← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 127

Sashe 27

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

Meye gabanki"Kawai haka nan ke Nifa karatun ma.ya fice a raina "Hafsa ce ta ce " Amma baki da hankali Aira to idan ba karatu ba zaman me zakiyi a gidan "Turo baki tayi ta ce " meye abun Rashin hankali ra'ayi ne kowa da nasa"to munji ra'yin ne amma me zakiyi banda karatu"Hmmm nifa wlh da so samu ne Kawai Ayi mana Aure *Nida Yaya Arman* wlh kwata kwata gaba d'aya hankalina baya kan komai yana kanshi kuma koma naje karatun Allah ba abun kirki zanyiba saboda tunaninshi ma bazai barni nayi karatu ba shiyasa ko a kaina da Abba ya ce bazanje karatu ba ni ya ma fa hutashsheni ai indai ba gani na nayi a d'akin yaya Arman ba matsayin matarshi to sannan ne hankali na zai kwanta har na samu damar yin karatu cikin kwanciyar hankali"sakato Amma da Hafsa sukayi suna kallonta Sosai ta basu mamaki Amma ta ce "Chabd'i lallai Aira waike kanki wani irin taurine dashi duk abun nan da akayi sabodake ba Aje ko ina bama Har kina tunanin wai Aure Aurenma da Arman kuma " Tsaki taja ta ce "To ina ruwanki ni bansan wani k'abli da ba Adi abar maganar" Hafsa ce ta ce "Ni banga laifinkiba Yanda Kuke baza wannan love d’in ai kawai gwara a shige daga ciki kowa ma ya huta" Dariya Aira tayi ta ce "Shiyasa nake mugun sonki sis " Dariya Hafsa tayi ta ce”Mudai a taimaka kar a samar mana D’an baba a waje a bari dai sai anshiga daga cikin dan naga dukanku ke da shi kan dancing yake “kulli a baya Aira ta kai mata ta kauce ta ce “ke dama yar iska ce wlh hafsa “Dariya hafsa tayi ta ce “Sorry uwar gida kuma Amarya a gidan Yaya Arman “insha Allah “Aira ta fada da karfi Amma ce ta ce "uhm sarkin tura turarre wannan ai ba a zuga ta" Dariya Aira tayi ta ce "da a zugani da kar a zugani duk abunda naso nake zugar bata hanani kuma bata sanyani indai akan yaya Arman ne " girgiza kai kawai Amma tayi dan kanwar tata ta riga da tayi nisa batajin kira Suna gama cin abincin Aira ta haye Gado ta kwanta Ta ce "Bacci zanyi kaina ke ciwo idan anyi magriba Dan Allah ku tasheni" kinsan dai baccin yamma ba kyau"Amma ta fad'a tana gyara Inda suka bata "ke kika San wannan Aira ta fad'a ta na jan blancket tayi kwanciyarta. Sai Bayan magriba suka tasheta tana tashi taji kanta ya daina ciwo sallah tayi ta fito palour Ta tarar da Inna cikin Sauri Inna ta tashi ta tarbeta ta ce " y'ar lelena Shine kika tafi kika barni duk nayi kewarki gidan bayamun dad'i sai yanzu da nake tambayar Zainab ke ban labarin Abunda ya faru wai ubanki ko gidana ya hanaki shiga rabamu yake so yayi"Inna tafada tana kwakuro hawaye "Dariya Aira tayi ta ce " Haba My Inna aikinsan ni Dake mutu karaba ki bari kawai ya huce nasan zai barni"yawwa y'ar kirki ai daman Nasan ke y'ar arziki ce Bazaki juyamun bayaba "Itadai Aira murmushi tayi tare da tashi tace bari na shiga wajen Mamy tashi Inna tayi ta ce " nima bari na wuce daman ganinki kawai nazo"Hug din inna Aira tayi tare da shigewa d'akin Mamy a Gado ta tarar da Mamy da Mama Halima saishan