← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 127

Sashe 14

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

Man zafi Aysha ta d'auko ta dinga shafa mata tukwana ta b'alla mata magani dak'yal ta samu ta Had'iye kallon Aunty Aysha tayi ta ce " Thnks Aunty"Amma ce dake zaune ta ce "Sannu Aira" tsaki Aira taja tare da kauda kai Dan Duk haushin mutane take ji".

jan bakinta amma tayi shiru dan tasan Aira akwai huce haushi,Hafsa ma dake gefen Inna ta ce "Ko baki lafiya Sis" Itama banza Aira tayi mata ,Aiysha ce ta ce "Kwanta Kan kujera ki huta kinji kanwata" gyada mata kai tayi tare kwanciya ta kalli sama ta rufe idanunta Tunanin yaya Arman ne kawai yazo mata a kwalwa taya ma zaiyu ace su rabu da juna duk wannan dukan da tasha batajin zata iya rabuwa dashi ga haushinta na zarginsu da Abba sukayi Abba hada cemata karuwa sosai ranta ke mata k'una gashi tasan Momy ba k'aramun fushi tayi da ita ba .

Hafsat ce ta kalli inna ta ce "Inna Dan Allah Na tambayeki Allahsa ki fad'amun" Inajin Hafsatu fad'amun tambayarki"Inna wai me ya had'a Daddy da Abba basa jituwo nidai tsawon Rayuwata tunda na tashi a haka na sansu Kuma Idan Na tambayi Mama dalili saitak'i fad'amun ta ce Wai Family issue d'insu ne basainajiba Abun Yajima yana d'auremun kai Dan Allah Inna fad'amun"

"Gyara Zama Inna tayi tare da cewa "Aiko yau zakiji labari tiryan tiryan y'ar nan ki gyara zama kisha labari inbanda abun Halima meye abun boye a Lamarin nan da duniya ma ta sani sannan ta fara da cewa..........✍🏿

*Tofa Abu ya rikice ya kuke tunanin Abba da Daddy zasu d'auki al'amarin nan kowannansu yad'au zafi*

*Ya makomar soyayyar ARMAN da AIRA zata kasance nan gaba Bayan al'amari ya k'ara rikicewa*

*Tofa ga wata sabuwa Hafsa tayi tambayar da kowannenku ke jiran Amsarta bari mu gyara zama Dan shan labari wajen Inna Dan nasan harkun k'agu kuji dalilin wannan gabar*😂

Share fisabilillah

*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
[6/5, 18:30] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️..............25&26

.....Kabir Da Abubakar y'an uwane Wanda suka fito ciki d'aya ma'ana uwa d'aya uba d'aya su Ukku ne a wajen iyayensu Abubakar ne Babba Sai Kabir da Abubakar ya bashi shekaru Ukku a duniya sannan Autar su Halima da har an cire ran Haihuwarta.

Saida khabir ya bata sama da shekaru sha biyu Halima Nada wata Ukku Allah yayiwa mahaifinsu Malam Umar rasuwa Mahaifiyarsu Hajara ita taci gaba da kula da su Iliminsu,cinsu,shansu,suturarsu da koman su Tasha wahala sosai akansu Dan dangin ubansu Tunda mahaifinsu ya rasu basu tab'a taimaka musu da komai ba .

Nida Hajara uwammu daya ubanmu ubanmu daya mu biyu kenan a wajen Iyayenmu Koda Allah yayiwa mijin ta rasuwa Saina dawo Wajenta daman mijina ya jima da rasuwa bantab'a haihuwa ba na d'auki y'ay'an Hajara tamkar nawa suma haka suka daukeni tare muka cigaba da kula dasu har Allah ya kawo girmansu.

Sun taso cikin Had'in kai da son juna Abubakar tun yana Yaro yake da sha'awar siyasa yayinda shi kuma Kabir yake da sha'awar kasuwanci Koda Abubakar ya gama jami'a ya fad'a kasuwanci Sosai ya habaka Inda Har yayi Aure ya auri Zainab y'ar nan kano ce mace mai hakuri Shima Kabir yana kammala karatunshi ya fad'a harkar kasuwanci kafin kace me sun Tara arziki me yawa Su suka dinga kula da ni da Mahaifiyarsu tare da kanwarsu da suke ji da ita.

