← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 127

Sashe 73

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 5 min read

Abba na zaune a palour da misalin karfe Tara na dare yana kallon labaran N T A News Kira ya shigo Wayarshi duba mai kiran yayi yaga Alhaji Madugu ne Amsawa yayi tare da Kara wayar a kunnenshi ya ce "Assalamu alaikum" Wa alaikumussalam Alhaji Madugu ya amsa daga ganin kasan yana cikin fushi cikin Fushi ya fara magana "A Gaskiya Alh bukar ka cuceni ka zalince ni daman Kasan y'arka y’ar iskace baka bata tarbiya ba dan tayi cikin shege shine ka lik'amun ita to kasani asirinku ya tonu dan asibiti mukaje dr ya tabbatar mana da tana dauke da juna biyu na wata hudu Bayan aurenmu da ita wata ukku da kwanaki ne hasalima ni wani abu baitab’a shiga tsakanin ni da ita ba sannan nakirakane Dan na fad'a maka a halin yanzu y'arka bata hannuna na saketa tabi Tsohon Saurayinta da ya yaudare ni kusan wata guda yake Aiki a karkashina ashe shirine sukayi da ita Bayan mun kamasu dumu dumu dazu da safe na saketa saki Ukku Ta bishi sun tafi Dan karma ka bincika y'arka wajena bata hannuna tabi tsinannan saurayin da yayi mata Cikin da bakinshi ya fadamun cikinshine daman sone kukayi ku likamun cikin shege shiyasa ka lakabamun ita sannan kuma ka sani duk abunda na kashe tundaga neman Aurenta har zuwa yanzu saika biyani Dan bazanyi asara a banza ba "Tunda Alhaji Yusuf ya fara maganar Daddy Ya shiga tsananin tashin hankali har yakai karshe " Innalillahi wa inna ilaihiraji'un ya fad'a wayar tuni ta sulale a hannunshi A tsayen da yake ya dire kan kujera tare da dafe saitin Zuciyarshi a rarrabe ya ce "Ci ki Aira " Ai tuni Yaji hankalinshi ya fara gushewa Ya fara ganin jiri Mama ce da tafito taga yanayin da yake cikin cikin tsananin tashin hankali Ta nufe wajenshi tare da cewa "Alhaji lafiya? Me ya faru " Wayarshi ya nuna mata a rarrabe ya ce "Ki ki ra mun Dr cikin Sauri Mama ta dauki wayar tare da Nemo number Dr bashir ta kira ring Ukku ya d'aga cikin tsananin damuwa ta ce " Dr kazo gidanmu yanzu ka taho tare da kayan aiki ina tunanin jinin Alhaji ne ya hau sosai "Tana kashewa ta kwalawa Mamy kira " Rahama ki fito Alhaji ba lafiya!Cikin tsananin tashin hankali Mamy ta fito tare da nufar wajen ta ce "Subhanallahi me ya sameshi yanzu fa muka rabu dashi lafiya" wlh ko nima haka yanzu na sameshi"Su amma da su Haidar ma duk sun fito Cikin tashin hankali sunyi jugum jugum a haka Dr ya shigo cikin Sauri ya nufi Inda Abba yake tare da Fara Dubashi Abun awon DP ya fara mashi yana dubawa yaga jininshi yahau sosai irin yanda yake bada matsala cikin Sauri ya sanya mishi semomitre a harshe tare da saurin had'a allura Yayi mashi su mama dr ya Kalla yace su taimaka a kaishi daki Mama da Mamy suka taimakamai aka kwantar dashi a kan gadon Mama Wanda tuni bacci ya daukeshi Dan allurar ta bacci ce Daman kallonsu Dr yayi ya ce "wani Abu aka fad'amai kafin ya fara haka Dan kadan ya hana ya samu heart attack" Subhanalla heart attack kuma Dr Gaskiya nidai bansan anyi mashi wani ba Saidai ko Yaya idan ta sani "Mamy ta fad'a tana kallon Mama " itama cewa tayi bata saniba magunguna Dr ya rubuta musu akan a sayo daya tashi ya cigaba da shansu sannan su barshi shi daya ya huta a dakin har zuwa sanda zai tashi kar a tasheshi jinin zai sauka Daman yasan Abba yana da hawan jini amma irin na manyanta ka ne bamai matsala ba magani kawai yakesha "Godiya su Mamy sukayiwa Dr Bayan ya tafi suma Duka barin d'akin sukayi Dan kar ayi hayaniya kowannensu ya shiga kogin tunanin meye ya sanya jinin Abba hawa a take.
Washegari sai wajen goma na safe Abba ya farka jinin nashi ya sauka Saida Dan Rashin jin dad'i da bayayi a lokacin Duka iyalannashi na dakin Sannu kawai suke jera mishi da kanshi ya Mike " Kallon Mama yayi ya ce "Banyi asuba ba ko?Eh Alhaji bakaiba Dr yace a barka ka tashi da kanka shiyasa" Cewar Mama "Aida kun tasheni ya fad'a tare da shiga toilet ya dauro alwala yaxo ya gabatar da salla Mamy ce tayi k'arfin halin cewa Ya jikin" Da sauki ya bata Amsa Kallon Mama yayi ya ce "Ki kira su Aisha da Ummy Dukanku karfe sha biyu ku sameni a palour na yana gama fad'ar haka Ya fice daga d'akin ya koma part d'inshi sosai duk sukayi sanyi Basusan me yake faruwa ba kamar yanda Abba ya fad'a haka Mama ta kirkira su Aysha karfe sha biyu tayiwa kowa na gidan a Babban palourn Abba har Inna saida yasa aka kira idan aka cire yaya Umar da Maryam sai Aira Bayan kowa ya zauna Aysha Abba ya Kalla ya ce " Kiramun Maryam a waya kisa hads free "Sannan ya kalli Ummy ya ce " Ke kuma kiramun Umar Duka inason kowa ya saurari abunda zan fad'a "hakanko akayi Duka aka kirasu Gyaran murya Abba yayi ya ce " To ba bakomai yasa na taraku anan ba Saidai In kafa hujja sannan ku shaida ku sani a gaban kowa daga yau Ni Abubakar Umar na cire Hajara a cikin jerin y'ay'an da na Haifa daga yau babu ni babu ita Sannan duk d'an Dana Haifa Shima na rabashi da ita babu ku babu ita Na yanke zumuncin dake tsakaninku ko a boye wani yayi mu’amula da ita ban yafe mashi ba daga yau kar a k'ara alak'antata da y'ar da na Haifa na yafeta a cikin jerin y'ay'an da na haifa ...........✍🏿

*Jumaat khareem*
*ina yiwa yan uwa musulmai murnar nuna mana wannan rana ta Arafa mai Cike da albarkoki Allah yasa muna daga cikin masu dacewar wannan rana ya yafe mana kura kuranmu ya amsa mana adduoin mu da ibadinmu Allah bamu ikon zuwa wannan k’asa mai tsarki don muma mu sauke farali Ameen ya Allah*

*zamu shiga hutun sallah koda na kwana biyu ne kuyi hakuri kunsan hidimar sallah bazata bari nasamu damar typing ba Ayi salla lfy sannan kowa ta ajemun nama na yawan nama yawan typing*😂

_*Miss Hajo ce*_🤙🏿🤙🏿
[7/11, 12:53] Hajo hajo: 🅿️............*89&90*
Chapter 73 · 0% Book details