← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 127

Sashe 8

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

*********
Washegari Su Aira su na bacci Ummy ta tashesu cikin murna tace ku tashi yanzu mama ta kira Mamy ta haihu “Aira kamar an tsikareta haka ta tashi tace “da gaske Ya Ummy me ta Haifa”nima ban tambaya ba yanzu dai Mama ta kira tace da asuba ta haihu mu gyara gidan tare da Laure(yar aikin su)ba jimawa zasu dawo.

Cikin murna Aira ta tashi da dinga murna nan suka gyara gidan wajejen 12 su Mamy suka dawo gida inna dauke da jaririn mamy ko duk tayi lakwas Aira sai murna take ganin k’anin nata shima fari me kyau dan duka d’iyan Mamy su ukkun fararene Haidar ne ma baiyo hasken mamy sosai ba nan yan barka da yan uwa suka fara shigowa.

Aira ko bayan flowers ta koma domin kiran Arman taji ya tafi ko zaizo dan taga har anyi la’asr tana sand’o ta ciro k’aramar wayar da ya bata daman ta hardace number dannawa kawai tayi saitaga yamayi mata save da My yaya murmushi tayi tanajin karason Arman na ratsa kowani sassa na jikinta saida kiran ya katse kafin ta kara kira taji kiranshi ya shigo murmushi jin dadi tayi tare da kissing d’in wayar tace I love you my yaya tukwana tayi picking..........✍🏿

Manage ba yawa 😊

Share saboda Allah 👏

_*Miss Hajo ce_*🤙🏿
[5/30, 23:01] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION * 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️...............15&16

Daga dayan bangaren Arman ya ce "Hello Cutie ykk " lfyqlau yaya harka tafi ko"ta fad'a cikin sigar shagwaba "Yanzu haka ina Abuja my cutie jirgin 9 nabi shiyasa bansamu nazo nayi maki bankwana ba".

"Ayya to Sannu ya gajiyar hanya "Alhmdllh ya fad'a yace Yadai Naji kamar kina cikin farinciki my cutie Shakomun " Dariya tayi jin ya ce Wai shak'omun ta ce "Yaya Mamy ta haihu fa ".

Daga bangarenshi kamar tana ganinshi ya zaro ido ya ce "da gaske cutie Ah dole muyi farinciki me muka samu" Namiji ni nama zaci mace zata Haifa na samu y'ar uwa kawai sai ta haifi namiji"ta fada tana turo baki .

Dariya yayi har tana jiyowashi cikin waya sosai k'uruciyarta ke burgeshi komai ya fito daga bakinta fad'a kawai take cikin shagwaba ta ce " Dariya ma kakemun ko"Sorry my Beauty Kece kikaban Dariya kince ke mace kikeso ko?"Eh yaya ni mace nakeso " To yanzu shikenan tunda Mai faruwa ta faru saimuyi addu'ar idan Kikayi Aure Haihuwarki ta farko ki haifo mana mace mai kama da ke ko?wara idanu tayi kamar yana gabanta kunya duk tabi ta lullubeta ga yanda yayi maganar ya d'an kulle mata kai "Ki haifo mana?sai muyi addua?Aranta take maimaitawa me yake nufi ?

tsinkayar muryarshi tayi da cewa " Yadai cutie kikayi shiru"Uhm "kawai tace duk kunyarshi ma takeji" Shiko bangarenshi da gangan yayi mata har yanzu yana so ya furta mata Kalmar so amma ya kasa hakan yasa ya yanke shawarar nuna mata k'arara yanda zata gane ko baice yana sonta ba ta d'auko hanya.

Jin tayi shiru ya sanyashi sauya maganar da cewa"Ki d'auko mun hoton kanan namu ki turoman"Ajiyar zuciya ta sauke jin ya sauya maganar ta ce "To yaya Anjima zand'aukarma" Hango Ummy tayi na nufo wajen cikin Sauri ta ce "Yaya sai anjima Ga ya ummy nan ta maza ta katse wayar ta boye bayanta.

