Sashe 44
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 7 min read
jin zuciyarshi yake kamar zata rabe gida biyu dak'yal Mummy ta samu ya shiga gida cikinsu babu Wanda ya kuma yiwa magana Ranar kamar wani zararre haka ya koma ba um ba um um ga wani zazzabi da ya rufeshi lokaci guda Sosai Mummy ta shiga tashin hankali Kwantar dashi tayi a d'akinshi lallashi da nasiha ba irin Wanda Mummy batayi ba Amma a banza ko tanka mata baiba wajen karfe goman dare ganin har yanzu Arman yaki magana ya sanya Mummy fashewa da kuka ta ce "ya kakeso nayi Arman karka sanya rayuwarka cikin wani hali please kaikad'ai nake dashi " Shima fashewa da kuka yayi tare da Rungume Mummy ya ce "Shikenan Mummy yanzu ya rabamu Mummy me yasa kikaje wajen me yasa zakice na bar mashi ita su tafi Mummy why ina sonta sosai itad'in rayuwata ce Mummy ko kema kin daina sona kamar Daddy duk Wanda ya rabani da Aira mak'iyina ne Mummy na tsani Abbanta bana kaunarshi ya rabamu.....ya k'arasa fad'a yana rushewa da matsanancin kuka Itama mummyn kuka take ta ce " ka nutsu son ina sonka sosai kawai Inajin takaicin irin wulakancin da ake makane a sabo da ita shiyasanya nace ka rabu da ita nafi kowa sonka tare da ita Arman Amma tunda mahaifinta bayaso ka hakura da ita shi yafi Allah zai musanyama da wacce ta fita Alkhairi a lokacin da naje wani D’an sanda ne ya kirani yace nazo ba lafiya shiyasama harka ganni “Mummy babu wacce tafi Aira a duniyar nan ki daina fad'ar haka ni ita kadai nakeso kuma ita kadai zan iya rayuwa da ita Mummy mutuwa zanyi ya k'arasa fad'a yana rushewa da kuka Mummy Lallashinshi sosai Mummy ta shigayi amma ya dinga mata sabbatu Daddynshi ta kira ta fad'a mashi halin da ake ciki tsaki yaja yace "ki rabu dashi indai akan mace ne yake wannan haukan ni kaina mahaifinka bazan tab'a yarda ka aureta ba baka isa ka aurarmun jinin Rahama ba duk na kyale kane ka gama haukan naka kuma yayimun daidai da ya rabaku kuma zai mata Aure Kamar yanda mahaifinta ya isa da ita zai mata Aure to haka nima indai na isa dakai Bazaka k'ara sati biyu ba batare da na maka Aure ba " yana gama fad'ar haka Daddy yayi waje Arman sosai ya k'ara burkicewa Mummy ya zame mata kamar wani Mahaukaci dak'yal ta samu ta kira family doctor d'insu yayi mishi allurar bacci Saida bacci ya daukeshi hankalin Mummy ya d'an kwanta gefenshi ta zauna tana hawaye tayi tagumi sosai ta tausaya halin da tilon d'an nata yake ciki. Daren ranar Aira bata rintsa ba kwana Tai tana kuka tana jin daman mutuwa tayi ta huta washegari koda ta tashi batayiwa kowa magana ba ko kukan ta daina Dan tuni ta sik'e duk yanda akayi da ita tayi magana takiyi kowa yazo Saidai tayi mishi banza wajen k'arfe Goma da wani Abu yayar mamanta Fadila ta shigo Tare da farfesun Kaza a plate da tasha had'i zaunawa tayi tare da Kallon Aira ta ce "maza maza y'ata ki cinye wannan kinji Wai Yama za ayi Ace Amarya ba gyara ba dilka ba komai har yau d'aurin Aure Amshi ki cinye wannan muje na had'o maki ruwan wanka " Wani irin banzan kallo Aira ta wulla mata Tare da Amsar Farfesun ta watsa mata shi a jiki dukanshi ga zafi"Fadila saida tayi ihu Dan sosai zafin ya shigeta cikin tashin hankali ta mik'e tana yarfe hannu Tace "Aira ni zaki k'ona koma nace kika k'ona tsaki Aira taja tare da tashi tayi hanyar waje Aunty Maryam ce dake d'akin tace " waike Baki da Hankali yayar mahaifiyartaki zaki yiwa wannan wulakancin"itama harara Aira ta galla mata tare da Jan tsaki tabar d'akin Fadila koda ta koma sosai yayyun Mamy suka shiga yi mata Dariya Aunty ramlat tace "daman wa ya kaiki in banda kinibibi irin naki" Dariya Mama Halima tayi ta ce"Ai saida nace ki rabu da ita wannan kiyi waje kawai ki ajeta Muma ido muka zuba mata Aira tana barin d'akin daman dakin Mama ne Chan ta kwana Dakinsu ta koma Tare da buga uban tagumi K'arfe d'aya da wani Abu aka d'aura Auren Hajara Abubakar tare