Sashe 106
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read
....Ni ce Baba Su Mamy na ciki"?Eh suna ciki Alhaji dai naga ya fita"Ajiyar zuciya Aira ta sauke jin Abba bayanan cikin Sauri ta shiga cikin gidan twins na biye da Ita "sosai take kallon gidansu tana jin wani dadi gidan da rabonta dashi shekara kusan hud'u A bud'e ta tarar da Palourn Cikin fargaba da shiga twins na biye da Ita suna surutansu Tana tura kofar amma da Mama Sai Haidar ta tarar a palourn ja tayi ta tsaya suma duk Kallon mamaki suke binta dasu amma Ce tayi k'arfin halin cewa " Sis kece da gaske ko gizau ne nake gani"Tuni hawaye suka wanke fuskar Aira gyada mata kai tayi "ai da gudu ta rugo ta Rungumeta Itama Rungumeta tayi tana jin kewar y'ar uwar tata sun jima suna kuka kafin suyi shiru wara idanu amma tayi ganin twins Bayan Aira da mamaki ta isa garesu tare da dukursawa ta ce "naila Nihal kune nake gani gabana kodai mafarki nake" Dariya Aira tayi ta ce "sunedai gabanki sis" da mamaki ta ce "me kike nufi Aira me ya hadaki da Yaran nan" Dariya tayi ta ce "Ai yarankine sis" Mama ko duk mamaki ya gama cika ta ga mamakinta na ganin Aira da wani cikin cewa tayi ta yi"mufa in sanyamu a duhu Aira Yaran nan dai ko ba a fad'a ba daka gansu kasan na Arman ne yaushe kika haihu bansaniba Bayan baki da Aure"Goge hawayenta Aira tayi tare da cewa "Mama ina yini" Haidar ne Shima da ya gama mamakinshi ya rugo suka Rungume juna yana hawaye ya ce "Yaya Aira me yasa kika tafi kika bar gida tsawon wannan lokaci" kama hannunshi Aira tayi ta na Goge hawayenta ta ce "Nima ba haka naso ba bro k'addarace ta zabamun haka Ina Mamy ta fad'a tana hawaye" D'akinta ya nuna mata Ai cikin Sauri Hartana hadawa da gudu Tayi d'akin tana turawa ta samu Mamy bakin Gado da gudu Aira ta Ruga tare da Fad'awa kan Mamy ta Rungumeta ta fashe da kuka Mamy da jin mutum kawai tayi a kanta ana kuka sosai tayi mamaki"Juyowa tayi ta duba fuskar aira taga ita d'ince wara idanu ta yi ta ce "Aira tace nake gani ko gizau" Tana kuka tana hawaye ta ce "Mummy Airankice Mamy Dan Allah ki yafemun " ta k'arasa fad'a cikin wani irin kuka "Itama Mamy kuka ta sa tare da Rungume y'artata tanajin soyayyarta har cikin ranta ta kasa koda magana Twins ne da suka shigo biyo mamansu Sakin rungumar Mummy tayi tare da dafa kafadar Aira Kare mata kallo Tayi Tare da Kallon cikin jikinta gabanta na tsananta fad'uwa ta ce " Aira ciki?meya hadaki da ciki Bayan ba Aure gareki ba"hawaye nabin k'umcinta Aira tayi k'asa da kanta twins ne suka zo suka D'are kanta Nihal ta ce "Cutie mom ina Mom en taki take"Nuna musu mamy tayi tana Hawaye tare da K'asa da kanta " Kallon mamy sukayi a tare Itama mamyn kallonsu take ta kasa koda magana Da zaka duba yanda zuciyarta Take tofa da kila tana Daf da fashewa saboda fargabar yaran nan nan da Cikin nan Kardai a waje ta samesu "cikin k'arfin hali ta ce " Aira ina kika samu yara da ciki keda ba Aure gareki ba fad'amun abunda ke faruwa kinsanyani cikin duhu"Goge hawayenta Aira tayi tare da kama hannun Mamy