Sashe 93
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read
...Ka gansu nan a hannuna "Cike da farinciki Arman ya ce " Alhamdulilla Mummy kina nufin Duka yaran nan nawa ne"Lakutar kumatunshi tayi ta ce "nakane son halak malak" mik'a mata d'ayar yayi tare da sujjudul shukur Yajima yana Godiya da yabo ga ubangiji itadai Mummy murmushi yaki barin fuskarta yana Dagowa Amsar d'ayar yayi ya ce "Allahu Akhbar Mummy kamata sukayo sak" Wlhko naga Duka Kaine ni harna rikice ma Bana banbancesu Inbanda naga ta farkon tafi K'aramar girma ta haka kawai na bambance su"Hawayen farinciki suka zuboma Arman amsar d'ayar yayi tare da rungumesu gabaki d'aya ya ce "Allah yayi muku albarka yarana" cikin Sauri ya ce Mummy ina cutie tana lafiya"lafiyanta qalau muje ka ganta Mummy tafada suna shiga Inda suka tarar da Aira kwance Tana hawayen farinciki cikin Sauri Arman ya nufi gadon tare da rungume ta tare da Yaran ya ce "Thnks You so much My cutie kin gama yimun komai a rayuwa kinbani abubuwan da bazan tab'a mantawaba dasuba ked'in haskece cikin rayuwata Allah yayi miki albarka ya baki lafiya" murmushi Aira tayi tana Goge hawayenta ta ce "Ameen hero" zaunawa yayi tare da kafe yaran da idanu Inda ya shiga musu Adduo i sosai yakejin k'aunar yaran na shigarsa ta musamman Bayan yayi musu addua jin sun fara kuka ya sanyashi kallon Mummy ya ce "Ba abunda za a basu Mummy " Zamzam ta ciro tare da Dabino mai laushin nan irin na makka ta mik'a masa tace tauna musu Kad'an ka basu saika basu ruwa daga nan zaka iya musu hud'uba "hakan yayi Bayan nan yayi musu hud'ubar kiran salla Kamar yanda manzon Allah ya koyar tukwana ya rad’a musu suna Dagowa yayi ya kalli Mummy tare da Yin murmushi " Kallonshi tayi ta ce "Me ka sanya musu" Mik'a mata Hasanar yayi ya ce "ga takwararki Fatima zahra d'ayar kuma Rahama"Cike da farinciki Mummy ta amsa ta ce " masha Allah Allah ubangiji ya raya manasu sosai Aira taji dad'in sunan da ya sanyawa yaran sunan mahaifiyarshi da nata Hakan ya mata dadi sosai nurse dinne suka bukaci da Akai Aira d'akin Hutu Dan yanda tasha wahala saita huta sosai haka ko akayi ita kadai aka bari ba b'ata lokaci bacci ya d'auketa Arman da Mummy suna waje sai liliyar yaran suke Dan yanzu sunyi shiru Har sha biyun Dare sunanan dak'yal Mummy ta lallaba Arman ya koma gida Bayan ya sayowa Aira abubuwan da zataci su Kaza fresh milk fruit Da sauransu Baiso ba ya koma Dan bayason abunda zaiyi nesa da yaranshi da yakejin kaunarsu ta musamman Mummy dakinda aka kwantar da Aira ta nufa da Yaran har lokacin Bacci take ga yaran sunfara kuka Alamun sunajin yunwa Haka nan tayi ta jijjigasu Inda Hasanar ta rude da kuka Wanda kukan ya tashi Aira har cikin Ranta takejin kukan yaran ganin ta tashi ya sanya Mummy saurin zuwa tare mik'a mata ita ta ce "Kinga tund'azu ita tafi rigimar" Amsarta Aira tayi tare da Fara jijjigata tad’an lafa da kukan Amma bata dainaba Alamun yunwa takeji sanyata Mummy tayi ta fito da Mamanta ta sanya mata a baki dukda kunyar da Aira takeji Amma me babu ruwa "Cikin Sauri Mummy ta hadawa Aira tea mai kaurin gaske Mik'a mata