← Book details Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 127

Sashe 53

Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read

......Tare da shiga da k'afar hagu girgiza kai Mama Halima tayi batare da tace mata uffan ba harsuka shiga cikin gidan itadai Aira idonta lullub'e yake sai yanda akayi da ita tana ta jin bud'ar mata har aka shiga da ita tana jin an zaunar ita ta tabbatar da an kawota d'akinta kenan sosai ta fashe da wani irin kuka mai cin rai wai yau itace aka kawo d'akin miji amma mijin ba yaya Arman ba wannan wace irin yankan k'auna ce sosai ta fashe da kuka yayyun Alh Yusuf da suka d'aukota saisuka d'auka kukan rabuwa da gida ne Lallashinta suka shigayi sukace "ki kwantar da hankalinki insha Allahu mudin zamu zame maki tamkar iyaye" Mama Halima ce ta rada mata a kunne ta ce "Karna sake Naji ko kin nuna bakisan Auren nan ko kiyiwa mutane rashin kunya ki saki jikinki kinji kibar kukan nan" gyad'a mata kai Aira tayi Alamun to ta daina kenan sosai dangin alh yusuf suka tarbesu da tarba ta musamman abinciccika kala kala wata yayar Alh Yusuf tazo ta ce ya kamata Aje a kaita wajen uwar gidan A had'a su "Sosai gaban Aira ya fad'i " to Mama Halima ta ce "Sannan suka kama hannun Aira suka tafi da ita bangaren uwar gida Suna isa suka isketa ita da Y'ay'anta da y'an uwanta sai cika suke suna batsewa Hakanan suka zauna gaishe da Matar sukayi wacce zatakai sa annin Mama Ta amsa ciki ciki Mama Ramlat ce ta ce " Amarya muka kawo miki y'ar uwa Amana dan Allah ku hada kanku sannan ita munyi mata nasiha insha Allahu Zata girmamaki "Tab'e baki Hajiya saudatu tayi ta ce " Wanda ya kawota zaku ba Amanarta ba niba sannan zaman lafiya za ayishi indai ta zo dashi"Sosai gaban Aira ya tsananta fad'uwa jin kalaman Matar a zuciyarta ta ce "Na shiga ukku an kawoni wajen wata matsalar nidai ina ganin rayuwa" Su Mama Halima sosai ransu ya b'aci tashi sukayi tare da Aira batare da sunce uffan ba yayar Alh Yusuf Hadiza ta ce "kedai saude baki da mutunci wlh iyayen yarinyar nan fa y'an mutunci ne ba da tashin hankali sukazo ba Amma abunda kika fadamusu kin kyauta kenan" Tsaki saude taja tare da tashi tabar palourn Ana komawa da Aira a lokacin ana kiran Sallar magriba sai sannan ta daga idonta ta kalli d'akin dakine babba na gani na fad'a ga kuma tantsara tantsaran kayan da aka zuba mata karewa d'akin kallo tayi Sosai Tasan Abba ya kashe mata kudi a kayan dakinma kansu dukda bataga sauranba Sallah ta tashi tayi suma su Mama Halima sukayi salla Bayan sun. Gama sosai suka shiga yiwa Aira nasiha gami da wa azi akan ta zauna da kowa lafiya kuma tayiwa mijinta Biyayya Allah ba ruwanshi da bakisan auren nan zai kamaki da laifi Aira na jinsu yanda suke fad'a mata maganar na shiga kunnenta haka take fita ta d'ayan kunnen Sannan suka Mike sukace Zasu koma Dan dama ba kwana zasuyiba fly din dare zasubi sosai Aira ta fashe da kuka ta rirrikesu ta ce "Dan Allah Mama Karku tafi ku barni na shiga ukku kuma yanzu Tafiya zakuyi...sosai take kuka su kansu su Mama Halima saida ta sanyasu kuka Dak'yal kannen Alh Yusuf suka bambare Aira dake jikin Mama