← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 127

Sashe 46

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

......Kai tsaye asibitin doctor aminu kano suka nufa da ita suna isa emergency aka nufa da ita cikin k'ank'anin lokaci manyan likitoci suka duk'ufa a kanta Dan ceto rayuwarta Mama Halima waje suka tsaitsaye sai safa da marwa suke Mama Halima ce ta Hango Mummy tare da yayan nata cikin Sauri ta nufi wajensu tace "Yaya lafiya me ya kawoku asibitin nan" Cikin tashin hankali Daddy yace Arman ne ba lafiya yake aman jini yanzu haka yana emergency bamusan halin da yake ciki ba "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un " Mama Halima ta fad'a tana hawaye ta ce "Allah ya bashi lafiya Kunga dai irin halin da kuka jefa y'ay'anku sannan ta kalli Mummy dake zaune tana kuka ta ce " Sannu Aunty Allah bashi lafiya"Goge hawayenta Mummy tayi tayi ta ce "Amen Halima wa kuka kawo" Wlh Aira ce muka kawo Tasha fiya fiya zata kashe kanta koma ta mutu badai mu saniba sundai shiga ciki da ita "Cikin tashin hankali Mummy ta mik'e ta ce "Innalillahi wa inna ilaihiraji'un kai mudai muna ganin kaddara sannan ta kalli Daddy tace hankalinku ya kwanta shikenan in suka mutu saiku zubda ruwa a k'asa kusha kun cucemu Alh d'ana d'aya tilo shikenan Kunmun sanadin mutuwarshi ga ta Chan itama Tasha fiya fiya duk sabodaku hankalinku saiya kwanta idan suka bar muku duniyar" ta k'arasa fad'a cikin kuka cikin b'aci rai Daddy yace "Ni da kike maganar nima ba shi kad'ai bane d'an nawa ko ina da wani d'an Bayanshi " Ai zaka iya k'ara Aure ka haifi wasu y'ay'an Nifa daga kanshi na gama haihuwa shi kadai garan kun kasheshi ai"Kallon Aunty Halima Daddy yayi ya ce"An d'aura Auren ne?"tana hawaye tace "Eh an d'aura labarin d'aurin Auren ne ma ya sanya ta yunkurin kashe kan nata" dafe goshinshi Daddy yayi sannan ya kalli Mummy yace "kinji an d'aura da ba a daura ba da sainaje musan yanda za ayi" Cikin kuka Mummy tace "ba tun kafin a d'aura ba nace kaje ka bashi hakuri ku bari su Auri juna kaki" kan Daddy gaba d'aya ya kulle ga Rashin lafiyar Arman da basusan halin da yake cikiba ga Mummy itama tana neman chazamai kai Rungumeta yayi tare da Fara Lallashinta yace "kiyi shiru bansan wannan kukan naki addua zamuyi ta musu Allah basu lafiya sannan zanyi magana da mahaifin nata tunda haka kike so kidaina kukan amma" Goge hawayenta Mummy tayi tare da gyada mashi kai kamar wata yarinya. Abba bayan ya dawo ya samu wannan labarin Tashin hankali Alh yusuf kawai ya fadawa halin da ake ciki cikin kankanin lokaci suka sallami mutanen da suka gayyata basu yarda kowa yaji wannan labarinba sosai alh yusuf ya shiga tashin hankali amaryarshi guda na asibiti halin mutuwa ko rayuwa Abba tashin hankali biyu ga na mamy dake sume a d'aki ruwa ya d'auko tare da yayyafa mata saida ya yayyafa mata sau Ukku tukwana ta fara sauke ajiyar zuciya Shima Abba Ajiyar zuciya ya sauke Dan sosai yakeson Mamy da kaunarta baisan wani Abu ya sameta Mamy na tashi Ganin Abba ya sanyata Fara kuka tace "Ka tafi banson ganin ka Alhaji ka kashemun y'a hankalin ya kwanta wlh yau saika sakeni wlh bazancigaba da zama da kaiba tunda baka da imani" Sosai Abba yayi sanyi Kallon