" Ummy ko tab'e baki tayi Dan ta ganta sarai ta ce "Kidaibi A Sannu rawar kan nan taki karta kaiki ta baroki Manya ma Abba ya bida bare ke tsirit" Aira ko kauda kai tayi ta na gunguni Saida taga wucewarta tukwana ta mik'e ta sanya k'aramar wayar a jikinta tayi bedroom d'in Mamy ta k'ara yimata ya jiki ganin d'akin da mutane ya sanya ta juya ranar duk sanda taso ta dauki jaririn hoto a wayarta ta turamai gagara tayi.

Sai washe gari wajen 11am taje gaishe da Mamy ta tarar da Ita ta na Toilet ga Alamun wanka take kuma jaririn na kan Bed shi kadai cikin Sauri ta Ruga part din inna ta ciro wayarta dake locker ta boyeta a jikinta koda ta koma tayi sa a har lokacin Mamy wanka take cikin Sauri ta fiddo wayar ta shiga d'aukar babyn hoto a snap sosai yake yin kyau.

Cikin Sauri ta bud'e data ta shiga ta turama Arman hotunan Sannan ta shiga status tayi status daman bata d'auki number kowa na gidansu ba Dan haka ba Wanda yasanma tana da waya bare har Susan tana chat tana gama dorawa ta sauka ta maza ta kira Arman tana lek'awa Kar wani ya shigo ta na kara wayar a kunne yana d'auka cikin Sauri ta ce .

"Na tura maka hoton ka hau ka gani " rikicewa tayi ganin Fitowar Mamy tayi tsaye bakin bathroom d'in ta na kallonta maza tayi cikin Rashin gaskiya ta kashe kiran Tare da Boye wayar a bayanta "Wace waya ce na gani a hannunki?ta tsinkayi muryar Mamy " .

kafin kace me idonta sun cika da hawaye ta fara in ina karya ma take so tayi abun bata saba ba ta kasa "Mamy ta daka mata tsawa ta ce " nace wayar uba waye na gani hannunki mik'omun wayar Mamy ta fad'a ta na nufota Tashi tayi tana ja da baya ta ce"I m sorry Mamy bazan Sake ba"me nace kinyi da zakice bazaki sakeba kuma wlh na k'ara magana baki mik'omun wayar nan ba zanmiki abunda baki tunani"Tuni Aira ta fara Kuka.

tsawa Mamy ta k'ara daka mata ba arziki ta mik'a mata wayar ta na yayyarfa hannu kamar wacce aka daka "jujjuya wayar Mamy ta fara cike da mamakin ganin wannan tstsadar wayar Dan taga a Instagrams ana tallarta kudinta sun haura 700k " Kallon tuhuma ta kalli Aira dashi ta ce "Wayar wacece?Tawace Mamy Dan Allah kiyi hakuri kar Abba yaji " .

ta fad'a cikin kuka "Salati Mamy ta rafka ta salamce ta ce " Na shiga Ukku ni Rahama Aira lalacemun kikeso kiyi Ki rik'e har wayar kusan 1 million a gidan nan batare da sanin kowaba Aira kunyata ni kikeson kiyi uban wa ya baki wayar wannan me tsada kuma banason kimun k'arya wlh kika kuskura kikamun k'arya saina lillisaki kuma na kira babanki na fad'a mashi maza fad'amun ubanwa ya baki yanzunnan " Tuni cikin Aira ya fara d'urar ruwa kuka ta k'ara fashewa dashi to ita me za tacewa Mamy Arman zatace ya sai mata kowa ..........✍🏿

*Tofa Fans ku taimaka ku bawa Aira shawara ta shiga matsala wa zatace ya saya mata waya 😰😢gaskiya ni harta bani tausayi*