tana kuka ta ce "Mamy wlh duk abunda Alh Madugu ya fad'a muku wlh sharrine suka mana bantaba zina ba......Duka ta bawa Mamy labarin komai bata boye mata ba har zuwa Aurensu da iyayen Mummy suka hada har zuwa yaran da suka Haifa. Koda ta gama bata labarin Ajiyar zuciya Mamy ta sauke ta ce " Amma Gaskiya Hajiya Fatima ta cika uwa ta gari ba ku kadai ta taimaka ba ni kaina ta taimakeni Allah ya saka mata da gidan Aljanna yanzu Dan Allah ina da za a akai rabon yaran nan da Saidai ku haifesu a waje Allah na gode Maka da komai yazo yanda banyi tunanin ba sannan ta kalli twins tana fara a ta ce "Ina takwarar tawa da takeson Gani na " Nihal cikin Sauri ta Ruga tare da Rungume Mamy itama mamyn Rungumeta tayi ta ce "oyoyo takwara ta yau dai Gaki ga takwararki ko?gyada mata kai Nihal tayi Ta na mata Dariya tare da shafa Fuskarta " Naila ce ganin Mamy batayi mata magana ba ta fashe da kuka tare da Fara didiira kafa "duk kallonta suka tsayayi Aira ta ce " me aka miki Naila "Tana kuka ta nuna Mamy ta ce " ba mom enki bace ta kyaleni ta dauki takwalalta Nima ki kaini wajen mom tunda itace takwala ta kuma bazan kala zuwa nanba tunda ni bata so na"Dariya mamy tayi tare da janyota ta Rungumeta ta ce "Sorrry Mamy tayi laifi ayi hakuri ina sonki sosai kema kinji" Lokaci guda Naila ta fara Dariya tare da Fara tsalle jikin Mamy ta ce "I love you so much mom En cutie" Dariya mamy tayi tanajin soyayyar yaran a ranta ta ce "I love you too yaran kirki" Nihal ko Lafewa tayi jikin Mamy kamar daman ta Santa tana Tsotsar yatsa kallon Aira Mamy tayi ta ce "Karkiga yanda Halima ta rude kullum bata da zance sai Oum twins Da twins ashe dai yarantanema Akwai lokacin da ta nunamun hotonsu har ina fad'a ina cewa baki da magaya Aira me ya kaiki d'ora yaranki a media " Murmushi tayi ta ce "Mamy ai yanzu na daina" Ai tun lokacin da kika daina karkiga yanda ta damu lafiya dai ko"Wlhko y'an shan jinine suka kamasu twins nan ta bata labarin abunda ya faru"Subhanalla Mamy ta fad'a ta Ce "Aidaman nasan anrina Allah ya kiyaye gaba sannan ki dinga sanya musu hula in zaku fita jifa gashinsu waje tubarakalla sunyo gashinki Sai a cinye miki yara a banza " murmushi kawai Aira tayi tana wasa da yatsun hannunta Amer ne ya shigo Bayan dawowarshi daga Tahfex Wara idanu Aira tayi ganinshi da mamaki ta kalli Mamy ta ce "Mamy amer ne ya girma haka" Dariya Mamy tayi Dan yau cikin farinciki ta ke ta ce "Wlhko ai yaushe rabonki dashi" Amer ko kallon mamaki yakewa Aira Dan baisan taba wajen Mamy ya nufa Tare da Kallon twins dake cinyarta Dariya yayi musu Suma suka mayar masa kallon Mamy yayi ya ce "Mamy ina kika samo mana yara masu kyau" Dariya Mamy tayi tare da nuna masa Aira ta ce "yaranka ne auta kaga mamansu ka ganeta?Kallon Aira yayi da itama shi take kallo Ya girgiza kai ya ce " a a a Mamy bansan taba amma naga tana kama da Abba kuma ina ganin hotonta"to yayarkace itama Nina haifeta wannan kuma yarantane aidai kasan Ayra a baki ko?wara idanu yayi ya ce "Lah Mamy Aunty Ayra ce Sannan ya Ruga ya