Sashe 121
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta ce "Ashe da gaske kake my hero I miss you so much Wlh " Ta fad'a tana marairaicewa "kama lallausan hannunta yayi Cikin kasalalliyar murya ya ce " Naki a baki ne cutie ba k'aramun kewarki nayi ba "Uhm ai naga harka rame wlh yakake ya zaman gauranci ta fad'a tana Dariya" Hararar wasa yayi mata tare da shigar da ita mota Shima ya zagaya ya shiga ya ce "dole kicemun gauro Tunda dai an maidani na karfi da yaji" Kama hannunshi Ayra tayi ganin yana shirin tada mota ta ce "Yaya ina kuma zamu please ka tsaya " Bai saurareta ba sai Tada motar da yayi ya ce "Allah baki isa ba Yau saina Rage zafi ya fad'a yana Jan motar da karfi " Duk yanda Ayra ta firgice amma bata nuna masa a fili ba "Uhm kawai ta ce " Cikin zuciyarta kuwa tsoro ne fal a ranta Dan batasan Inda zai kaita ba gidansu dake nan kano taga ya nufa haka yasa ta Dan kwantar da hankalinta suna isa daukarta yayi ba tare da jin nauyi ko wani Abu ba bai dire ta ko ina ba sai Bedroom d'inshi Ayra na ganin hakan tasan yau Kuma saita Allah tutturo baki ta dingayi ta ce "Yaya Banda lafiya fa har yanzu" Hararar wasa yayi mata ya ce "Ai zaki warke yanzu zan baki magani......Bayan komai ya lafa Ayra sai nishin wahala take Dan ta gurzu ba Kad'an ba wanka ta yunkura tayi tare da fitowa ta sanya Kayanta da Tazo tashi dukda sunyi squeeze Kallonshi tayi da shidinma ita yake kalla yana k'are mata kallo ta galla masa harara ta ce " ai saimu tafi gida ko"Mirginawa yayi tare da kwantawa ya ce "Akwai gidan da ya wuce wannan kin dawo gidanki ai" D'ora hannu aka Ayra tayi ta ce "Na shiga ukku yaya so kake Su Mamy su tsigeni To wlh nidai ka maidani gida " Dariya yayi mata tare da mik'ewa ya ce "Kina da gidan da yafi na mijinki daman" Kuka ta sanya masa hada diddira kafa ta ce "Daman kasan wayau zakayimun shiyasa " sosai take zuba masa ruwan shagwaba shiko Dariya kawai yake mata tana nan har yaje yayi wanka ya shirya cikin shigar K'ananan kaya da sukayi mugun Amsarsa Suka Kara fito masa da ainahin kyawunsa Ita kanta Ayra da ta Kalleshi saida ta yaba A zuciyarta ta ce "Nidai nayi sa ar miji baida makusa ta ko ina ga iya d'aukar wanka " Irin Kallon da take masane ya sanyashi hure mata ido ya ce "Yadai y'an mata ko wankan yayi miki ne " Firgit ta dawo cikin hayyacinta ta ce "Uhm wankan yayi kyau sosai hero Saidai ina kishin Ace ka fita da shigar Dan Banason Ana kallemunke miji " ta fad'a tana turo baki"rungumota yayi ta baya Tare da rada mata a kunne cikin sexy voice dinsa mai dad'in sauraro ya ce "Mujaheed na Hajara ne ita kad'ai Ki daina kishinsa da yawa Dan kinriga kinyi babakere a cikin zuciyarsa babu gurbin wata dagake ba k'ari kece ta farko kece fari sannan kece karshe Kin kulle zuciyata da Soyayyarki a cikinta Wanda Kika jefar da Makullin a ruwan maliya Babu wacce ta isa ta sameshi " Sosai farinciki ya mamaye zuciyarta Ayra Tasan Gaskiya mijin nata yake fad'a mata Dan Bata tabajin tunda take a rayuwarta ba