← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 127

Sashe 109

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani private hospital suna isa kai tsaye labour room aka nufa da ita ya nan yana safa da marwa yaji kiran Mama Halima Bayan ya d'auka ya shaida mata asibitin da suke ba ayi minti goma ba sai gata cikin rudu ya nuna mata d'akin da take Kallonshi tayi ta ce "kun taho da kayan haihuwarne?a a Mama bamu taho da komai ba " To.ka maza kaje ka sassayo da abunda za asa jaririn da komai nikuma bari naje "To ya fad'a duk ya rud'e tare da tafiya neman abunda Mama Halima ta fad'a ita kuma ta shiga ciki Inda ta samu Aira na labour sosai Sannu ta dinga mata a lokacin Tara na dare Karfe sha biyu Aira ta haifo d'anta namiji kyakyawa dashi mai tsananin kama da ita Bayan ta haihu a lokacin Arman ya kawo jibgin kayan da ya sayo hamdala kawai yake da yaji ance ta haihu Bayan anshirya jaririn itama Aira anshiryata d'akin Hutu aka wuce da ita saboda galabaita da tayi Gashi kuma taso tayi ikilamsiya saboda jininta da yahau Allah dai ya kiyaye Arman sosai ya ji soyayyar yaron a ranshi koda ya daukeshi cikin farinciki Yayiwa Allah Godiya Yau shine da yara har Ukku Tambayar Mama Halima Aira yayi ta ce " bazai samu ganinta ba saita huta sannan ta amshi jaririn ta ce "sauran kayan da ka jibgo ka wuce dasu Gidana sannan kace Hafsa ta gyara d'akinsu " to Arman ya fad'a nan takura ya shaida wa Mummy haihuwar itama Sosai tayi farinciki marar musaltuwa Aira ko sosai ta huta duk galabaice take Dan bama tasan abunda ta Haifa ba Mama Halima Tabawa jaririn ruwa gashi baiyi kuka sosai ba ranar Aira kwana tayi tana bacci Dan Dr d'in saida yayi mata allurar bacci saboda jininta da yau ya sauka washegari itace bata tashi ba sai 10 koda ta tashi Su Hafsa sunzo duk Sannu suka dinga mata Har Arman da yake tausayawa cutie d'inshi ganin yanda tayi firi_firi Mama Halima tayi mata wanka ta gasata sosai Bayan sun shirya ta bata yaron akan tayi feeding dinshi sosai Aira ta tsaya Kallon Yaran tanajin soyayyar shi kamar yanda takeson twins a zuciyarta ta ce "Allah ya raya munkai " a fili kuwa shiru tayi saboda nauyin Mama Halima da takeji Bayan an b'ata tayi Kari me kyau A yammar ranar aka sallamesu ta koma gida duk tayi shiru bata son magana sosai saboda ciwon kan da take "Wanda saida aka rubuta mata magunguna akan ta dinga sha. Washegari Mummy tazo ita da twins a lokacin Aira na D'aki tana kwance Kanta banda ciwo ba abunda yake Dan tunda ta haihu take wannan ciwon kan Mummy ta shigo Tare da twins dak'yal ta tashi tana kirkirar murmushi ta ce " Sannu da zuwa mom"yawwa daughter ya jikin naki barka ko Allah ya raya k'asa da kanta Aira tayi Twins ne sukaje Wajenta Suna mata murmushi itama mayar musu tayi Naila ta ce "Sannu cutie mom ya jiki baby boy d'in da muka gani namu ne ko"? Itama Nihal cewa tayi " Mom ai boy dinmune ko wai Mama tace bazata bamu ba ta fad'a tana turo baki"Dariya Aira tayi ta ce "sarakan surutu " Dariya Mummy tayi ta ce "Kunga kubar maman taku ta huta" k'iyawa sukayi suka D'are Aira Girgiza kai tayi