Aunty fadila yayi dake yiwa Mamy firfito yace "wani Asibiti aka kai ta" Asibitin Dr aminu "ta bashi amsa Tashi Abba yayi ya ce " bari naje Chan Asibiti ita kuma ku kula da ita sosai "yana gama fad'ar haka ya fita tare da Alh Yusuf suka tafi asibitin suna zuwa Suka tarar da Su mama chirko chirko tare sukacigaba da zama jiran fitowar likitocin yayinda Abba da Daddy ko kallon juna basuyiba suna zaune wani likita ya fito ya ce " ina wad'anda suka kawo Hajara wacce Tasha fiya_fiya har rigen cewa ga munan su Mama ke "Kallonsu yayi ya ce " Ammafa Gaskiya yarinyar nan ta Auna arzik'i rabon kwana a gaba ne ya tayar da ita amma gubar da tasha mai kashewace nan take Yanzu munyi bakin kokorinmu wajen ganin mun bata agajin gaggawa alhmdll Munsamu mun daidaita abun saida bazata tashi yanzu ba zata iya kai gobe Gaskiya zaku iya shiga ku ganta"Alhmdllh duk suka Ambata tare da sauke ajiyar zuciya musamman Alh Yusuf Mummy ma sosai tayi hamdala dukda tashin hankalin ciwon Arman da suke ciki dukansu d'akin da Aira take suka nufa kwance suka tarar da ita saman gadon marassa lafiya bata Ko motsi drip daure ga tsintsiyar hannunta numfashine kawai zai tabbatarma da tana da rai Shima ba Sosai ba sai Wanda ke kusa da ita zaigane tana yinshi cike da tausayawa Mama Halima da Mama sukace Allah bata lafiya Abba ko sosai ya tsorata ganin har akan abun nan zata iya kashe kanta Shima addu'ar fatan samun lafiyar yayi mata Alh Yusuf bako kunya yaje ya zauna gadon da take tare da kama hannunta guda da babu komai ya ce "Allah ya baki lafiya my wife ya tashi kafadunki" Mama Halima da haushinshi takeji tsaki taja tare da fita itama Mama fitar tayi Dan haushinshi sukeji tace "me budurwar zuciya kawai wannan ritaten k'aton Alhaji zaiba figigiyar y'a ko ba ta mutu ba yanxu wannan ai sai ya kasheta inashi ina ita" Sai wajen 10pm tukwana Dr ya fito tare da cewa su Daddy su biyoshi office d'inshi cikin girmamawa binshi sukayi har office d'in hankalinsu duk tashe Bayan sun zauna kallonsu yayi ya ce "Alhaji munyi iya bakin kokarinmu wajen ganin mun shawo kan Lamarin d'anka alhmdllh mun d'anci nasara Kad'an zuciyarshi ce take gab da Bugawa Wanda idan ba ayi Sauri wajen ganin Anyi mashi abunda yakeso komai zai iya faruwa Sannan yanzu Egypt zamu turaku munyi magana da Babban likitan zuciya dake Chan gobe a shirya tafiyar kawai saimu tafi tare insha Allahu zai samu lafiya Allah ya bashi lafiya" cike da tashin hankali Mummy dake kuka ta ce "ciwon zuciya kuma Arman innalillahi Na shiga ukku" calm down Hajiya insha Allahu zai samu lafiya kiyi tayi mashi addu'a "Girgiza kai Mummy tayi tayi ta ce " to doctor mungode yanzu ashirya tafiyar goben harni saimu tafi"ba matsala Hajiya Daddy ko ya kasa magana kallon Dr yayi yace "ayi duk abunda ya kamata zanturo PA d'ina a shirya komai Dan Allah ka taimaka mana Dr karmu rasashi shi kadai garemu" Insha Allahu Excellency zai samu lafiya amma ayi kokari wajen ganin an bashi ko an mishi abunda yakeso Dan ciwon nashi na attack ne kamar yaji ko yaga abunda yafi k'arfin kwalwarshi"Girgiza Daddy yayi yace insha Allahu yanzu zamu iya ganinshi "ba matsala ranka ya dad'e zaku iya ganinshi amma kar ayi hayaniya a kanshi" A tare da Dr