tayi Tasha Bayan nan ta zuba mata Farfesun naman da Arman ya sayo Shima tadanci sosai Fresh milk da Malta Mummy ta k'ara had'a mata marairaicewa tayi ta ce " Mummy wlh na k'oshi" a a a Aira daurewa zakiyi kisha Dan asamu abincin yaran nan yazo Kinga sai kuka suke ki daure jin Haka ya sanya Aira saurin shanyewa "yawwa to Mummy tafada tare da cewa " to gwada bata insha Allahu ruwan zaizo yanzu"cike da jin kunya Ta Kara gwadawa Tana sanya mata taji yazo ta kama ta fara tsotsa Sosai Aira taji wani irin zafi d'an k'ara tayi tare da saurin fusgewa "Tana hawaye ta ce " Mummy zafi"Matsawa kusa da ita Mummy tayi ta ce "Daurewa zakiyi ko so kike kibar yaranki na kukan yunwa Daga yanzu bazaki sakejiba " Jin haka ya sanya Aira mayar ma da Hasana taci gaba da sha Dukda zafin da takeji haka ta daure gashi yarinyar da ancire zata hau kuka tafi minti ashirin tana tsotsa Ganin d’ayarma ta fara kuka ya sanya Mummy saurin karbeta ta ce "ba d'ayar itama Amsarta tayi itama ta fara bata tanajin tana tsotsa tayi shiru Babbar ko kuka ta fara Jijjigata Mummy tafara ta ce " Haba takwara karfa kiyi Rashin hakuri Kinji "Sosai Mummy ta shiga jijjigata Inda ta samu har bacci ya d'auketa itama d'ayar tana cikinsha bacci ya d'auketa kwantar dasu kan gadon tayi itakuma Aira ta koma gefen karshen gadon ta kwanta. Washegari safko Arman ya buga musu a lokacin Aira sunfito Daga wanka Wanda mummy ta gargasata doguwar riga ta sanya tare da zaunawa kan kujera Lokacin shigowa yayi tare da kayan break fast d'aya shirya Bayan ya zauna Kallon Aira yayi ya ce " Sannu cutie ya jikin naki"Murmushi Aira tayi ta ce "Alhamdulilla" Mummy ina kwana "Lafiya qalau son ta fad'a tana d'aukar Rahama da ta tashi don yi mata wanka Plask din d'aya shigo dashi ya Tsiyaya ruwan tea din tare da sanya madara millo da bounvita a ciki sosai yayi kauri mik'a mata yayi ya ce " Amshi maman twins kisha"Wara idanu tayi kasa kasa ta ce "Uhm harna tashi daga cutie na koma maman twins kenan" Dariya yayi ya ce "Ai Duka sunankine my cutie " Amsa tayi tare da Fara kurba a hankali Inda take hadawa da wainar kwan da ya kawo kallon Mummy yayi da take yiwa Rahama wanka yace "Sannu Mummy ga break fast d'innan a hada maki ko saikin gama" Bari dai na gama tafada tana Tsaneta a towel Dan ta gama mata "Gado taje ta kwantar da ita tare da zaunawa kan chairs din dake d'akin Arman ya had'a mata tea din itama da wainar kwai tana cikin break fast Zarah ta kwala Kuka da duk saida suka Kalleta Cikin Sauri Arman ya d'auketa tare da Fara jijjigata ya ce "Mummy ko bata lafiya?Lafiyanta qalau wlh inajindai takwarar tawa zatayi kukan banza bata ta bata Tasha " sorry my Mummy karkiyi Rashin hakuri Kinji takwararki hakuri gareta ki taimaka "Arman ya fad'a yana kallonta " Duk Dariya sukayi har Aira data kusa kwarewa ta ce "Yaya kamar irin tanajin naka nan ko" Kallonta yayi da murmushi a fuskarsa ya ce "tanaji mana ai tasan daddynta tama Cemun bazata sakeba " Girgiza kai Mummy tayi tare da amsarta ta dorawa Aira kan cinyarta ta ce "Karki biyema mashiririncinnan Bata Tasha " Amsarta Aira tayi tare fara