← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 127

Sashe 41

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 3 min read

bazu duk hotel d'in da suka sani sannan Abba ya sa Mama Halima ta tura musu hoton Arman. Aira itace bata tashi ba sai karfe d'aya na rana sosai taji ta wartsake bayan tayi wanka Salla tayi kayan jikinta ta mayar zaunawa tayi bakin Gado tayi tagumi Ta na zaune taji shigowar Arman da harta tsorata tana ganin shine Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta ce " ina yini Yaya "Murmushi yayi ya ce " Alhmdllh cutie yau munsha bacci ko"murmushi tayi ta ce "Wlhko banzaci munkai haka ba" Ai nima banjima da tashi ba bari naje na Samo maki kayan da zaki sauya kafin mu tafi na so ace sauko mukayi "rik'e hannunshi tayi ta ce " Yaya zan mayar da na jikina plx kawai mu tafi banson a samu matsala nasan duk Inda y'an gidanmu suke nemana ake "a a ki bari na samo maki wasu kayan cutie babu wata matsalar da za a samu tunda kina nan ba tare zamu ba Kuma ma mota ta tinted ce bamai ganinmu daga Chan saina taho maki da abinci nasan yunwa kikeji ba Dan Aira ta so ba ta bar Arman ya tafi Arman yana fitowa daga farfajiyar hotel d'in kai tsaye motarshi ya nufa ya tada Y'an sanda ko suna ganinshi suka ganeshi Dan tunda aka turo musu hoton daman sunsanshi d'an Excellency ne Abba suka kira sukace " ranka ya dad'e munyi nasarar ganin shi Mujahid d'in yanzu a harabar Grand central hotel amma shi kad'ai muka gani yanzu haka ya tada mota ya bar hotel din amma ga alamu kamar bazaiyi nisa ba "" Abba tashi yayi daga zaunen da yake ya ce "Karku saki ya gudu Kuyi yanda kukayi kuka tsayar dashi suna Tare da ita Tabbas gani nan zuwa " to ranka ya dad'e kayi Sauri Dan Gaskiya bamu da power Kamashi D'an governor guda zamu iya ta aikinmu amma kai kazo "Suna cikin wayar suka ga dawowar Arman " ranka ya dad'e gama shinan ya dawo ka yo Sauri"Cikin hanzari Abba ya d'auko mota Dan zuwa Inda suke ya ce "kusan duk yanda zakuyi ku tsaidasu Karku bari su gudu kafin nazo" Angama y'an sanda suka Fad'a suna ganin Arman ya fito daga motar ya shiga ciki suka maza sukaje sukasa k'usa suka sace tayar motar Arman ko baisan wainar da ake toyawa ba yana shiga ciki ya samu Aira Inda ya barta "Sorry dia ya fad'a yana zama " murmushi tayi ta ce "Amma kayi Sauri yaya " murmushi yayi tare da fito da wata had'ad'd'iyar zoben gold ya matuk'ar tsada mai shegen kyau kama hannun Aira yayi tare da saka mata zoben yace ga zoben alk'awari murmushi Aira tayi tare da fito da zoben dake hannunta azurfartace tun tana Yarinya take jikinta dak'yal ta cirota itama k'aramar yatsar hannunshi ta kama tare da saka mashi tace "nima ga tawa ta alk'awarin" murmushi suka sakarwa juna tare Sosai Aira taci abinci saboda yanzu Hankalinta ya d'an fara kwanciya Arman Shima ya samu yaci Waje ya bata ya ce ta sauya kayan yana fita Aira cikin Sauri ta cire na jiya ta sanya doguwar rigar d'aya kawo mata bak'a tana gama sawa ta d'ora hijab d'inta pink ta jiya yana shigowa kallonta yayi yace"Koda yaushe Kyanki karuwa yake cutie "murmushi tayi ta ce " kamar kai kenan"A nan suka bar kayanta na jiya hannunsu mak'ale Dana juna suka fito Bayan Yaje ya saki d'akunan da suka kama Aira tunda suka fito kanta yake a k'asa saboda ganin yanda ake kallonsu ga kuma gabanta dake fad'uwa Suna isa Inda Arman yayi parking sosai yayi mamakin Ganin tayoyinshi Duka a sace cike da mamaki yace "yanzu fa lafiya qalau na bar motar nan cutie " Cike da tsoro Aira tace "ko wasu suka sacemaka su Yaya nidai tsoro nakeji muyi Sauri mubar wajen nan Tab'i suka jiyo daga bayansu raf RAF Raf saurin Juyawa sukayi a tare Wara idanu Aira tayi cike da firgice ganin...........✍🏿
Chapter 41 · 0% Book details