Sashe 28
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 4 min read
kara hutawa naga kamar gajiye kike" harara Khady ta gallawa Aira tare da Jan tsaki Hafsa ce ta tashi ta ce "Daman da wasa nake wlh " Tashi sukayi ita da Aira suka koma bedroom d'insu suna kwasar Dariya. Da dare Aira ta lallaba Amma ta ce "Dan Allah sis kaya na zaki daukomun a bangaren Inna wayoyina na cikin d'akin Dan Allah daukomun " Dak'yal ta samu Amma taje ta d'auko mata Allah yasa lokacin da wuta Aiko tasa wayoyinta Duka chaji k'aramar Kara d'aya tayi ta maza ta bud'e tana kiran shi saida ya katse ya kira Ajiyar zuciya ta sauke Suka shiga gaisawa cikin so da k'auna kwancewa gado Aira tayi rufda ciki tana jin farinciki ya mamaye zuciyarta Sunjima suna waya tukwana ARMAN ya tambayeta Ya sukayi da Abba Duka ta fad'amai amma bata fad'amai maganar karshe ba na Aure zaiyi mata Dan bata d'auki abun serious ba "Ajiyar zuciya Arman ya sauke ya ce " Ai wannan ni Abba ya taimaka bai sani ba ya hanaki fita bare wani ya ganemunke har yace yana so,makaranta ma hakan yayimun dad'i Daman ina kishin shigarki makaranta kowa ya dinga kallemunke a bilis"na Ukku kuma abunda bazai tab'a yiwa bane har abada Watau rabuwarmu Kinga ko ai Hukuncin mai sauki ne "Dariya Aira tayi ta ce " kai yaya kuma fa hakane sai kuma ta bata fuska ta ce "To idan munason mu hadu yazamuyi Bayan ya hanani fita" murmushi yayi ya ce "banida damuwa da wannan saboda duk sanda naso ganinki dole saina ganki ko ana ruwa ko ana iska Allah yana tare damu Insha Allahu" wani sanyi Aira taji a ranta kwata-kwata ma Arman ya kwantar mata hankali Sai takega Duka hukuncin ma da Abba ya yanke mai sauki ne sunjima suna shan hirarsu gwanin sha'awa cikin so da kaunar juna. Hafsa satinta guda Driver yazo daukarta a lokacin Su Yaya Umar sunzo sosai yayi mata tsaraba su Mamy ma sunyi mata tsaraba sosai Airako hada kuka duk saitakejin ba dadi itama Hafsa din Har zasu tafi Aira da Jan magana ta ce "Yaya ka amshi numberta kuwa" mik'a mata Wayarshi yayi ya ce "Amshi ki sanyamun ki sanya mata tawa mundinga gaisawa a waya tunda bata da zumunci " murmushi Hafsa tayi ta ce "Yaya aikai dinne ganinka ke wuyar gani" cike da gayya Aira ta sanya musu numbobin juna Khady ji take kamar ta shak'e Aira sai aika mata da harara take da abun ya isheta tsaki taja tare da ficewa tabar gidan Gaba d'aya "girgiza kai ya Umar yayi sannan ya kalli Aira ya ce " so kuke ku haukatamun mata ko"Dariya Aira da Hafsa sukayi suka tafa Hafsa ta ce "To me aka mata kawai kishidai yayiwa Matar ka yawa " Dariya Aira tayi hada rik'e ciki Mamy dake kallonsu girgiza kai tayi ta ce "Allah shiryeku" Mama ko Addua tayi ta ce "Allahsa Umar son Hafsa yake wannan Matar zamanta ita kadai gidan dana matsala ce " Hafsa Na tafiya Aira ta koma ciki duk batajin dad'i. Haka rayuwa taci gaba Aira bata zuwa ko ina Abba ya fad'awa me gadi kar asake a barta fita Amma tuni harta fara zuwa makaranta hakan ko Kad'an bai damu Aira ba Saboda tana shan wayarta da Arman kullum Daki take rufewa susha wayarsu da video call da dare ko raba dare suke suna shan love Harsai Amma tayi fafatu akan sun hanata bacci Daman Haidar ya koma bangaren Inna yake tayata kwana. A haka har akayi wata guda ranar wata juma'a Arman ya kirata ya ce ya shigo kano kuma yanason su hadu tasan yanda zatayi ta fito su hadu Sosai hankalin Aira ya tashi ta kasa zaune ta kasa tsaye Mamy taje ta samu tana hawaye ta ce "Mamy Dan Allah gidan Aunty Aisha nake so naje ki taimakamun naje kafin Abba ya dawo Allah na dawo" Wlh Aira ba ruwana Tunda Abbanki ya hanaki fita kawai ki hakura yanzu Abun na barki ki fita ne ni kaina matsala zaki jamun ba ruwana karkije ko ina idanma Aishar kikeso Kuyi magana amshi wayata ki kirata"Goge hawayenta Aira tayi ta ce "Shikenan Mamy ba sai na kira ta ba " ta fad'a tana barin d'akin saida Mamy ta tausaya mata Aira na komawa gado ta fad'a tare da kiran Arman yana kira ta fashe da kuka ta ce " Yaya mamynma ta hana "kuka kawai take Lallashinta yayi ya ce " jeki ki samu mai gadi ki lallabashi kiga zai bari ki fito "to Aira ta ce sannan ta fita tana zuwa ta samu Baba mai gadi najin radio har k'asa ta durkusa ta gaisheshi ya amsa cikin sakin fuska Zaunawa tayi gefenshi ta ce " Baba Dan Allah fita nakeson nayi "Dayake baba suke cemai tsohone sun jima dashi " kallonta yayi ya ce "Kiyi hakuri Hajiya Alhaji yayimun kashedin na sake na barki kika fita a bakin aikina ni kuma aikin nan dashi nake sha nake ci shine rufin asiri na bazanso rasa shi ba Dan haka kiyi hakuri bazan bud'e miki k'ofa ba" Cikin tashin hankali Aira ta fara kuka ta ce "kayiwa Allah da girman manzon Allah S a w Baba ka bari in fita wlh ba zanja maka matsala ba yanzu zan dawo........✍🏿