hira suke daman Chan tunda aka Auro Mamy k'awayene saboda sa'annine "Tsayawa tayi tare da gyaran murya kallonta sukayi Mamy ta ce " lafiya"sosa kai tayi ta ce "Lafiya Mamy sannan ta kalli Mama Halima ta ce " Mama Dan Allah wayarki zaki aramun"Mamy ce tayi karaf ta ce "Uban me zaki mata da waya" Bakomai Mamy "wayar Mama Halima ce tayi ringing duba mai kiran tayi saikuma tayi murmushi ta d'auka Daga d'ayan b'angaren ARMAN ya ce " Haba Mama tun d'azu nake kiranki bata shiga ina my cutie tun d'azu na kasa samun sukuni kwata_kwata banji muryarta ba Yau idan banji muryarta ba ban iya bacci wlh Mama please ki kai mata wayar"Kallon juna Mamy sukayi saboda wayar a hands free take girgiza kai Mamy tayi Mama ta ce "To sarkin y'an Rashin kunya aikama tambaya mun Iso lafiya" Kamar Wanda zaiyi shagwaba ya ce "Nasanma kunje lafiya insha Allahu nidai bani ita please" Aira duk tana tsaye jin muryar sahibin nata sai taji wani farinciki ya mamaye zuciyarta Mama ce ta ce "zo ki amsa Aira hada tuntub'enta taje ta amshi wayar Ta Kara a kunne kamar wadda zatai kuka ta ce " My yaya "Ajiyar zuciya bangaren Arman ya sauke ya ce " My cutie are you okay "gyada mai kai tayi kamar yana gabanta " Alhmdll kunje lafiya ya hanya fatan baki wahala ba ko?gyad'a mishi kai tayi ta ce "Alhamdulilla " kallonsu Mama tayi zata tashi ta tafi "Mamy ta ce " Dawo ba Inda zaki gama wayar a nan "ta fad'a ta na Harararta " Chan gefe Aira taja ta tsugunna ARMAN ne ya ce "Yadai naga kinyi sanyi ko Abba ya dake ki" a a a yaya baimun komai ba su Mamy na wajen shiyasa kaji haka"ta fad'a yanda bazasuji ba "wai kina nufin a gaban Mamy muke waya kenan yanzu itama ta hakura muyi tare" murmushi tayi ta ce "Abunda nake tunani kenan Dan ko fad'a batayimun ba" Alhamdulilla Arman ya fad'a sannan ya ce "Gaskiya nayi farinciki daman ba na fad'a maki ba Ai wannan Abun da mukayi zai iya sawa suyi sanyi" murmushi Aira tayi Arman ya ce "to ban labarin ya kukayi da Abba" Kallon su Mamy tayi taga hirarsu suke ta ce "Yaya zan fad'a maka amma ba yanzu ba sai basa wajen" to yanzu ina wayarki wai Duka biyun fa basa shiga"tana part d'in Inna dukansu Idan na samu ko zuwa gobe zansa a d'auko mun sainayi chajinsu nasan mutuwa sukayi ba chaji"okay ke bazakije ki daukoba yanzu kinsan bana jure Rashin jin muryarki "Zanfada maka duka yaya sai anjima" okay bye dia take care of yourself"murmushi tayi ta ce "Don't mention my yaya" I love you my cutie ya fad'a cikin kasalalliyar murya k'asa k'asa ta ce"I love you too "tukwana sukayi bankwana Mama ta mik'awa wayar ta ce " gashi Mama "Kallonta Mama tayi ta ce " ba kince zaki ara wayarba tafi da ita"Sosa kai tayi tana murmushi ta ce "Shikenan Mama" Daman shine zaki kira kuma ya kira ko?Mamy tafada tana Harararta b'ata rai Aira tayi tayi ta ce "Ai nidai bance ba sannan ta d'auko Ameer dake k'asa yana rarrafe ya Mike zai Fard'o kayan kwalliyar dake mirror ta ce " wannan D'an naki mab'annaci ne Wlh""Ai bai kai k'afar b'arnar da kikayi ba "inji Mamy " kai Mamy nidin kuma ta fad'a tare da barin d'akin tare