sannan ta Kalleta ta ce "Ki fad'a abubuwan da kike buk'ata a sunan daughter saina taho maki dashi Dan anan za ayi sunan tunda naga jikin naki ba adinga yawo dake ba " Kasa tayi da kanta ta ce "ba komai Mummy duk yanda Mummy tayi Aira ta fad'a abunda takeso kiyawa tayi ta ce komai ma ta yanke yayi " Ita Mummy duk sai ta bata tausayi ganin irin sanyin da tayi Lallashinta ta dingayi gami da nasiha Cikin hikima "Da yamma Mummy suka wuce tare da twins dan yanzu sunyi mugun sabawa da mum " da dare Aira na kwance tana kallon boy d'inta Arman ya shigo Dagowa tayi ta Kalleshi da murmushi a fuskarsa ya zauna tare da d'aukar jaririn ya ce "Sorry my boy yau bamu gaisa ba ko to ya jikin mom d'in taka" ya fad'a yana kallon Aira ya ce "ya jikin cutie" Murmushi ta masa ta ce "Alhamdulilla" "Allah ya k'ara maki lafiya uwar y'ay'ana yasa kaffarane " Ameen ta fada "Huduba tayima yaron Bayan ya gama Kallonshi Aira tayi ta ce " wani suna ka sanya masa "Aliyu Haidar " Munyiwa Bappa takwara Saboda shi ya zama silar samun wannan farincikin namu "Murmushi Aira tayi Tabbas hakane ta ce " Allah ya raya my hero ka kyauta kuwa "Sun tab'a Hira cikin so da k'aunar juna sai wajen 11 yabar D'akin da Haidar a hannunshi saboda yaron baida rigima Sosai Arman keson Haidar saboda kamannin cutie d'inshi da yayo " Hafsa ce ta shigo d'akin da farfesu a hannunta ta ce "Sis gashi Mama ta ce kisha karki sake tazo bakici ba" Dariya Kad'an Aira tayi ta ce '"Uhm my Mama kenan"Zaunawa Hafsat gefenta tana mata hira Bayan Aira ta cinye Kallon Hafsa tayi ta ce "Hafsa Dan Allah aroman wayarki zanyi kira banda layin nan k'asar" Mik'a mata wayar tayi number Aysha Ta dannawa kira Bayan ta d'auka "Aysha ta ce " Sis kina lfy dazu amma ke fad'amun Abunda Abba yayi maki wlh banji dadi ba yanzu kina ina?Goge hawayen da suka zubo mata Aira tayi ta ce "Ina Kaduna sis Na haihu ina gidan Mama Halima" Cikin farinciki aysha ta ce "Wow masha Allah me muka samu" Baby boy "ta fad'a kasa kasa" kai amma nayi farinciki wlh Allah ya raya insha Allah gobe Nida Ummy zamu taho har sai anyi suna tukwana bari nafadama honey Babban Albishir murmushi Aira tayi Bayan ta katse kiran number Mamy ta kira a lokacin Mamy sun gama fadansu da Abba tana d'aki Taga kiran Hafsa jin muryar Aira ya sanyata sauke ajiyar zuciya ta ce "Kina lfy Aira tunda kika tafi hankalina bai kwanta ba" Ajiyar zuciya Aira ta sauke ta ce "Ina lafiya Mamy ina Kaduna Ma gidan Mama Halima" Ajiyar zuciya Mamy ta sauke ta ce "Alhamdulilla gwara da kikaje Chan Dan Allah kici gaba da hakuri ki kwantar da hankalinki ba ason mai juna biyu na damuwa Kinga yanda kike " Murmushin K'arfin hali Aira tayi ta ce "Mamy ai na...sai kuma tayi shiru tanajin nauyin abunda zata fad'a " Dariya Hafsat tayi tare da Amsar wayar ta ce "Mamy so take ta ce maki ta haihu tun jiya mun samu baby boy" Cike da farinciki Mamy ta ce "Kai Alhmdllh amma nayi farinciki wlh Allah ya raya yanzu wannan cikin nata Har isa haihuwa nazata da saura " eh wlh Mamy Naji Mama tace ba watan Haihuwarta bane kawai tension ne ya kawo nakudar kuma ma