Rungumeta Itama Rungumeshi tayi ta ce " Ah lalle autan Mamy ya girma "Dariya yayi Inda yaje Yayi tayiwa Su twins wasa suna Dariya sunk'i sauka daga kan Mamy sai liliyarta suke Haidar ne ya shigo shida amma tare da plate a hannunsu Amma tazo ta zauna jikin Aira tana kallonta ta ce " sis oum twins ga abincinan kici ga ya Ummy na kirata hada saurinta ta ce tana hanya Ashe dai surprised Dina da akace za ai da gaske ne"Dariya Aira tayi ta ce "Ai cewa nayi a bazata zanyi maki yaudai gaki ga twins dinki"mikawa twins hannu Amma tayi tana musu murmushi Naila ce ta Ruga Wajenta Nihal ko tayi luf jikin takwararta daman ita uwar son jiki ce fita amma da Naila sukayi Kallon Haida Ayra tayi da yayi tsaye yana Danna waya ta ce "Hmmm su Haidar manya tunda nazo sai daddauremun kake" Mamy ce cikin fad'a ta ce "Rabu dashi uban bak'in hali kamaga y'ar uwarka ko farincikin ganinta bakayi ni wuce ka bani waje kazo kayima mutane tsaye kana Danna waya" Murmushi Haidar yayi ya ce "Sorry Mamy sannan ya kalli Aira ya ce " Tunfa a palour muka gaisa sis "Amsar wayarsa Aira tayi ta ce " Kayi waya kenan bari na d'auki number ka D'aukar number tayi save Shidai Haidar mamaki yake Inda Aira ta samu yara Suna haka Ummy ta shigo da gudu Suka Rungume juna itada Aira sai murnar ganin juna suke dukda abokiyar fadantace itama saida tayi mamakin jin twins yaran Aira ne Palour Aira ta fito Nan Mamy tayiwa Su Mama bayanin da Aira tayi musu sosai suka jinjina Abun kuma sukayi farinciki da abunda akayi tunani bashi bane Mama ma sosai tayi fad'a ta ce "da yanzu ina za akai rabon yaran nan Haidar ma sai yanzu yaji sanyi harma ya d'auki twins Dan dazun dukda yayi farincikin ganinta amma Yaji haushin Ace yayartashi tayi abunda ake zargi ashe ba haka ba nan aira ta tambaya ina inna akace mata batanan tayi tafiya kauye ziyarar yan uwa sosai aira taso ta hadu da inna Suna palour ana jajinta abunda ya faru Amma na bawa twins abinci Aira ce ta ce “sis wai Ina makarantar kin gama?Murmushi amma tayi ta ce “two months kenan da kammala degree dina sai jiran result kingani abunda nake fada maki yanzu fa bakinki sec sis Da yanzu kema kingama degree dinki “Dariya aira tayi ta ce “Ni kinga degree dina nan “ta fada tana nuna Twins duk Dariya akai Mamy tace “kujimun marar kunya’duk Dariya akai sosai aira ta tsinci kanta cikin farinciki ganinta cikin yan uwanta da mahaifiyarta ana wasa ana dariya ana haka Suka ji sallamar Abba sosai gaban Aira ya fad'i Ganin shigowar Abba Mikewa tayi a matuk'ar firgice Shima a mamaki Abba yake kallonta cikin tsananin b'acin rai ya nunata da yatsa ya ce Uban me ya kawo wannan abar gida na da izininwa " Tuni Aira ta fara hawaye Bayan Mamy ta boye ta ce "Dan girman Allah Abba kayi hakuri ka yafemun na tuba " Mama ce ta mik'e ta ce "Kayi hakuri Alh ka sauraremu’’ Tsawa ya daka mata Tare da nuna Aira da yatsa ya ce "Minti d'aya na baki ki fitarmun daga gida bana k'aunar ganin bak'ar Fuskarnan taki a cikin gidana " Sosai Aira take kuka ta ce "Dan girman Allah kayi hakuri Abba Mamy