Inda akace ga budurwar Arman ko da kuwa a yarintane hakan yasa Daraja da martabar mijin nata Koda yaushe take karuwa a cikin zuciyarta cikin jin dad'i ta ce "Nasan da haka mijin da babu kamarsa kaid'in na musamman ne a cikin mazajen duniya Har gobe ina Kara godewa Allah na mallakamun kai da yayi a matsayin miji kuma uban y'ay'a na anan duniya da ma lahira insha Allahu" Sosai suka dinga zubama juna kalamai masu dad'in sauraro Nanma saida suka shagala suka k'ara ruftiyawa kogin wata soyayyar Sune dai basu gama soyayyarsu ba har magriba ganin haka ya nusar da Ayra tun Ukku rabonta da gida hakan yasa hankalinta yayi gida Bayan sun Sake wanka Ta sanya hijab d'inta hannunsu mak'ale Dana juna harsuka isa parking space Inda ya fito da motarsa a hanya saida ya biya yayi mata sayayyar kayan ciye ciye da Kaza da su juice tukwana ya wuce da ita gida a lokacin amma kusa isha i cike da kewar juna suka rabu Aira ko tana shiga cikin farfajiyar gidansu saita tuno da a da lokacin da idan suka fita da Arman da rayuwar da sukayi a baya da dramar su a gidan Inna batasan lokacin da wasu hawaye suka zubo mata ba ta ce "Bazan tab'a daina kukan rashinki ba my Inna Allah jikanki da Rahama " Goge hawayen tayi tare da shiga cikin Amma da Mamy kawai ta tarar a palourn Haidar na hannun Amma tana masa wasa "Kallon Mamy tayi ko zata nuna mata wani Abu saitaga tama kauda kanta wajen amma ta k'arasa Haidar na ganinta Ya mik'a hannu d'aukarsa tayi tare da cewa " Wannan k'aunar Sis keda Haidar zanga idan Kikayi Aure yaza ayi"Dariya amma tayi ta ce "Ai dashi zan tafi Shima Ai ya al-Ameen din ya San da wannan zancen " Dariya Mamy da Ayra sukayi Mamy ta ce "Aiko harya koroki keda d'an naki" Korama tun tana da sauki Mamy Ina aka tab'a kai amarya da d'a"Dariya amma tayi ta ce "akanmu za a fara sannan ta daga Ledar da taga Ayra ta shigo da ita ta ce " My k'anwas me aka samo mana"Dariya Ayra tayi ta ce "Sai Naji wani iri ma wlh wai my kanwa ko kunya ma baki jiba Ni yanzu ai Yayarkice tunda Harda yara Ukku " Harararta Amma tayi ta ce "Kujimun yarinya nanfa jinki kike daidaima kike da kowa To ko dai kiki ko kiso Ko d'iya d'ari kikayi Nice dai gaba dake ta fad'a tana Kai kaza baki" Dariya ayra tayi sosai ta ce"Kici a hankali karki kware uwarson girma"Mamy ce ta ce "waini Ayra ya maganar Karatu zakici gaba kuwa Dan naga amfara registration na Jamb d'in this year naga ma ke kwata kwata kamar karatun baya gabanki" k'asa tayi da kanta Ayra tayi ta ce "Ba haka bane Mamy Ni wlh wahalar ce Nake tsoro Ga Haidar Kinga Ko shekara fa Baiyi ba Yanzu idan nace zanjona karatu zansha wahala kuma ma shi baiyi mun maganar makaranta ba har yanzu bamuyi maganar dashi ba" Tab'e baki Mamy tayi ta ce "Ai karatu baya hana kula da yara Ni Ina goyonki Nayi NCE Dina Hankali kwance kuma" Dariya ayra tayi ta ce "Mamy Ai Inna tace Lokacin baki iya komai ba ita ke Reno na Ke ai y'ar dad'in Inna ce a bulus kika sameni" pillow mamy ta d'auka tare da nufar ta dashi zata Jefa mata