feeding d'inta Arman ko d'aukar Rahama yayi yana kallonta tare da Fara mata wasa Kallon Mummy yayi ya ce "Wai Mummy baza a sanya Musu Nick name ba" ku zan tambaya ai me kuka zaba musu"Kallon Aira yayi ya ce "Cutie wannan zab'inkine wani suna kike tunanin za a dinga kiransu dashi? Yaya duk sunan da yayi muku nima yayimun ku zaba kawai " Mummy ce ta ce "a a a baza ayi haka ba ke zaki zabawa yaranki ne Ai tunda yayi na farkon ke kuma saiki zab'i sunan da yayi maki ko zuwa kafin suna ne Kinga sai a sanya" Kasa tayi da kanta ta ce "To Mummy " Bayan tagama bata itama Amsarta Mummy tayi itama Bayan tayi mata wanka ta shiryata Nan Arman ya shiga yiwa yaran nashi hotuna masu kyau a waya ranar aka sallamesu Bayan sun koma gida Nan Mummy ta shiga kiran y'an uwa tana shaida musu haihuwar tare da tura hoton yaran groups d'insu na y'an gida kowa sai Farinciki yake Sosai yaran tun a hoto suka shiga ran mutane murjace ta kira Aira Bayan ta d'auka ta ce "Congratulation kawata Allah ubangiji ya raya mana twins wlh Kinga Dana gansu a hoto kamar na sace Ji nake kamar nayi tsuntsuwa na taho" murmushi Aira tayi ta ce "Ai gwara ki tahoma tun wuri karsuyi fushi da Mummyn su " ah suyi hakuri ina hanyar tahowa my twins ki shafa mun kansu Sis Zadai ki bani su kyauta ko Dan wlh ina sonsu"Hasina ce tayi saurin amshe wayar ta ce "Rabu da ita sis Me ya kaiki ba wannan mahaukaciyar yara Ni zaki bawa su yanda zankula dasu " Dariya Aira tayi tanajin irin yanda suke drama A waya Bayan sunyi bankwana hotonsu tahau what's App ta tura musu tana ganin yanda suke ta status Ana hadama yaran tiktok sak daka kalli yaran zakace musu turawa grps suka bude su hudu waidan tattaunawa akan sunan Aira ce tayi voice ta ce "Manyan iyayen twins wani suna kukeganin za a dinga kiransu dashi nidai wlh na kasa ganowa Ku zaba musu suna mai dadi" Voice maryam tayo ta ce "Gaskiya kam kyanta a naima musu nick name mai dadi bari hasina ta fito itace Gwanar sanin sunaye nima ita ta zabawa hanif" Hasina ce tayo voice bayan nasu ta ce "a gaskiya inaga a kirasu da Nihal da Naila ko ya kikace sunan yayi kuma Kunga baiyi yawa Ba sosai" kowa yayi na am da sunan Hakan yasa Aira ta ce "sunan yayi sis kawai a kirasu da hakan amma yaushe zakuzo" Insha Allahu zuwa jibi mukeson tahowa tare da su goggo"Sosai Aira tayi farinciki sosai take chat da su ana raha da Hira A lokacin Aira na Gado Arman ya shigo da Rahama dake Kuka mik'a mata ita yayi tare da zaunawa ya ce "wani sunan kuka zaba musu za a bugo musu abubuwan suna "Nihal & Naila yayi ko Yaya?Wow ya fad'a tare da Jinjina mata hannu ya ce " sunan yayi mom.twins "takwarar Mummy sai a kirata da Naila takwarar Mamy kuma Nihal ko " Eh my hero ta fad'a tana feeding d'in Nihal Kallonsu yake gwanin sha wa Shafa sajenshi yayi ya ce "Kinsan me cutie" Dagowa tayi ta ce "Saika fad'a hero" Nifa mamaki nake har yanzu Wai kece da yara saina tuna kema yarintataki gani nake kamar haka kece da kina yarinya"Dariya sosai Aira tayi tare da mik'ewa ta ce "Lallai hero Allah kana maidani baya da yawa sannan tayi Farr da ido ta ce " Me yafi son ranka