Halima tana kuka harsuka tafi Aira ihu take tana kukan karsu tafi su barta dak'yal y'an uwan mijinta suka dinga Lallashinta harsuka samu tayi shiru nan mutane da y'an uwa suka shiga shigowa ganin Amarya Aira in banda hawaye ba abunda take wajen karfe goma Wata kanwar Alh ta sanya Aira tayi wanka ta shirya cikin tantsanemen lace d'inta da tasha d'inki ta sanya mata Turare sosai dukda hawayen da Aira take sosai tayi kyau Saida ta gama shiryata tukwana ta mik'e ta ce " to nima na tafi yanzu ba jimawa angonki zai shigo Allah ya bada zaman lafiya "Aira bata iya ce mata komai ba saboda k'ududun bakin cikin da take ciki tana ganin fitarta ta maza taje ta sanyawa k'ofar key tare da barin key din a jiki Da gudu ta fad'a Gado tare da fashewa da kuka mai cin rai tunanin Arman yaki barin kwalwarta Alh Yusuf da murnarshi ya taho bangaren Amaryarsa sai fara a yake tare da ledarshi katuwa yana zuwa ya yi knoking yaji rufe sosai ya shiga Bugawa Aira na jinshi tayi banza ta kyale sai kuka take key ya d'auko ya gwada bud'ewa amma ya kasa hakan ya nuna mai tabar key din jiki kenan sosai ya damu cikin k'asa da murya ya ce " Haba Amaryata ki bud'e mana nasan kina jina please ki budemun kofa kinji"Aira na jinshi tsaki taja tare Kara fashewa da kukan takaici cike da damuwa.Alh Yusuf ya ce "Da Allah na had'aki baby ki bud'emun k'ofar please" cike da jaraba da masifa Aira ta ce "Bazan bud'e d'inba karka dameni Malam Karka takurawa rayuwata tun da sauran mutuncinka a idona bazan bud'e ba Saidai ka kwana a tsaye " tana gama fad'ar haka ta fad'a Gado tare da cigaba da hawaye"Alh Yusuf bai hakuraba haka yayi ta tsayuwa a wajen yana bubbuga mata ko Allah zaisa ta bud'e Hajiya saude ce ta fito cike da masifa ta ce "Da Allah Alhaji ka damemu meye hakan da kake ko kunya babu tunda tak'i bud'e maka ai sai ka hakura Amma wannan Abun da kake zubda girma ne y'ay'anka na jinka wannan wace irin jaraba ce " ta fad'a ta na Jan tsaki "Kallonta yayi ya ce " kinsan dai bansan katsalandan ko saude"to Naji yanzu dai kayi hakuri kaje ka kwanta "Ba tare da ya ce komai ba ya juya ya nufi part d'inshi tsaki saude taja tare da komawa Bedroom d'inta !*Asalinsu*??Alh Yusuf Sanannen d'an kasuwa ne a nan Jahar sokoto da ma ketaran ta Matarshi d'aya Saudatu yar asalin Garin sokoto ce yaransu hud'u Babbar d'iyarsu Zuhura tana nan tana aure anan sokoto yaranta hud'u sai mai biya mata Abubakar Sadiq shi har yanzu baiyi Aure ba,sai Mubarak shi kuma yana matakin Deegree ne anan Sokoto yake karatu sai Autarsu Laila me shekaru Ashirin da d'aya a duniya tana matakin Deegree level 2 Hajiya saude sosai take juya Alhaji sai yanda tayi dashi tunda suke da ita bai tab'a yunkurin ma Kara Aure ba Dan sosai yake shakkarta irin matan nan ne jibga jibga masu jiki da k'iba itama bak'a ce koda Alh zaiyi Auren nan sosai aka sha dagu da ita Dan y'ar bala'i ce suko danginshi daman so suke ya k'ara Aure hakan yasa suka k'arfafa abun tayi shige da ficen ta wajen malamai da Bokaye amma ba nasara Y'ay'antama sosai suke takaici da bakincikin auren da Daddynsu zaiyi musamman Zuhura da laila dan Sadeq baya k'asar