← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 127

Sashe 23

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 7 min read

.....Ya ce "Keda kikasan Inna saurin sayuwa gareta sayayya na had'o mata na rikita ta nace ta bani ke zaki rakani wani bikin best friend Dina kuma kowa da budurwarshi yake zuwa sannan na had'ata da 100k nace ko minti ashirin bazamuyi ba zamudawo "karkiga yanda ta rude hada cewa bari taje ta tadoman ke" Dariya sosai Aira tayi ta ce "Kai yaya amma wlh kasan logar Inna" shafa sajenshi yayi ya ce nid'in na wasa ne "cikin shagwaba tace" to baka tunanin Abba Da kowa zai gani me yasa kakira yan gidan television"Murmushin gefen baki Arman yayi ya ce "Saboda su shaida kalar son da nake maki" Uhm kawai ta ce "ta d'ora kanta a saman kafad'arshi Ta ce " My yaya wai tun yaushe ka fara sona haka"Tun ranar da kikazo duniya "ya fad'a yana murza lallausan hannunta sannan ya ce " kece ma zan tambaya yaushe kika fara sona haka kodan Kinga d'an beautiful ko"Hararar wasa tayi mashi ta ce "Kaine dai kaga y'ar beauty ka rud'e" Dariya Arman yayi ya ce "to oya nima fad'amun yaushe kika fara sona" Cikin k'asa da murya ta ce "Tun sanda ina zanin goyo" Dariya sosai maganarta Tabawa Arman saida ya dara Suna isowa Gidan Aunty Halima Har cikin get d'in gidan Mai gadi ya shiga dasu Shima had'adden gidane flat da ya tsaru da shuke shuke Saidai baida wani girma sosai Dan Parking space d’in bazai wuce ya d'auki mota Ukku ba Aira ta fara fita tukwana ARMAN Shima ya fito Hafsat ce ta rugo da gudu daga ciki ta Rungume AIRA ta ce "oyoyoy my Fav sis sannunku da zuwa Gaskiya i'm glad to see you” " Itama Rungumeta Aira tayi ta ce "Nima nayi farincikin ganinki sister Tukwana suka shige palour Arman ma yabiyosu Bayan sun zauna Hafsa ta ce " bari na kira Mama ta na ciki ta fad'a tare da shiga Tare suka fito Hafsat da Mama da harara Mama ta tare su da ita Arman ko murmushi yayi tare da cewa "Sannu da fitowa big Mom uwata ta kaina" Harara Mama ta aika mashi ta ce "marar mutunci nizakayiwa dad'in baki kai yanzu abunda kayi ko ince kukayi ganinku kun kyauta" Haba Mama ki bari mu gaisa mana sauran fad'a saiya biyo baya "Arman ya fad'a " Aira ko kasa tayi da kanta "Mama ta ce " baza a gaisa ba d'in wlh karkaja nayi maka shegen Duka a gidannan "Dariya Arman yayi tare da tashi yaje fridge ta d'auko ruwa ya ce " tunda ba ayi mana tayi ba bari mu d'auka da Kanmu ya fad'a tare da d'auko cup ya tsiyaya ya sha sannan ya k'ara tsiyayawa Ya mik'awa Aira ya ce "My cutie amshi kisha nasan kinajin kishi" Aira da duk kunya ta isheta ta lura Arman kwata kwata baisan meye kunya ba k'asa tayi da kanta Mama ta ce "Marar kunya kawai " Aira ta d'ago gabanta na faduwa ta ce "Ina kwana Mama "Lafiya qalau Mamana ke yanzu abunda kukayi kun kyauta kenan kuje ku jawa kanku bakin duniya bakin mutane ma aka barku dashi ya isheku dole saita hakane zaku bayyanawa duniya kuna son junanku Dan tsabar shak'iyanci" Aira tuni idonta ya ciko da k'walla cikin kuka ta ce "Mama kuyi hakuri bazamu sake ba" Haba Mama Kinga kin sanyamun ita Kuka Dan Allah abar fad'annnan haka shikenan "Arman ya fad'a yana mik'awa Aira Handchiep Girgiza kai kawai Mama tayi ta ce " Allah kyauta kai daman ai nasan ba kunya gareka ba Sannan ta kalli Hafsa ta ce "jeki hado musu breakfast" Aira da Arman sukayi rigen cewa "mun karya kafin mutaho" Hafsat ce taja Aira ta ce "Taho muje ciki sis Arman har suka wuce yana kallonta cikin so da k'auna " Mama ce ta sauke ajiyar zuciya Bayan su Aira sun wuce ta kalli Arman ta ce "Wai me ya kaika hada abun nan jiya maimakon kazo ka sameni ka fad'amun komai mubi komai a hankali har mu samu Iyayenku su Amince Amma kaje ka rikita Abu karkaga irin fad'an da Babanta ya dingayi dazu da na kirashi " Mama a tunanina hakan da mukayi shi zaisa su gane kalar son da mukeyiwa junanmu har su hakura su bari mu mallaki juna "girgiza kai Kawai Mama tayi ta ce " Allah ya kyauta Gaskiya zance nafi kowa jin dad'in wannan al'amarin Allah ya tabbatar mana da alkhairi ya ida nufi"murmushi ARMAN yayi cikin jin dad'i yace "Ameen Mama yanzu kikayi magana wlh ina son Aira sosai Mama bazanso abunda zai raba mu ba Dan Allah kiyi mana kokari ki shawo mana kansu" ya fad'a kamar mai shirin yin kuka"Insha Allahu zanyi iya bakin kokarina "Daganan suka cigaba da hirar duniya sai wajen Azahar Arman yayi musu bankwana ya wuce Abuja.