da Angonta Alhaji Yusuf Madugu sokoto Wanda ya samu halartar manya_manyan mutane Dan Alh Yusuf Shima ba k'aramun attajiri bane haka Abba a masallacin Juma a aka D'aura Auren Arman na kwance Bayan ya tashi lokaci guda harya rame Mummy ta sanya mishi pillow a bayanshi tana bashi tea a baki Wanda dak'yal ta samu yakesha saida tayi kuka ta samu ya fara sha a plasma din dake manne a d'akinshi tashar da suke kallo suka ga An nuno D'aurin Auren Inda d'an jaridar yake cewa "Alhmdllh a yaune Ranar Juma a aka d'aura Auren Alhaji Yusuf Madugu Shahararren d'an kasuwar nan tare da Amaryarshi Hajara y'a ga Former Senate Alhaji Abubakar Umar.......ai Arman bai k'arasa jin sauran maganganun ba ya nemi numfashinshi ya rasa Mummy na bashi tea taji ya fara tari da wani irin Abu kuka ta fashe dashi tace " na shiga ukku me zan gani haka Arman "Kafin ta k'arasa maganar sai gani tayi jini yana fito mai ta hanci ta baki wani uban k'ara Mummy ta saki tare da rugawa tayi waje cikin tashin hankali ma aikatan gidan suka taryeta tare da Daddy da ya shigo ta kasa magana sai d'akin da Arman yake take nuna musu Cikin kid'imewa Daddy suka nufi d'akin sosai suka shiga tashin hankali ganin halin da Arman ke ciki gudajen jini kawai ke fitomai shi kanshi Daddy cikin rud'u dukda nauyin Arman haka ya sungumeshi cike da tashin hankali Mummy Da Abba sukayi waje Driver Ya fiddo mota tare da Security Aka nufi Asibitin Dr Aminu kano dashi Aira na kwance Wajen karfe biyu zuciyarta banda Bugawa babu abunda take ita kadaice a dakin Haidar ya shigo da shirinshi hada babbar Riga ya ce " ya Aira har an d'aura aurenki yanzu ma daga wajen d'aurin Auren muke kamar wacce aka zabura haka ta mik'e ta ce "whattttt ?ja baya Haidar yayi Dan sosai ya tsorata ganin yanda ta mik'e a zabure a matuk'ar tsawace ta ce " get out fita ka bani waje"Cikin sauri Haidar ya fice Dan sosai ya tsorata yanda tayi maganar saikace mai iska yana fita Aira ta mik'e tare da d'ora hannu aka ta ce "Shikenan na shiga ukku " sai kuma ta sauke hannunta Tare da Saukowa daga gadon dube duben fiya_fiyarsu da suke ajewa saboda kashe k'wari ta fara duk ta barbaza kayan d'akin Chan ta hangota k'ark'ashin Gado cikin Sauri ta d'auko tare da bud'e kwalbar ta kafa a bakinta Saida ta kusa Shanye Rabin kwalbar Haidar yana fita da gudu ya ruga d'akin Mamy yace Mamy ki taho kije kiga ya Aira kamar mai iska Da gudu Mama Halima da Mamy Tare da sauran mutanen dake d'akin suka fito a guje sukayi d'akin nata Mamy da Mama Halima suka fara shiga suna shiga suka sameta yashe a k'asa kumfa na fitowa daga bakinta A guje Mamy tayi kanta tare da fasa ihu tace "na shiga ukku Aira meye haka ki tashi karki mutu" Saurin duba kwalbar dake hannunta su Mamy sukayi Mama Halima cikin tashin hankali ta kwankwale kwalbar a hannunta dubawa tayi ta shinshina taga fiya fiya ce Salati tayi ta ce "Munshiga Ukku Ta kashe kanta fiya fiyace Tasha ku duba kwalba guda Kad'an ta rage warce kwalbar Mamy tayi cikin tashin hankali ta duba sakin kwalbar tayi tare da girgiza Aira kuka kawai take tace " Shikenan Alhaji hankalinshi ya kwanta ya kashe mun y'a ya ja ta kashe kanta ta mutuu"ta k'arasa fad'a tare da Rungume Aira da kumfa ke fita daga bakinta ta fashe da kuka Mama Halima ce cikin kid'imewa taje ta fiddo mota Dan Abba har lokacin suna wajen d'aurin Aure Mama ko cikin tashin hankali ta amshe Aira dake hannun Mummy ta sungumeta sukayi waje "ina zaku kaita kuma ku barmun ita tunda ta mutu hankalinshi ya kwanta ya kashemun y'a Mummy ta fad'a tare da bin Bayan su Mama Rikota yayarta Ramlat tayi ta ce " kiyi hakuri Asibiti za akaita a tabbatar da in mutuwarce tayi"Basuyi Aune ba sai ganin Mamy sukayi ta sulale a wajen summammiya Aira ko cikin tashin hankali Mama ta sanyata mota Ta shiga ta rik'eta Mama Halima tayiwa motar key kai tsaye asibitin doctor Aminu kano suka nufa da ita.........✍🏿