Sashe 86
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 8 min read
......Sune basu tashi ba sai washegari karfe Tara Arman yayi farkon tashi Kallon Aira yayi dake baccinta hankali kwance kallon agogo yayi yaga Tara hada wani Abu cikin Sauri ya Mike yayi saurin fad'awa toilet Dan baisan har yakai hakaba batare da yayi salla ba Bayan ya gabatar da salla kallon Aira yayi yaga baccinta take har yanzu kin tadata yayi Dan yasan tana fashin salla kuma tana buk'atar Hutu palour ya fito Inda ya samu sabon kuku din da ya d'auka A palour ya tarar dashi Yana mopping har ya gama shara jinjina mashi da hannu Arman yayi shikuma baturen ya gaisheshi cikin girmamawa Bayan Arman ya amsa zaunawa yayi tare da komawa ya d'auko paper da biro ya rubuta duk wani kayan abincin da zasu buk'ata Mik'a mashi yayi ya ce "yaje ya sayo " Arman yana zaune harya dawo sosai ya shigo da jibga jibga kayan abinci Inda ya shiga sintiri dasu store din Gida har ya gama Kallonshi Arman yayi ya ce "Idan kazo da safe zaka gyara iya palourn kawai da kitchen iyanan zaka dinga gyarawa 6am ya kasance kazo ka gama sannan daka gama ta kitchen zaka dinga fita idan kana buk'atar wani Abu ka kirani a waya kawai basai ka shigo cikiba " Jinjina kai Yayi Alamun ya fahimta "Check din kudi sosai ARMAN ya rubutamai sannan ya yanke albashin da zai dinga biyanshi mai tsokar gaske daga lokacin nan kukun ya shiga kitchen ya fara aikinshi. Arman ko dayan bedroom d'in yakoma Bayan yayi wanka ya shirya d'akin da Aira take ya nufa Inda ya sameta ta fito daga wanka daure da towel jikinta hand drayer a hannunta tana busar da gashin kanta da ta wanke ta baya ya rungomata " Dan Kara Aira tayi Dan ta tsorata"Dariya Arman yayi ya ce "Sarkin tsoro nine fa" Cikin shagwaba ta ce "Shine ka tsoratani hero" Murmushi ya sakar mata ya ce "Sorry Prince's" amsar hand drayer din yayi tare da Fara yi mata "Dariya Aira tayi ta ce " Kai Zumah me ina ka iya gyaran gashi"yau xanfara akan matas kede kawai kisa ido kiyi kallo yarinya"murmushi Kawai Aira tayi suna kallon juna ta madubi shiya gyara mata kan nata yayi mata stretching ya shafa mata mayiyyuka masu k'amshi Bayan tayi mata Parking "Sosai yayi kyau sai kyalli gashinan yake ya dirar mata har gadon bayawow yaya Amma fa yayi kyau kamar naje saloon" Murmushi yayi ya ce "da kina wasa ne da mijin naki" jinjina mai hannu tayi ta ce "Thnks mijin da yafi na kowa" Peck a kumatu yayi mata ya ce "Nagode Matar da tafi ta kowa a duniya" Saida sukayi shiriritarsu nan ma tukwana ya rabu da ita ya fita palour ita kuma ta shirya Cikin doguwar rigar atamfarta green Street gown sosai ta matseta d'an a jiki D'aurin zarah buhari tayi Ita kanta data duba kanta madubi tasan tayi masifar kyau Turarruka masu k'amshi ta faffesa palour ta fito Inda ta samu Arman yana kallon ball Kallonta yayi tare da sakar mata smiles ya ce "Kinyi kyau My beautiful wife" Far da ido Aira tayi ta ce "Thnks my beautiful husband" ta fad'a tana k'arasa shigowa palour tare da zaunawa gefenshi ta zagaye hannunta a “yau shigar hausawa aka yimun kenan "Uhm hubby " Kinajin yunwa ko Prince's ya fad'a yana shafa kanta"Cikin shagwaba ta ce "Eh mana Baby " Sorry babyn Yaya muje tund'azu kuku ya gama breakfast banson na tashekime shysa"Kallonshi tayi da mamaki ta ce "Wai honey da gaske kuku ka d'auka Haba Darling meye amfanina a gidan kowace mace fa tayi Aure ita take girkama mijinta abinci meyasa bakasan na samu ladan wannan