Sashe 122
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kabir da Abubakar "Sadeq da Shuraim" suma sosai akasha bishsha a sunan nasu dangi ko ta ko ina sunxo hatta Iyayen Mummy dake Yola saida suka zo har Bappa Saidai Bappa tafiyar biyu ne ta kawoshi a wani gidan daban suka sauka haka akasha bikin suna lafiya aka gama lafiya cikin kwanciyar hankali Da dare Ayra duk ta gaji Nan itada da y'an uwanta suka shiga fiddo abubuwan da ta samu bata tab'a samun alkhairi irin na haihuwar yaran nan ba kodan an haifesune cikin danginsu ba kamar haihuwar twins ba Naila ce ta shigo tana mik'a Gado ta haye ta ce "Mom bacci zanyi" Harararta Aira tayi ta ce "A nan d'akin kike kwana daman ki tafi Wajen Mamy Inda Nihal take "Turo baki Naila tayi ta ce " Ni anan zan kwana bazan kwana Chan ba"Kama hab'a Ayra tayi ta ce "Wlh idan baki tashi kintafi ba Dukanki zanyi" Kara turo baki Naila tayi ta ce "Ai daman cutie tunda aka Haifi Haidar kika daina Sonmu Nida Nihal Yanzu ma Dan An haifi wadannan Yaran shine har zakice zaki dakeni bazan kwanta gadonki ba to Kema Da su Allah bazaku kwanta ba ta fad'a tana Mikewa tare da barin d'akin " Duk da ido suka bita Aysha Da Amma suka kwashe da Dariya Amma ta ce "Wlh waccen yarinyar Sak kece Ayra kafiyar tsiya gareta ga jaraba Harta linka ki " Aysha ma tace "Ai tunda na ganta nasan Ayra ce " Tsaki Ayra taja ta ce "Wlh nema take duk ta rainani ban isa na mata magana tabi ba saidaga baya tazo tana bada hakurin munafurci" Dariya Duk sukayi Ummy ta ce "Ai kedince kema ai haka kike kizo kina hawaye kina yarfe hannu Kiyi Hakuri Mamy bazan sake ba na tuba Allah bazan sake ba " ta fad'a tana kwaikwayan yanda take magana duk Dariya suka kwashe da ita "Suna cikin Hira Ayra juyawar da zatayi wajen twins Taga kunama kusa dasu " Innalillahi ta fad'a tare da saurin d'auke Sadeq ta sauka daga gadon da hannu d'aya ta d'auke shureim "Ta ce " Na shiga ukku kunama a d'akin nan"?duk Kallon wajen sukayi da mamaki Aysha ta ce "Kunama kuma meya kawo kunama d'akin nan " Mik'a mata Sadiq Ayra tayi tana hak'i ta ce "Wlh nima bansaniba " Ummy da mamaki ta ce "Ayra twins na kwaffi daman ?Girgiza kai Ayra tayi ta ce " Nidai ban tab'a ga sunyi ba wlh "Chab Aiko wlh Naila ce Zata fito da kunamar nan kin manta tace kuma bazaku kwanta gadon ba" dafe k'irji Ayra tayi ta ce "Na bani Ni Ayra Kuma fa basu tabayiba wlh" Aysha ce ta ce "Kila k'inyi ne kawai suke " suna cikin hirar suka nemu kunamar suka rasa Dak'yal suka koma gadon suka zazzauna da anjima anjima saita k'ara fitowa ba arziki Duka suka bar d'akin sai a palour suka kwana Aira dukta tsorace washegari koda Naila ta fito ta gansu a palour nan ta dinga Musu Dariya Harararta Ayra tayi tare da Jan tsaki ta ce "Yau d'innan zaku bar gidan nan wlh tunda har kika iya mugunta babu ruwana dake dagayau Nihal ce kad'ai y'ata" Jin hakan ya sanya Naila fashewa da kuka tare da rugawa ta fad'a jikin Ayra ta ce "Kiyi hakuri mom bazan sake ba Dan Allah karkice Nihal ce kad'ai y'arki bazan sake ba " Shafa bayanta ayra tayi ta ce "To nahakura amma