*_Miss Hajo ce_*🤙🏿
[6/1, 18:30] Hajo: 🍏 *NI DA YAYA ARMAN* 🍏
Hot love story♥️🔐

```MALLAKAR```
*Hajara L Sadeq*

📚 *JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION* 📚

بسم الله الر حمن الر حين

*BOOK ONE*📔
🅿️...............17&18

......Bazaki d'aga baki kimun magana ba dukanki nayi da zakumun kuka"Mamy ta fad'a cikin b'acin rai" Aira ko kuka kawai take ta na yarfe hannu Dan tasan Mamy bata fiya mata haka ba Dan bata iya b'acin raiba.

"Okay bazaki fad'amun ba kenan tunda ni kin rainani bari na kira Abbanku saiki yi mishi bayani ta fad'a tana d'auko wayarta" Aira kamar wacce aka zabura haka ta zabura tareda Rugawa wajen Mamy ta rik'e hannunta ta na kuka ta ce "Mamy Dan Allah karki fadamashi zan fad'a maki wlh y'anzu Yaya Arman ya sayamun"

ta k'arasa fad'a ta na hawaye" Arman?Mamy ta maimaita tana mata wani irin kallo,Saurin sakin hannun Mamy tayi tare da ja da baya ta ce "Dan Allah Mamy karki dakeni bazan sakeba" Arman Mamy ta k'ara maimaitawa zaunawa bakin gadon tayi tana jujjuya wayar na y'an sakanni kafin da d'ago ka kalli Aira dake tsaye tana kuka ta ce "Shi Arman d'inne zai sai maki wannan wayar a wani dalili?Wlh Mamy shi ya sayamun".

" chabd'i Mamy tafada tukwana ta ce "Fad'amun yanzunnan wace alak'ace ke tsakaninki dashi Dan ubanki ,meye ke tsakaninku " Mamy wlh ba komai kawai zumunci muke dashi Mamy kin mance Yaya na ne fa"Ubanki ke da yayan Duka su sauran y'an gidan ba y'an uwanshi bane ko ke kad'aice y'ar uwarshi alak'ar dake tsakaninki dashi suma haka take su me yasa bai saya musu wayar ba saike kad'ai ya zab'a ya sayawa".

kasa tayi ta kanta tana hawaye ta ma rasa wace amsa zata ba Mamy "koma meye ke tsakaninku ai zamuji sannan ki gaggauta mayar mashi da Wayarshi muddin kina gujin b'acin raina marar jin magana kullum kinfison ki dinga jawomun magana yanzu da Abbankune yaga wayar nan da ni kaina basaikinjamun ba ki mayar mashi da Wayarshi ko ki kiramunshi ni nafada masa yazo ya Anshi abunshi bansan d'iyan iskanci idan kuma ba haka ba sainayi kwatsakwatsa da wayar".

cikin Sauri ta d'ago ta ce "a a a Mamy wlh bama saikin kirashi ba zan mayar masa da yadawo insha Allahu nagode da bazaki fad'awa Abba ba " Tsaki Mamy taja ta mika mata wayar tare da d'aukar jaririnta da ya fara tsala kuka Aira ko cikin Sauri ta amshi wayar ta sakata A siket ta fice daga bedroom d'in ta na fitowa palour ta tarar da Ya Umar da matarshi (Babban yayansu ss ne ya na aikine a Kebbi tare yake tafiya da matarshi khadija sai idan sunzo su sauka gidansu))cikin murna tace Lah ya yaushe kukazo"Murmushi yayi ya ce "Yanzu muka Iso little sis " sannunku da zuwa yaya Anzo lafiya ya hanya "Alhmdllh ya Rashin ji ya na nan ko yayi sauk'i " Dariya tayi ta ce "Yaya ai ni bana Rashin ji " Zadai kidaina y'ar gidan Inna "kallon Khadija tayi ta ce " .

Ina yini Aunty"Lafiya qalau "ta fada a takaice tab'e baki tayi Dan daman Chan haka halin Matar Yayan nasu take ba mutuncin kirki ya isheta ba shiyasa ma ko gidanta basa zuwa " Bari naje na fad'awa su Mama kunzo ".
Chapter 8 · 0% Book details