Shima Kabir yayi Aure ya Auri Fatima y'ar gidan Wazirin Adamawa a Chan ya ganta ya aurota itama mace ce y'ar gidan mutumci ana haka ne Abubakar ya fad'a harkar siyasa yayinda shi kuma Kabir yake cigaba da kasuwancinshi Dan harkokinshima yawaici a waje yake yinsu.

Kabir d'anshi d'aya a duniya Muhajed (Arman )tundaga kanshi bai sake haihuwa ba Abubakar ya rik'e mik'amai da dama a cikin wannan jahar tamu A siyasa kuma ya tab'a Senator A shekarun Baya .

Zainab ta haifamai Yara Biyar Umar,Maryam,Aisha,Fauziya(Ummy),sai autarta Halimatu da aka sanya mata suna na" ana haka ne Allah yayiwa Mahaifiyarsu Rasuwa mutuwar da ta girgiza Al'umma musamman ni da Y'ay'anta munshiga damuwa sosai daga karshe kuma mukayi tawakkali ga Allah Yaranta suncigaba da daukata tamkar uwa Inda Abubakar lokacin da ya Gina wannan gidan Da muke ciki ya waremun bangarena guda Sosai suke kula.dani shida Kabir.

Ana hakane k'watsam Kabir Ya had'u Da Rahama y'ar asalin Garin Agadez Bayan rasuwar iyayenta take zaune wajen Babban Yayanta tare da matarshi dake zaune a nan kano yake kasuwancinshi Fara ce sosai ga kyau irin jajayen buzayen nan masu masifar kyau Tunda ya ganta Kabir ya rud'e ba k'aramun so yake mata ba Nan ya samu suka sasinta ita ma har ta Fara sonshi .

Wasa wasa magana ta fara k'arfi Wanda har iyaye suka shiga Aka kai kud'in gaisuwa wajen yayanta ganin yanda Kabir ya rud'e kullum zancenshi Rahama Ya sanya Abubakar cewa shikam ya kaishi yaga wannan rahamar da zata haukata mai k'ani Nan Kabir ya jashi ya rakashi Har gidansu Rahama Koda ta fito Abubakar ya d'ora ido a kanta Yaji duk duniya baitab'a ganin macen da tayi mishi a rayuwa ba sama da ita

Lokaci guda ya kamu da matsanancin sonta Dak'yal ya iya daidaita kanshi suka gaisa tare da musu fatan Alkhairi Kabir yayi mata bayanin yanda suke da Abubakar ta gaidashi cikin girmamawa Har lokacin ya kasa Daina kallon ta .

ita kanta saida ta tsargu tunda Abubakar ya ganta kullum da tunaninta yake kwana yake tashi Ana Hakane Tafiya Ta kama kabir China akan kasuwancinshi Nan ya mik'awa Yayan nashi ragamar komai game da rahama tare da cemai Dan Allah ya dinga kula mai da ita har ya dawo sannan duk abunda take buk'ata ya dinga zuwa yanaji Dan a lokacin waya bata wadata ba.

Tunda Kabir yayi Tafiya Abubakar ya dinga zarya gidan su Rahama Kulawa ta musamman yake bata fiye da wadda Kabir ke bata Tun bata sakewa dashi har tazo ta sake dashi Cikin Dabara Abubakar yayi yanda yayi ya sace zuciyar Rahama A lokacin taji ba Wanda take so saishi.

nan suka k'ulla soyayya mai karfi wanda har akazo ga maganar Aure dukda yayanta da farko ya hana saida ya lura Rahamar na mugun so shiyasa ya hakura ya ce abubakar ya turo iyayenshi Koda yaxomun da maganar korarshi nayi na shiga f'ada Inda na shiga ba tanan nake fitaba Ba yanda baiyi ya shawo kainaba amma naki Nace ba ruwana a maganar Auren cin amana .