kika sake me.zan maki?Ki yankani Na yarda Allah mom" Dariya Ayra tayi ta ce "To shikenan na hakura my prince's jeki Kuyi break fast " Tsalle Naila tayi ta ce "Thnks cutie d'in hero " ta fad'a tana wucewa dinning Duk Dariya sukayi Ummy ta ce "Wlh kun b'ata yarannan Wai wani cutie din hero Suma sun shaida dai iyayensu y'an soyayya ne " Dariya Ayra tayi nan sukaci gaba da Hira da y'an uwan nata cikin raha da annashuwa Ranar akayi soye Inda wasu daga cikin y'an uwa suka tafi Aunty Maryam da Mama Halima ne a bakin kawai basu tafi ba sai gwagwo da Baffa da Bayan isha I Bappa ya shigo gidan Palourn Abba aka saukesu Inda aka Girmamasu sosai aka cika musu da abun arziki Inda Ayra Bayan taje ta Gaishesu ta Aje musu twins Bappa ne ya kira Mummy da Daddy da Arman akan suzo su sameshi a gidan Abba yanzunnan sosai sukayi mamakin me zasuyi Daddy ko dak'yal Mummy ta samu ya yarda suka tafi Dan acewarshi baiga abunda zaiyi gidan d'an uwan nashi ba karfe takwas da rabi Duka palourn ya cika da mutane Tundaga kan Daddy Abba,Mama Halima,Mamy,Mummy,Mama,Arman,Aira ,Aunty Maryam,Yaya omar,Aysha,Ummy,Amma,Haidar ,Hafsat,Twins,Little Haidar,dake hannun Hafsat,Hatta Amer dukansu Iyalan Saida Bappa ya had'a Bayan an bud'e taro da Addu'a ya far'a da cewa "Ba komai yasa Muka hadu a wannan wajen ba saidan sasunci a matsayina na babba kuma Wanda nake ganin Dukanku nan zan iya yin iko da ku Kallon Abba yayi ya ce " Da farko zamu fara baka hakuri a bisa Auren da muka d'aurawa y'arka bada masaniyarka ba munyi hakane badan komai ba saidan Kaucewa wacce matsala shi Aure da haihuwa da kake gani na Allah ne ba a fiya zakewa a Lamarin Aure ba saboda rabo Har kashewa yake yanzu duba ka ga Cikin k'ank'anin lokaci da auren zuri'ar da suka fara Tarawa yara har biyar Wanda da koda Aure ko babu sai an haifesu yanzu da ace a waje suka haifi yaran nan Dan Allah ya zakaji a cikin ranka zakayi tsantsar nadama to zandai gajarta maganar Yanzu dai muna neman yafiyarka Akan kuskuren da mukayi maka"Cikin girmamawa Abba ga d'ago ya ce 'Bakuyimun komai ba Bappa nine ma ya kamata na nemu yafiyarku sannan nayi muku Godiya akan Abun nan da kukayi Tabbas na sake da Lamarin ubangiji Nasan yaran nan da a yanda na hana Su auri junansu tofa yaran nan da a waje za a haife su kaga ko ai ni ya kamata nayi muku Godiya Allah ya saka da alkhairi ya k'ara girma banida da bakin da zan gode muku Saidai nayi muku fatan gamawa da duniya lafiya"Amen Baffa ya fad'a sosai yaji dadi maganar da Abba ya fad'a Bayan nan ya d'ora da cewa "Sai magana ta gaba kuma da itace ginshikin haduwar mu a wannan wajen magana ce ta tsakaninku kai da d'an uwanka ya fad'a yana nuna Daddy a Gaskiya banji dadi ba Kuma kowama dake karkashinku na tabbata basajin dad'in irin wannnan D'aurarriyar gabar da kuka daura akan Abunda baikai ya kawoba Maganar ce dai ta farko zata dawo Shi aure da haihuwa da kuka gani Abu ne mai wuyar AL amari tun ran Gina ran Zane Kowace mace a duniya da kuke gani Allah ya Riga ya Zab'a mata mijin da zata aura Wanda alk'awarin Allah baya tashi