da Amer suna fita Mama Halima ta kalli Mamy ta ce "Kidinga janta a jiki Dan Allah inba wajenki ba ba ina zataje taji sanyi " Girgiza kai kawai Mamy tayi ta ce "Ina bakin kokarina Halima wlh ni abunda yasa ma tun farko na nuna banason tarenta dashi karya lalatamun y'a shiyasa nidai tawa addu'a ce kawai Dan wlh yarinyar nan tayi nisa yanda baki tunani" ba abunda zai faru sai alkhairi insha Allahu addua zamuyi tayi Ai nice shaida wlh yaran nan ba k'aramun so sukeyiwa junansuba ranar sunjima suna tattaunawa akan Lamarin su Aira.washegari mama Halima suka shirya zasu tafi harsun fito da kayansu Aira sai magiya take abar Hafsat itama Hafsat din tana so a barta Mama ta ce "a a a ita takemun aiki wlh itace k'arfin aikin gida kunsanni ba maid house nake daukaba " Mamy ta ce "kedai kin k'iwace wlh Halima ki barta ta d'an huta ko sati biyu ne" Dariya Mama tayi ta ce "bazakiganeba wlh Ban iya aikin gidan nan ni kadai anma zatazo kwanannan"Yaya Umar ne sukayi sallama shida matarshi Kallon Mama yayi ya ce "Mama badai tafiya ba" wlhko babana wucewa zamuyi wai"Kallon Hafsat yayi ya ce "Amma ba da ita ba zaki tafi ko" Dariya tayi ta ce "Tare " haba Mama Ki barta mana ta kwana biyu wai meyasa bakyason barinta tana zumunci"Mamy ce ta ce "kaima dai ka fad'a " Hafsat ce ta ce "Dan Allah Mama ki barni ko 1week ne nayi" Mamy ce ta amshi Jakarta ta kaya ta ce "mun rinjayeki ba Inda zata " Dariya Mama tayi ta ce "Ai dole ma na barmuku ita Anyimun chaaa Hafsat sai murna take Ita da Aira Airace ta rad’a mata ta ce " wai Sis bakiga yanda yaya Umar ke kallonki matarshi sai Aiko miki harara take"Dariya Hafsa tayi ta ce "Kai Aira sharri Juyawa sukayi suka koma ciki Mama Halima ta tafi. Washegari Wajen la'asar kasancewar girkin Mama ne gashi Y'ar aikinsu batajin dad'in bata zoba Mama ta shiga kitchen tana girki Khady tana ganin yanda take aiki da zirga zirga ko Sannu batacewa Mama ba bare har ta tayata " Itako Mama bata damuba Dan ta saba Aira ce ta Hafsa suka fito palour suka zauna Sukace "Sannunku da hutawa Yaya" Yawwa Y'ar Inna Sosai Umar ya dinga Jan Hafsa da Hira Khady ta cika tayi Fam Airako Kad'an Ya hana tayi dariya hakan yasa take tsunkunin Hafsa akan ta k'ara chusa mata Haushi itama Hafsat da Jan magana tashi tayi taje kujerar kusa dashi ta ce "Yaya please ka kaini naga gari Dan na shaida nazo Hutu nima" Cike da farinciki Umar ya ce "Aiko yanzu zaki shiga gari kanwata jeki shirya" Khady ce ta mik'e cike da b'acin rai Ta ce "wannan wani irin iskanci ne to ba Inda zaka kaita wlh ta tari napep mana ta hau inbanda tsabar iskanci ka tashi mu tafi ni gida nake so muje mu huta da bakazoba da wa zai kaita " Bata fuska Umar yayi ya ce "Meye haka Khady banson iskanci gaban yara idan gidan zaki ga hanya nan ki tafi ko dole saidani" Aira me zatayi inba Dariya ba hada durk'ushewa Amma kasa kasa take yanda bamaiji Hafsat ko itama ji take kamar ta fashe da dariyar Aira Dan ta k'ara chusa mata Haushi ta ce "Haba Aunty ki bari mana ya kaita bakuwace kafin su dawo ma Kinga kin
Chapter 27 · 0% Book details