tunda ta haihu bata da lafiya ciwon kai take kullum ikilamsiya taso ta sametama Allah ya kiyaye Amma yanzu da sauki "cikin tashin hankali Mamy ta ce " Subhanalla Oh ni Rahama Kenan Bata da lafiya bata wayar"Hararar hafsat Aira tayi ta ce "wa yace ki fad'a mata kinsan zata tashi hankalinta " A lokacin Mama ta shigo "Amsar wayar Aira tayi ganin yanda Mamy ta damu ta ce " Mamy lafiya ta fa qalau karya take"Sosai ta kwantarwa da Mamy hankali ganin yanda ta rude Hartana cewa kodai ta taho dak'yal ta samu hankalinta ya kwanta "Bayan sun gama wayar mik'awa Mama Halima wayar Aira tayi nan suka shiga gaisawa da Mamy Inda Mamy tayi mata Godiya Ta ce " bakomai ai Aira y'atake a Wajenta abunda zatayiwa Hafsat dole shi zata mata nan suka jajinta abunda ya faru a baya Mamy ta ce "Wai kina sanin kema bakisan abunda ke faruwa ba sai yanzu" Girgiza kai tayi ta ce "Wlhko banida masaniya komai Kawai sai kirana Hajiya Fatima tayi akan naje Asibiti sai jiya da tazo take fad'amun abunda ke faruwa na ce " ai da ta fad'amun tunda dai nima da Bayan goyon abun zan bada Allah dai ya kyauta ya kawo mana karshen AL amarin nan"Ameen Mamy ta fad'a Bayan sunyi bankwana Mama Halima ta Kali Aira ta. Ce "ki daina sanya damuwa a ranki Mamana jifa kin haihu keda zakiyi k'iba kiyi kyau amma ramewa kike " Kasa tayi da kanta ta ce "To Mama" Bayan fitar Mama kulli Aira ta kaiwa Hafsat ta kauce tana Dariya Hafsat ta ce "Wlh sis mamaki nake wai muna sa anni amma kece hada yara ukku" Dariya Aira tayi ta ce "me yafi son ranki kema ki fito mana da miji kawai musha biki" murmushi Hafsa tayi tana far da ido ta ce "Ah bakisan an sanya aure na ba ni da yaya omar" wara idanu Aira tayi ta ce "wanne yaya Umar din " Dariya tayi ta ce "naku mana " Sosai Aira tayi mamakin ashe soyayyar Hafsa da yaya omar kamar wasa ta zama gaske sosai kuma tayi farinciki da hakan suna cikin hirar ya kiraa Inda Hafsa daman ta fad'a masa komai a waya Aira Tabawa wayar sosai yayi farincikin jin muryar y'ar uwar tashi nan yayi mata barka tana jin kunya Daga karshe ta ce ya gaishe da Aunty Khady Dariya yayi ya ce "Abokiyar fad'ar taki zakice zataji insha Allah gobe zuwa jibi zanzo naga jikin naki kinji y'ar kanwata Allah ya raya mana boy" Dariya Aira tayi ta ce "To yaya Allah kawoka lfy tukwana ta mik'awa Hafsat wayar saida suka gama shan love d'insu tukwana suka yi bankwana Kallon Hafsa Aira tayi tana Dariya ta ce " zakici gidanku hannun basamudiyar Matar nan Dan wlh ta zauneki saikin hango k'abari ni zan baki labarinta"Sosai Hafsat ke Dariya hada rik'e ciki ta ce "yarinya kedai zatayiwa taganki haka kamar fara amma ni kam Saidai mu chashi juna sannan ma ina zan ganta muda ba gida d'aya zamu zaunaba ya ce " gida zai raba mana"Nan suka cigaba da Hira har bacci ya kwashesu . Washegari kamar yanda su Aysha suka fad'a ita da Ummy sukazo daga gidajen mazajensu Sosai Aira tayi farincikin ganin y'an uwan nata nan suka shiga d'aukar Haidar suna yabawa da kyan yaron Aysha ji take inama nata Har saida tayi hawaye a b'oye Mamy duk sanda taso tazo
Chapter 109 · 0% Book details