ta kauce tana Dariya ta ce "ja ira da yake ke kikayi nak'udar kika haifi kanki ko" Dariya ayra tayi tana barin Palourn bedroom dinsu ita da Amma ta nufa sosai tayi hawaye tunowa da irin labaran da Inna ke basu Da dramar da ake sha a part d'inta Haidar ta sauyawa Kaya ta sanya masa pampas amma ce ta shigo da indomie A hannunta a plate Marar yaji ta zauna tare da cewa "Miko na basa yaci baici Ta dare ba " Mik'a masa shi ayra tayi ta ce "Zaki barmu da aiki fa kika tafi sis kin saganta yaron nan da yawa ace kullum sai an dafa masa indomie sau kusan hud'u Jiyafa Da na kwana dashi Cikin dare ya dingamun kuka na basa komai yakici saifa Mamy ta ce " sai na dafa masa indomie Itace kawai yake ci yanzu komin dare haka kike tashi ki dafa masa "Murmushi amma tayi ta ce " Yaronne dole a dage masa da abinci wlh ni tausayima yake ban Ace an yaye ka tun 7months da haihuwa danma hakuri garesa wlh baya da kukan banza"Jinjina kai Aira tayi ta ce "Wlhko Yana da hakuri kam ba kamar su twins ba Ai cikin nan yamun cikas wlh Afa lissafin da nayi yana da 4 months na samu wani cikin Ina ta haukana bansaniba Jifa Dan Allah wai wannan Dan yaron wata sha d'aya za ayiwa k'ani kamar wata kaza" Harararta Amma tayi ta ce "Ki godewa Allah wlh Wasu Nema ma suke da kud'in da komai Su hana idonsu bacci suna rokon Allah akan ya basu Amma ke kinsamu shine zaki butulce masa " Shiru Ayra tana Nazarin hakane kam Astaghfurilla ta fad'a tare da Kwanciya kan Gado ta cire hijab d'inta ta ce "Nikam na kwanta saida safe na gaji wlh " ba dole ki gaji ba Tun rana Kinje kuna Abu d'aya"jin abunda amma tace ya sanya Ayra bata Kara cewa komai ba kenan kowa yasan Abunda sukayi Tsaki taja a ranta ta ce "Aidai miji na ne kuje Kuyi ta zargin naku"ba bata lokaci bacci yayi awon gaba da ita.. tun daga ranar Arman ya samu kofar zuwa ya kirata itakam bata kin fitowa suyi Tafiyarsu suje su shakatawarsu ya maido ta Ayra ko sosai taji dad'i ganin ba Wanda ke hanata Fita Abba ma akwai lokacin da har ganinsu yayi amma baice komai ba Arman da yazo da niyyar kwana Ukku ya koma shine saida yayi sati kafin ya koma wajen Aiki tunda ya tafi kullum suna waya da video call Su raba dare Suna baza soyayyarsu A yanzu cikin Ayra ya shiga watan haihuwa Inda Yayi wani irin girma sosai Kamar lokacin da take Da cikin twins Sosai gidan ake kaffa kaffa da ita Mummy ma duk sati tare suke zuwa da twins taga jikin nata Ranar wata Alhamis Ayra ta tashi da nakuda sosai kai tsaye Asibiti aka wuce da ita Sosai Tasha wahala Tun safe ita ce bata haihu ba sai Bayan magriba Inda ta haifo twins d'inta Duka maza kyawawan gaske kowa yazo saiya yaba yaran Bayan an sallamesu daga asibiti koda aka kira Arman aka fad'a masa haihuwar sosai ya shiga farinciki washegari tun asuba ya baro Abuja Amma ta fito masa da Yaran Wanda yakejin soyayyarsu ta musamman Dan d'ayan kamarsu D'aya da Dad d'inshi d'ayan kuma kamanninshine sak Nanfa Arman ya shiga bishashar kudi sati na zagayowa ranar suna Yara sukaci suna