Aira ko suna Chan suna shan hira da Hafsa tana nuna mata hotunansu da vedio wadanda ta gani a social media sosai Aira tayi mamakin yanda abunsu ya bazu duniya cikin k'ank'anin lokaci.
Mamy ce zaune gefen kujerar Abba ta na hawaye ta ce " Abban Aira Dan Allah ka taimakamun a nemo Inda Aira take harfa Azahar yanzu kayi hakuri mu nemeta karta b'ata"cike da b'acin rai Abba ya hayayyak'o mata ya ce "Ke ki tashi kije ki nemeta da yake ni na aiketa na rantse da Allah kika k'ara zuwamun da maganar nemanta ranki zaiyi mugun b'aci ki barni da abunda ke damuna Dan tsabar rainin hankali harma nemanta kike yarinya ce ita kuma ina nan ina sauraran zuwanta Saidai ki haifi wata y'ar badai ita ba" Kuka Mamy ta fashe dashi ta ce "Wlh ko ta dawo bazaka kashemun y'a ba duk ba kai kaja ba da baka raba suba da duk haka ta faru ina dalili tunda suna son junansu ku barsu mana Su auri juna kawai in banda ana son a samun y'a cikin wani hali nidai wlh na gaji kawai a nemu mafita" Abba ji yake kamar ya d'auke Mamy da Mari tsabar bacin rai da kyal ya iya control d'inshi ya tashi ya bar mata d'akin tare da barin gidan Gaba d'aya mamy ko durk'ushewa tayi ta na kuka mai tab'a zuciyar mai sauraro.
Da misalin k'arfe Tara na dare Aira suna dinning suna dinner ita da Hafsat da Mama sai faruq Wanda Aira tsakular abincin kawai take hankalinta duk yana wurin Mamy "Mama ce ta lura da haka ta daddabata ta ce " Mamana Yadai ko bakyajin dad'i"girgiza kai Aira tayi ta ce "a a Mama " to menene"Mamy ta fad'a ta na hawaye "to shine kuma saikinyi kuka uwar y'an shagwaba Bari mu gama na kira maki ita " cikin murna Aira hada Dariya ta ce "thanks Mama" suna gama dinner Mama ta kira Mamy ringing Biyu ta d'auka Daga d'ayan b'angaren mamy tayi sallama Mama ta amsa Tare da cewa "Yadai Naji muryarki wani iri maman Aira" ba dole ba Halima tun jiya fa Aira bata dawo gida ba Gashi Abbansu yaki saurarena "Ajiyar zuciya Mama ta sauke ta ce " Aira fa ta na gidana Ni nasa ya kawomun ita saboda nasan halin yaya a lokacin nan zai iya illatata"Ajiyar zuciya Mamy ta sauke Wanda har saida Mama taji cikin waya ta ce "Alhamdulilla Halima kin taimakemu wlh kuwa da ta dawo din da illatatadin zaiyi gwara da take nan din daman tashin hankali na ba asan Inda take ba " Ai nasan hakan zata faru shiyasa idan komai ya lafa zanzo muyi zama Dan Gaskiya yaran nan nason junansu inba wani hali akeso ajefa rayuwarsu ba"Mamy ta ce "Wlh maman Hafsa nima tuni na hango hakan amma Abbansu yaki ganewa kamar ma Kara zugashi ake ni da sunbi ta tau kawai su barsu muga yanda Allah zaiyi" Hakane Allah dai ya shige mana gaba Mama ta fad'a sannan ta ce "ga Airar ku gaisa A tsorace Aira ta amshi wayar ta ce " Hello Mamy ina yini"Lafiya qalau ya kaduna d'in"Alhmdllh Mamy "Sosai Aira tayi mamakin Mamy yanda ta nuna mata kamar ma komai bai faru ba " To sai anjima "Mamy na fad'ar hakan ta kashe wayar Ajiyar zuciya Aira ta sauke Dan kashi Hamsin cikin d'ari na tashin hankalin da take ciki ya ragu yanzu kuma saura na Abba batasan Me zata tarar ba.
Chapter 23 · 0% Book details