← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 127

Sashe 50

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 4 min read

ka yau d'innan saika sawwakemun Ka sakeni kawai " Shima Abba cike da masifa ya ce "Ni zaki dinga zagi Rahama Dan Kinga ina Miki lakwa lakwa harkina samu daman fad'amun magana mahaukaciya kawai wacce batasan abunda take ba" Sosai fad'a ya kaure tsakanin Mamy da Abba Wanda dak'yal Mama Halima da Yayar Mamy suka samu suka basu hakuri Dan Aunty Ramlat saida tayi kamar zata bugi Mamy tukwana ta samu Ta koma daki Nan suka bawa Abba hakuri saida suka kashe case d'innan ne ma suka samu damar zuwa wajen Aira Daren ranar Aira bacci k'auracewa idonta yayi ga wani masifaffan ciwon kai da ya addabeta sai wajen karfe ukku wahalallen bacci ya kwasheta ko Sallar asuba bata samu tayi ba sai wajen Tara ta tashi Shima Dan Ummy ce ta tayar da ita da tazo ba jimawa tana tashi salla Aira tayi tana gama salla ta koma ta kwanta ta Lula duniyar tunanin Arman shin yana wani hali ya yake ta jima tana tunani batasan lokacin da wasu zazzafan hawaye ke zubo mata ba Mama da Mama Halima da Aunty Ramlat su suka shiga shiryen shiryen tafiya da Aira Mamy ko lek'owa batai ba Dan bak'inciki Daman tun last week akaje akayi jere maza sukayi jeren sosai Abba ya kashewa Aira kud'i a kayan daki kayan kitchen da sauransu gara ko ba a magana duk wani Abu da uwa zatayi shi yayi bai bari Mamy tasai ko chokali ba Dan daman yasan bazata sayaba tunda ba son Auren take ba wajen k'arfe biyu na rana y'an uwan Alh Yusuf sukazo su shidda manyan mutane domin tafiya da Amarya Sosai aka musu tarba ta musamman Mama Halima ita taje ta sanya Aira tayi wanka ta had'a mata ruwan Turare Aira na kuka ta na wanka Bayan ta fito kallonta Mama Halima tayi tare da fito da wata tantsetsiyar farar laffaya ita da kanta Mama Halima ta shiryata ba make up ba komai amma tayi bala in kyau dukda damuwar da Aira ke ciki ana shiryata tana hawaye farfesun y'ay'an ciki Aunty Ramlat ta kawowa Aira ita da kanta ta dinga bata tana ci dak'yal Tana ci tana hawaye Wajen k'arfe Hud'u da wani Abu Su Mama Halima suka kama hannun Aira suka fito da ita idonta Rufe cikin laffaya Amma ganin an fita da Aira kuka ta fashe dashi a d'akin bata tab'a jin damuwar Auren nan ba sai yanzu da za a tafi da Aira sosai ta dinga risga kuka Itama Airar kuka take Kama hannunta sukayi sukayi da ita d'akin Mamy suna shiga Kafin su k'arasa Mamy ta ce "ku tafi da ita kawai na yafe mata karku k'ara tayarmun da hankali" Jin haka ya sanya Aira saurin fusgewa tare da rugawa taje ta Rungume Mamy ta fashe da wani irin kuka itama mamyn Rungumeta tayi tana kuka sosai suka shiga rera kuka hatta su Mama Halima saida suka sanyasu kuka Sun d’au minti goma suna kuka ganin abun nasu ba mai kyalewa bane ya sanya Mama Halima zuwa ta kama Aira Fusgewa Aira tayi cikin kuka ta ce "Mamy Mamy karki bari su tafi dani Mamy nasan ke kina sona " Itama sosai Mamy ke kuka Mama Halima ce ta ce "ki mata addu'a ki yafe mata ba kuka zaku zauna kunayiba" Cikin kuka Mamy ta ce "Na yafe mata duniya da Lahira Allah yayi miki Albarka Allah yayi miki Albarka Aira na yafe ma..kasa karasawa tayi sakamakon kukan da yazo mata kama Aira sukayi Dan tafiya da ita sosai Aira ke kuka tana ruk'o Mamy tana cewa" Mamy karsu tafi dani Mamy Mamy......Dak'yal suka samu suka Bambareta suka fito da ita Kai tsaya dakin Mama suka Nufa da ita itama Sosai sukasha kuka tukwana suka wuce da ita wajen Abba "Ganin irin kukan da Aira take karo na farko kenan da Abba yaji tausayin y'ar tashi tunda aka fara abun nan Danne zuciyarshi yayi ya ce " Allah yayi miki albarka Mama na na yafe miki duniya da lahira Allah ya bada zaman lafiya kutafi da ita kawai"Rik'e k'afar Abba Aira tayi dake kuka kamar zata mutu ta ce "Abba karka bari su tafi dani Dan Allah Abba" Rungumota Abba yayi tare da mik'ar da ita ya kalli su Mama halima ya ce Muje Abba da kanshi ya saka Aira mota dake kuka Kallonsu mama Halima yayi da yan uwan Alh Yusuf ya ce "muje na Muku rakiya Airport d'in Abba da kanshi ya tuk'a Aira har Airport......✍🏿
Chapter 50 · 0% Book details