Sashe 87
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read
a ranta saida aka kwantar da su na kwana biyu kafin a sallamesu. Kwana Ukku Aira tayi wanka Wanda ta fara salla daman Ka idar AL adartane kwana Ukku ko hud'u Daga ranar suka d'ora sabuwar rayuwarsu daga Inda suka tsaya batare da haufi ba soyayyar da Aira da Arman suke zubawa taban mamakice wacce zan iya cewa tsawon Rayuwata bantaba ga masoya masu k'aunar junansu irin haka ba ranar Friday tanayi Aira ita da kanta ta shiga kitchen ta girkama mijinta special food naban mamaki banda drinks da ta harhada da kanta Bayan taci gayunta cikin K'ananan kaya jiens da wando Sosai tayi wutar kyau Fitowa tayi a lokacin da yake shigowa Bayan yadawo daga masallacin Juma a wajenshi tayi tare da Rungumeta ta ce " highly wellcome my husband"Shafa kanta yayi ya ce "Thnks my Prince's" Kama hannunshi tayi ta ce "Muje ciki nasan ka kwaso gajiya a tare suka shiga ciki Ta taimaka mashi ya sake wanka Inda ya shirya cikin K'ananan kayan da sukayi mashi masifar kyau kai tsaye dining suka nufa tayi serving d'inshi tana murmushin ta Shima murmushin yak'e sakar mata na so da k'auna Spoon ta d'auka tare da zubo abincin takai saitin bakinshi tace ha a my honey" murmushi yayi ya d'aga bakin zuba masa tayi Arman koda ya tauna lumshe idanu yayi jin girkin da bai taba nin dad'in irinshiba da yana cewa duk duniya Mummy tafi kowa iya girki ashe Aira ma gwanace wajen girki"Ganin yanda yake lumshe ido yasanya Aira Dariya ta ce "Baby yadai mark nawa na samu" Jinjina mata hannu yayi ya ce "Ai mark d'inki ya wuce 100% saida trillion % Dariya sosai Aira tayi ta ce " a sa masa waigi"Dariya yayi ya ce "Serious fa Bantabajin girki mai dad'in wannan ba matas yayi dadi sosai yanda baki tunani kice yau dad'i biyu za Ajiyar dani gana girki gana bed ya fad'a yana kashe mata ido" Kashe mashi ido itama tayi ta ce "Yau kai din d'an gata ne Ai hero Har Arman ya gama cin abincin yana santi Da sanyawa Aira Albarka koda yasha drink dinma Shima sosai taji dad'inshi Aira ko sai dadi takeji yanda mijinta ke yabawa. A satin ne ya fara koya mata mota kullum fitarsu suke Inda ba kowa Sosai take ganewa Wanda cikin sati ukku Aira ta iya tuk'a mota inbanda in sunfitama a shiririta Rabi ake karewa shiyasanyama bata iya da wuri ba ranar ta karshe ita ta tukosu har gida Sai murna take ta iya driving Dan yana daga cikin abunda tafiso ta ganta tana driving Aira sosai takeson Arman yasaya mata waya amma tanajin nauyi Dan bazata iya rok'arshi Abu ba hakan yasa ta hakura koda yaushe cikin waya da video call suke da Mummy. Mummy duk yanda taso ta Ganar da mijin nata gsky abun ya gagara da ta ma d'auko masa maganar Arman yake dakatar da ita akwai lokacin da Kamar ya buge ta Sosai ya shiga mata bala I akan ta k'ara mashi zancen Arman ranta zaiyi mugun b'aci hakan yasa ta daina mashi Sosai Abun ke damunta d'an tama kasa samun y'ar damar da zatayi mashi bayanin abunda ke faruwa koda ta kira mahaifinta ta fad'a masa halin da ake ciki ce mata yayi karta sake mashi maganarsu ta