Mummy da Daddy sukaje sukaga Arman Mummy saida tayi kuka ganin d'an nata yashe kamar gawa Cikin kuka ta ce "Allah ya baka lafiya my son " Daddy ko ya jima yana zirga_zirga fitowa yayi Inda su Abba suke ya nufa Yana zuwa kallonsu yayi yace "zamu iya magana" Batare da Abba ya kalelleshiba ya ce "ba matsala" Kallon Alh Yusuf Daddy yayi yace "ko zaka bamu wuri" Dage kafada Alh Yusuf yayi tare da komawa d'akin da Aira take Dan Kara ganin jikin nata Kallon Abba Daddy yayi kamar bazaiyi magana ba saikuma yace "Daman Alfarmace nake son nema wajenka akan maganar yaran nan ni ta bangarena na hakura su Auri juna tunda dukansu Suna cikin wani hali kuma suna son junansu " "to ai anriga an baro magana a baya ko baka da labarin dazunnan aka daura Auren ta Saidai Kuyi magana da mijinta yanda yace yanzu bata hannu na" Daddy Danne zuciyarshi kawai yayi Dan sosai yakejin haushin Yayan nashi kamar bazai magana ba saikuma yace "OK had'ani da mijin nata" ta waya Abba ya kira Alh Yusuf yana zuwa Abba ya bar wajen tare da barin asibitin ma gaba d'aya kallon Alh Yusuf Daddy yayi ya ce "Kaine mijin mamana Hajara?eh nine lafiya" Ajiyar zuciya Abba ya sauke ya ce "Ina son ne ka saketa Saboda d'ana yana cikin wani hali a saboda da ita Sannan itama a saboda shi ta shiga halin da take ciki suna son junansu ka saketa ta auri wanda take so ni kuma daga million d'aya abunda yakai billion zan iya kashewa a saboda d'ana ka fad'i duk abunda ka kashe tundaga neman Auren har auranta zan linka maka sau gomanshi"Alhaji Yusuf jin maganar Daddy ma yake ya raina mashi wayau yanda yake maganar a gadara ga maganar da yazo da ita ko hauka yake ai bazai iya sakin Matar da tazomai allura cikin ruwa haukama yake zai saketa "cike da girmamawa Alh Yusuf ya ce " A Gaskiya excellency kayi hakuri amma Bazan iya sakinta ba ina sonta sosai nima zan iya shiga halin da d'an naka ya shiga koma fiye da nashi Allah ya bashi lafiya amma kayi hakuri Bazan saki mata ta ba "Yana gama fad'ar haka Shima yabar wajen tare da d'aukar motarshi ma ya bar asibitin Daddy sosai ranshi ya k'ara k'uluwa har ya sauke fushinshi shida akafiyima laifi ma ya nemu alfarma su hanashi cike da b'acin rai ya koma d'akin da Arman yake tare da d'aukar aniyar har abada bazai kara neman alfarma wajensu ba kallon Mummy yayi yace " Daman na fad'a maki mutumin Chan baida mutunci shiyasa Tun farko banje neman alfarma wajenshi ba nan ya kwashe yanda sukayi ya fad'awa Mummy cike da hawaye ta ce "Kayi hakuri sannan ta kalli Arman tare da murza hannunshi tace " Allah ya baka lafiya my son ya cire maka k'aunar yarinyar nan a cikin zuciyarka"Zanje mu cigaba da shirya tafiyar nan gobe Dan komai ya Zama cikin ready"gyada mashi kai Mummy tayi batare da tace komai ba Mummy ita ta kwana tare da Arman Wanda ko motsi bayayi Aira ko Mama Halima ta kwana da ita Washegari Wajen k'arfe Sha biyu na safe Aira ta Farka da sunan Arman ta farka a bakinta Su Mama Halima da Alh Yusuf da Aysha Da Aunty Ramlat yayar Mamy dukansu hankalinsu ya koma Wajenta cikin Sauri Aysha tayi gadon tare da kama hannunta ta ce "Alhmdllh sis kin tashi" Aira da takejinta kamar ba ita ba Bud'e idanunta tayi a hankali Sai
Chapter 46 · 0% Book details