shiko Mubarak ba ruwanshi Dan irin y'an duniyar nan ne shiko Alh Yusuf da yake Allah ya d'ora mishi k'auna da soyayyar Aira hakan yasa ko girgiza baiba sai ya jima tsoron Matar tashi da yake ya ragu wannan kenan.....Daren ranar Aira kwana tayi batayi bacci ba kwanan bak'inciki tayi Bayan tayi Sallar asuba wani masifaffan zazzabi ya rufeta da ciwonkai cikin bargo ta shige sai rawar sanyi take hawaye na bin k'umcinta a haka har wani wahalallen bacci ya kwasheta....k'arfe Tara tayiwa Su Mama Halima a Kano Kai tsaye gidan Abba suka sauka suna isa nan ne suka samu labarin Tafiyar Mamy Dafe kai Mama Halima tayi ta ce "ohh muna ganin rayuwa wlh harna gaji da kashe kashen case nidai gobe zan tafiyata Nida garin nan kuma sai an ganni " Aunty Ramlat ko sosai taji haushin Mamy Abba ta samu ta ce "Dan Allah Alh kayi hakuri insha Allahu zamuyi mata fad'a zata daina sannan ina neman Alfarmar da ka bani na tafar mata da yaron insha Allahu kome mukayi gobe zaka jimu" Jinjina kai Abba yayi ya ce "Bakomai Ramlat amma yaron ki barshi a nan tunda ta iya tafiya ta barshi a tunaninta ko bazan iya Rikesu bane ko me gwara ki barmunshi " dak'yal Dai ta samu har Abba ya sauko ya ce "ta tafi da Amer d'in a tare da Amer Aunty Ramlat suka tafi gidan Yayansu suna zuwa sosai Aunty Ramlat ta shiga yiwa Mamy fad'a Inda ta shiga batanan take fita ba itadai Mamy batace uffan ba Hamdalarta d'aya kawai da Ta amso mata Ameer Dan tunda ta taho shi kawai take tunani " Kiyi Hakuri Aunty Insha Allahu hakan bazata k'ara faruwa ba ya hanya kunsha hanya "Allah sa hmm hanya Alhmdllh Aira dai ana Chan gidan miji" Badai taci gaba da kukanba Aunty "Kuka kuma da sauki to amma har muka taho tanayi" Goge hawayenta Mamy tayi ta ce "Amma Aunty kina ganin ba matsala gida d'aya aka had'asu da kishiyar?tab'e baki Aunty Ramlat tayi ta ce " to da sauk'i dai za ace Amma banga Alamun mutunci a tattare da wannan kishiyar tata ba ga Aira ba Wayau ba dad'in abun kawai da dangin mijin da mijin na sonta sun hana Wani abun Amma a yanda naga Alamun kishiyar nan da yaranta banga Alamun arziki a tattare da su ba "Innalillahi Mamy ta fad'a tare da Fara kuka ta ce " wlh Alhaji ya cuceni kawai sayarmun da y'a ne yayi yanzu Dan Allah akwai adalci a abunnan kuwa Aunty Aira za akai uwa duniyar nan kawai kashemun d'iya ne za ayi"tsaki Aunt Ramlat taja tace "daman ban fad'a maki ba rikitacciya kawai ke Ko karar nan ma na y'an fari bakyayi wai d'iyarki da agaban wasu manyan ne zasu miki d'aukar marar Kunya ko Dan ai baki da itama ai wasu ko sunan d'iyan farinsu basa fad'a wlh " ni bawani karar y'ar fari da zanyi akanme masu yinma sun daina wahalshe da kansu ne suma suke ai maganar Gaskiya Ce nidai kawai an cucemu Allah saka mana Mamy ta fad'a tare da d'aukar Amer dake mata kuka tayi ciki Daren ranar da tunanin halin da Aira ke ciki Mamy ta kwana ko baccin kirki batayi ba....Aira ita ce bata tashi ba sai wajen 12 jiri na dibarta haka ta tashi tana tashi Wanka ta shiga tayi tana fitowa ta shirya cikin Atamfarta Riga da sicket cikin k'arfin hali ta shirya ganin ana kiran salla
Chapter 53 · 0% Book details