rabu dasu akwai lokacin da yake so Akai Wanda shida kanshi zaizo ba yanzu ba sannan karta Fad'awa kowa maganar Aurensu Aira har yanzu taci gaba da rufewa. Bayan wata Ukku idan ka kalli Aira ta k'ara murjewa da kyau Ga wani fresh da take karawa ko ina na jikinta ya cicciko tayi gwanin sha awa Shi kanshi Arman ya lura da Yanda tayi kallonta yayi ya ce "Cutie Kinga kuwa Yanda kika koma baki tab'a kiba Irin haka ba" Far da ido tayi ta ce "Allah ko Honey" Shafa Hips d'inta yayi cikin wani irin salo ya ce "Serious har nanma jifa yanda suka ciko Gaskiya na iya kiwo" Dariya tayi ta ce "Allah ko hero" Eh mana Baby "Uhm Gaskiya ne ka iya kiwo nikuma Fa ban iya kiwo fa kenan kaima ai kayi kiba gashi na sanyamaka Haske kaima ka k'ara Haske"Nina isa nace Cutie bata iya kiwo ba Ai kecema kikafi kowa iya kiwo My Prince's Hh Haske nima ai na goga maki namu na Fulani Gashinan yanda kike k'ara haskawa kamar wata Daren goma sha hud'u" turo baki tayi ta ce "Uhm Amma dai nafi goga maka nau da yawa wayau ma kakemun ka had'a Haske biyu na kusa amshe abuna" Dariya yayi tare da sungumarta ya ce "ayi hakuri kar a amshe a barni na cigaba da dangwalar arziki. Sosai Arman yake lura da sauyi Daga gareta Yanzu Abu Kad'an zatayi tace ta gaji ga kwadayi da ta tarka kullum suna hanyar yawo sayayya ga bacci kamar kasa minti kadan sai bacci ya kwasheta shidai ARMAN baikawo komai a kanshi haka dai har wata guda yauma ta fito daga Bedrom d'insu Zuwa palour iskeshi tayi kan sopa yana kallo gefenshi ta zauna tare da d'ora kanta kafarashi ta ce " wash na gaji wlh kamar nayi wani aiki da yawa"Da mamaki ya Kalleta ya ce "Daga daki zuwa nan ne kika gaji ko wani aikin kikayi" girgiza mashi kai ta yi ta ce "ba abunda nayi y'ar tafiyar da nayi ce Na gaji wlh" galala yayi yana kallonta cike da damuwa ya ce "Cutie kodai Asibiti muke tafiya Nifa abunnan naki ya fara bani tsoro Kinga Inma wata chutar ce Saisu gani'turo baki tayi ta ce " um um naki Nida lafiyata qalau ba abunda ke damuna"Ba yanda baiyi da ita ba akan su tafi Asibiti takiya A haka baccima ya kwasheta a jikinshi"Kallonta ya tsayayi yana k'are mata kallo Sosai cike da damuwa Dan yana tsoron ace wani abun ne ya samu cutie d'inshi Dan baccin nan nata da kasala bana lafiya bane. Washegari Suna zaune kan Bed suna Video call da Mummy a laptop d'in Mummy Aira sai shagwaba take zuba mata akan taki zuwa ganinsu"Murmushi Mummy tayi ta ce "yi hakuri y'ar Mummy insha Allahu zanzo nan kusa" ihun murna Aira tayi ta ce "yeyeye Mummynah Allah ya kawomun ke lafiya wlh munyi missing d'inki sosai ko Yaya" ta fad'a tana kallon Arman dake gefenta "gyada mata kai yayi ya ce " eh Mummy munyi missing naki sosai "to Karku damu ina nan zuwa kusa " Bacci ne ya kwashe Aira batare da ta sani ba ta kwantar da kanta jikin Arman "Kallon Arman ta Cikin laptop Mummy tayi ta ce " son ya naga daughter tayi fresh ta k'ara k'iba da fari Jifa ana waya ta bige da bacci Anya baku b'oyemun wani Abu kuwa?cike da damuwa Arman ya ce "Wlh Mummy tayi wata hud'u ina Ganin haka tattare da ita ga