kowace mace da kake gani da mijinta wani bai isa ya auri Matar wani ba Auren Rahama da Abubakar yayi dukda ance ana barin halak kodan kunya tofa ku sani shi silar tashi haduwar da Matar tasa ne tazo ta silar d'an uwanshi ko da Kabir baiga Rahama ya ce yana so ba dole Abubakar Zai Aure ta Komai Yana da Sila ne su nasu silar ne yazo da haka ta dalilin d'an uwansa Wanda abunda ya kamata ayi shine tawakkali da Allah to duk bakuyi haka ba kai Kabir saika dauri gaba da d'an uwanka Wanda hakan bai kamata ba har yakai ga kunfito takara to yanzu dai bazamu tsaya tashe tashe ba Duka abunda ya wuce ya Riga ya wuce ya kamata kuyiwa kanku fad'a tun kafin duniya tayi muku Rayuwar Duka nawace Duka cikinmu damu da ku babu Wanda zai maimaita shekarunshi na baya an riga an cinyesu tsufa na kama ku mutuwa na kusantomu ta na iya riskarkar kowannenmu a kowani lokaci yanzu ko mutuwar Inna bata isheku ishara ba ta mutu Da bakincikin gabar da kuke Sannan koda Mahaifanku dake k'asa na tabbata suna bak'inciki da wannan AL amarin Har koda yaushe burin wannan baiwar Allah bai wuce taga kun hade kanku ba kun shirya Amma kuka kasa cika mata wannan burin har saida ta bar duniya wannan kadai bai isheku ishara ba "Nidai ina mai baku shawara ne akan ku shirya ku sasinta junanku Dukanku nan kuna da Ilimi kuma Duka cikinku kowa yasan girman laifin da kuke aikatawa Yanke zumunci ba Abu bane mai wasa Wanda Allah s w a da kansa ya ce Zumunci rik'e take da al'arshi banda girman laifin yanke zumunci Kuma kuka had'a da laifin gaba Wanda Annabi MUHAMMAD s a w ya ce " Daga kwana Ukku Sallar mutum bata karbuwa wannan wace irin rayuwa ce kuke wacce babu Wanda ya isa ya fad'a muku Gaskiya mecece duniyar bare abunda ke cikinta Wlh duk Wanda ya d'auki duniya ma wani Abu ya maza ya sauke Dan Rayuwar nan da muke cikinta ba komai bace Dole zamu tafi mu barta ko muna so ko bama so kuma mutuwar nan dai da muka sani ba sallama take ba baka ta tabbacin zaka ma iya k'ara second d'aya a duniya Me zaisa duniya ta dinga ribatarmu Wanda duk abunda kake tak'ama dashi kudi,mulki,sarauta,izza,tak'ama,muk'ami,girman kai,dukansu a nan Inda kazo haka zaka tafi ka barsu kai kad'ai za a sanyaka k'abarinka da ga kai sai halinka sai abunda ka aikata alkhairi ko sab'anin haka Itafa duniyar nan da kuke gani makaranta ce In maka misali da Kamar matafiya ne muna cikin tafiya Muka tsaya yada zango mu huta Kafin wuce to kamar haka ne Mezaisa mu shagaltu da duniya Gidan aro Duniyar da ba komai bace Muyi kokarin mu Gina lahirarmu tun anan kafin lokaci ya kure mana Dan duk Wanda ya shagaltu da duniya to wlh ya Riga da ya gama tab'ewa a lahira lahira itace Matabbata Inda rayuwar ta Chan ce dindindin Har Abadan Abadan muyi kokari wajen mun Zage damtse mu gyara lahirarmu tun Anan har yanzu lokaci bai k'ure muku ba Tunda kuke da rai kuma kuke numfashi tofa kuna da ikon da Zaku daidaita kuma ku nemi Allah yafiya a take ya yafe muku,Nidai nasiha ce nake muku gami da bada Shawara sauran kuma ya rage naku "Ba Daddy da Abba Hatta kowa dake wajen saida yayi