Sashe 123
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 2 min read
sanyi sosai nasihar bappa tayi tasiri a cikin zuciyarsu hada masu hawaye Daddy ne ya Mike tare da zuwa ya Rungume d'an uwan nasa ya ce " Ka yafemun Yaya nasan Nafi kowa laifi a al'amarin nan da banyi tawakkali na barwa Allah komai ba Tun ba yanzu ba nayi nadamar k'iyayyar da muka kulla Nayi tsantsar nadama a rayuwa Dan Allah ka yafemun Har yanzu ina sonka ina maka soyayyar da muke yiwa juna tun yarinta "Rungume Dan uwannashi Shima Abba yayi sosai yanajin tsananin soyayyarsa na dawo masa ya ce " Ni zan nemi yafiyarka na fara yi maka laifin da nayi d'an uwana na fika nadamar abunda nayi a rayuwa nima ina neman yafiyarka ka yafemun "Daddy harda hawayen farinciki ya ce " Na yafe maka duniya da lahira Dan uwana Allah yafe mana tare "Nima na yafe maka duniya da Lahira " Sosai suka k'ara Rungume juna sunajin wata nutsuwa na shigarsu wacce rabonsu da ita harsun manta Sosai mutanen dake palourn Sukayi farinciki Hada Masu hawayen farinciki Kowa Alhamdulilla kawai yake fad'a Arman ma Da Aira nauyayyar Ajiyar Zuciya Suka sauke a tare suka kalli juna suka sakarwa juna murmushi Da Hannu Aira Ta jinjinawa Arman alamar jinjina "Kashe mata ido d'aya yayi" Dariya tayi tare da K'asa da kanta Farincikin da suka shiga b'ata bakine Bayan an tsagaita Bappa ya ce........✍🏿