bacci kamar kasa yanzu fa Rabin rayuwar a bacci takeyinta ga kasala komai tace ta gaji ni tsoroma nake Kar wata chutar ta shigarmun ita" cike da zak'uwa Mummy ta ce "wata hud'u fa kace Arman Tana zazzabi da ciwon kai ko amai?a a a Mummy batayin ko daya Saidai ciwon kan Shima ba Koda yaushe ba"yaushe rabonta da perioud" Tunani yayi sai yanxu ma ya kawo tunanin a ranshi kwata kwata cikin Sauri ya ce "Mummy ai takai wata Ukku ko fi batayi perioud ba" Salati Mummy tayi ta salamce ta ce "kudai anyi mashiririta Nifa ince Yarinyar nan Ciki ne da ita to ka maza ku shirya ku tafi Asibiti yanzu yanzu" ciki mummy"Arman ya fad'a da mamaki"Tabbas kuwa cikine da ita Ah Alhamdulilla ni Fatima burina ya cika Ka marmaza ku tafi Asibiti kuna dawowa ku kirani ku sanarmun wata nawane "Mummy tafada cike da farinciki tare da katse kiran hamdala kawai take tana godewa Allah Arman ko Sakato yayi yana tunani Tabbas shi gama zama soko wlh Sai yanzu shataf ya kawo a kanshi kodan ba sanin sign din masu ciki yayi ba cike da farinciki ya mike ya ce ''Alhamdulilla Allah na gode Maka kallonta yayi tare da shafa Fuskarta ya ce " Thnks you cutie Thnks you so much kingama yimun Komai a rayuwa sannan ya shafa Cikin tare da kissing d'in cikinta da ya d'an fara tasowa Sam shi baima lura da Hakan ba sai ya zaci ko k'iba ce ta sanyata fara tumbi ya ce "I love you so much My unborn Allah fitomun da ke\kai lafiya Farkawa Aira tayi taga Arman yana shafa cikinta Da mamaki take Kallonshi Shima kallonta yayi sai sakar mata murmushi yake " Juyamai idanu tayi ta ce "Yadai " murmushi ya sakar mata tare da mik'ar da ita ya ce 'Yau rana ce ta musamman a garemu cutie ina d'auke da Babban Albishir Wanda Ke ya kamata ki farayimun shi Amma ni zanyi maki "albishir kuma honey na me kenan" Sungumarta yayi tare da nufar toilet da ita ya ce "Wanda kika jima kina burin samu shi yayi mata wanka ita dai Kallonshi kawai take yanda yake wani sabon tattalinta da tarairayarta har mai shi ya shafa mata hatta kayan da zata sanya shiya fiddoata tare da sanya mata Bayan ya sanya mata hijab ya kama hannunta ya ce Muje my cutie" Muje ina Yaya"bai bata amsaba saboda ya fad'a mata Asibiti zasu yanzu zata kawo mashi kalula suna fita mita suka shiga ya yi motar key sukabar gidan kai tsaye wani had'adden clinic dake ba nesa dasu Suka nufa Bayan yayi parking a Farfajiyar asibitin Kallonshi tayi tare da marairaicewa ta ce "Darling me zamuyi a Asibiti kuma ?Murmushi ya sakar mata tare da kama hannunta ya ce " zaki gani my cutie yana gama fad'ar haka ya fita tare da bude mata itama ta fito kai tsaye cikin clinic din suka nufa babu wani layi hakan yasa suna shiga suka samu ganawa da likitan Bayan sun gaisa da Arman Cikin harshen Turanci yayi mashi bayanin abunda ke damunta "Itadai Aira na jinsu tayi jugum " wata nurse ya kira Tare da had'ata Da Aira yayi mata bayanin irin awon da za a mata ba jimawa Aira tadawo ta zauna Bayan an gama d'aukar abunda za a d'auka ba ayi 20 minute ba Nurse din ta dawo tare da mik'awa Dr result d'in karantawa Dr yayi