Abba ya fad'a tare da tashi ya fice part d'inshi"Girgiza kai Mama Halima tayi ta ce "Nima Allah ya kawoni Allah ya kyauta tukwana ta wuce d'akin mamy ta samu Aira na kanta sai risgar kuka take Mamy ko tayi tagumi sai huci take " Zaunawa gefen gadon Mama Halima tayi ta ce " Kuyi hakuri Rahama Kalar tamu jarabawar kenan Allah ya bamu ikon cinyeta "Cikin hawaye Mamy ta ce " Yanzu Halima ki duba kiga Akwai adalci a maganganun Alhaji kuwa"numfasawa Mama Halima tayi tukwana ta ce "Ni fa a ganina duk wannan maganganun yayi su ne cikin fushi Amma bazai aiwatar ba tunani na kawai zai tsorata ta da haka ne amma sai nakega bazai mata Aure ba Ki duba kiga yayyinta Duka saida suka kammala Degree d'insu A kanta bazai karya akidarshi ba ku kwantar da hankalinku kawai tsoratarwa ce sannan ma idan yace zai mata Auren itada yanzu ya hanata fita ina ma zata fita bare har wani yace yana sonta " bakiji me yace Ba sadakarta zai bada Mamy ta fad'a tana hawaye "Duka fad'ine yayi Dan mu tsorata Amma bazaiyuba zai sauko nan kusa" Ajiyar zuciya Mamy ta sauke ta ce "kila kuma hakanne Allah dai ya shige mana gaba " Ameen Mama Halima ta fad'a Aira duk tanajinsu sai sannan hankalinta ya Dan fara kwanciya Dagowa tayi cikin kuka ta ce "Mama Dan Allah ki rok'eshi ya bari mu koma Kadunan tare" Chab Inani ina wannan Mamana kina ganin dak'yal ma muka samu ya amshemu idan nace xan koma dake ai rikicewa abun zaiyi ki bari idan aka kwana biyu Zan dawo nayi yanda nayi na shawo kanshi ya bani ke sannan ya huce sannan kuma ki kiyaye ki hakura da Mujahid na wani lokaci "Gyada kai Aira tayi tana Hawaye taje ta Rungume Mama tana kuka Dak'yal Mama ta lallasheta harta samu ta hakura.