Dangin mahaifinshi ya sama ya saye su da kudi su sukaje suka nema mai Auran Rahama cikin k'ank'anin Lokaci ba ayi wata guda ba aka d'aura musu Aure har lokacin Kabir na China Ranar Da aka daura Auren Ranar ya dawo garin Inda ya tarar da wannnan tashin hankalin Wanda ya girmi tunaninshi Yayanshi uwa d'aya uba d'aya ya ci amanarshi ya Aure mai Matar da zai Aura .

Ranar munga tashin hankalin da bamu tab'a gani ba Dan Kabir dukansu shida Abubakar daman suna da zafin kai Shak'e Yayanshi Kabir yayi Ya hau zaginshi da Tsine mashi Wanda dak'yal na samu maza suka rabasu Tofa tun daga lokacin nan suka k'ulla D'aurarriyar gaba da k'iyayya a lokacin Kabir yafi d'aukar abun Da zafi Inda Yayi Aniyar saiya yi mashi ramuwar gayyar abunda yayi mai.

Rahama da Zainab sun had'e kansu sosai dukansu basu da tashin hankali sosai Rahama ke girmama Zainab haka d'iyan Zainab suna girmama Rahama sosai baka tab'a cewa kishiya da kishiya ne dukda kuwa lokacin Mijinsu Yana rid'in Rahama Dan yaso ya nuna yafi sonta a fili amma rahamar Ta k'iya ta nuna batason gwara ya dinga musu adalci kar ya rikita musu Zama .

Ana Hakane Rahama ta samu ciki Sosai Ya d'ora son duniya akan cikin saikace lokacin ne za a fara Mashi Haihuwa Haka Rahama tayi ta rainon cikinta sosai take samun kulawa daga wajen mijinta da kuma Zainab Dan ni haushinta nake ji tunda ta zama silar had'a y'ay'ana fad'a har cikinta ya isa haihuwa ranar wata Juma a ta haifi y'arta kyakyawa Fara Sol wacce ta dameta fari da kyau Tunda aka haife yarinyar kowa ke sonta yayyinta kamar su cinyeta musamman Aysha .

Ranar suna Yarinya taci suna "Hajara sunan Mahaifiyarsu kenan " A lokacin da Aka haifeta Mujahid duk Juma a yana kawomun ziyara Da mahaifinshi ya hanashi zuwa kwata_kwata dak'yal da kuka da kuma na nuna mashi Ya daukeni ba uwa ba hakan yasa Kabir ke barin d'anshi zuwa wajena sosai nakeson Mujahid kamar yanda Tunda aka Haifi Hajara nake sonta Dukda dai bana son uwarta data hadamun y'ay'a fad'a.

Koda yaushe Hajara na bangarena inba kuka tayiba akaita wajen uwar sosai Mujahed ke sonta tun tana jaririya Danshi ya sanya mata Sunan Aira daga nan sunan ya bita a lokacin Mahaifin Aira baya hana Mujahid mu'amula da Aira Dan har lokacin yana jin nauyin K'anan nashi yasan shi yayi mashi laifi hakan yasa bai d'auki abun da zafi ba Dan koda Aira ta girma Har fita Mujahid yake da Ita Yayo mata sayayya a saboda Aira Mujahid Koda yaushe da ya dawo daga Makaranta ya na gida na yana like da ita harta girma.

itama kuma sosai ta shaku dashi koda yaushe tana lik'e dashi Dan idan baizoba Haka zatayi ta kuka Ta rikice sai in yazo ake samun Lafiyarta Bayan Haihuwar Hajara da shekaru Hud'u Rahama ta sake haihuwar d'anta Namiji Aliyu Haidar tun daga kanshi kuma haihuwar ta tsaya mata Chak sai yanzu kusan Bayan shekara goma ta sake haihuwar wannan yaron

Koda Mujahid Yaje Karatu k'asar Misra duk hutun da suka samu saiya taho Dan Ganin Aira Haka har ya kammala karatunshi Inda yana gamawa ya samu aiki a CBN Abuja Dan abunda ya karanta kenan har lokacin Mahaifin Aira bai damu da Taren Aira da Arman ba Dan ko da ya samu aiki Abuja tofa duk karshen mako saiya taho yaganta.
Chapter 14 · 0% Book details