sannan nasan Mummy ma taji Bazataji dadi ba" kama hannunta yayi tare da mik'ewa suka nufi dinning ya ce "Bazakiganeba Cutie bazan juri ganinki kina wahala ba shysa Sannan lada kullum cikin samunta kike yanda kike kula dani kike jiyar dani dadi kadai ladan bata wasa bace ba saita girki bane kawai zaki samu lada akwai hanyoyin samun lada da yawa a Aure kuma girkin ma zaki samu ladar niyya tunda Kinga ninace na yafe Kinga kuwa ai kina da lada my prince's Mummy da kanta ta fara cewa Na d'aukar maki kuku"Uhm Yaya Amma dai Gaskiya ko ran Friday ne zan dingayi please karkace a a " To shikenan tunda kin ce Friday din saiki dingayi shikenan ko hankali ya kwanta"Murmushi tayi tana zama kujerar dining d'in Bud'e kulolin tayi k'amshi sai tashi yake serving d'insu tayi Inda ta zauna ta fara ci lumshe ido tayi Dan babu laifin abinci akwai dadi dukda ba irin namu bane"Kallonta Arman yayi ya ce "da dadi ko my prince's" yatsune fuska tayi ta ce "Uhm ba laifi amma da ni nayi da saitafi dadi" Dariya yayi ya ce "Ai daman inama za a hada abincin matas da wannan ai kinzarce wannan nesa ba kusa ba" washegari da Yamma suna zaune a palour suna kallo yayinda tana gefenshi tana shan tuffa Hakanan yau kawai ta tashi da tunanin Mamy kusan shekara kenan ba ta sanya mahaifiyarta a ido Dan tundaga aurenta da Alh Madugu rabonta da gida "wasu hawaye ne suka gangaro mata batare da ta sani ba "da mamaki Arman ya Kalleta ya Ce " Yadai me ya faru cutie "Cikin murya mai shirin fashewa da kuka ta ce " yaya Mamy"Ta k'arasa fad'a tana fashewa da kuka "Rungumeta yayi yana Lallashinta Ya ce " kiyi hakuri cutie komai zai daidaita insha Allahu kibar kukan nan kinsan bansan zubar hawayenki"yaya Kusan shekara fa rabona da Mamy nasan tana Chan kila cikin damuwa yaya Dan Allah kiramun ita a waya please "To yi shiru saina kira maki ita kinji" gyada mashi kai tayi tare da Goge hawayen mik'a mata wayar yayi Karba tayi tare da sanya number Mummy Cikin zumud'i ta danna mata kira cikin sa a kuwa taga ta shiga tana ringing Mummy ko tunda abunnan ya faru bata da zaman lafiya sosai hankalinta ya tashi akan Abunda akace Aira tayi kullum da bakincikin abun take kwana take tashi dukta rame yanzu haka bata da lafiya tana kwance Dan tunda abunnan ya faru yau lafiya gobe ciwo Danma Abba yana kula da ita bai nuna mata komai ba akan abunda y'arta tayi yauma tana kwance tana bacci taji ringing d'in wayar koda ta mik'e taga code din wata k'asa kuma ba na Niger ba bare tace y'an uwanta ne tayi mamaki sosai Tana shirin dagawa kiran ya katse Aira ko hawaye tayi ganin kiran ya katse Kallonshi tayi ta ce "Yaya bata dagaba"ki sake trying insha Allah zata d'aga " Sake kiran tayi cikin sa a kuwa ring d'aya aka daga wata nauyayyar Ajiyar zuciya ta sauke Wanda har saida Mamy taji daga waya Hello wake magana"Mamy ta fad'a "Sosai Aira taji nutsuwa jin muryar mahaifiyartata shashekar kuka ta fara ta kasa magana " Wai baza ayi magana ba"Mamy ta fad'a"Aira kasa magana tayi sai shashekar kuka "Mummy dukda taso ta gane ita ce ta ce " To idan baza ayi magana ba zan kashe ina da aikinyi"Cikin Sauri Aira ta ce "Mamy Aira ce" Aira Mamy ta maimaita cikin ranta dukda kewar y'ar tata da tayi hakan bai hanata fushi ba ta ce "Wace Airar" Airarki Mamy "ta fad'a tana cigaba da hawaye" tsaki Mamy taja ta ce "me kika kira na maki ai tunda kika zab'i namiji akanmu muma muka hakura dake Dan haka karki sake kirana " tana gama fad'ar haka ta katse kiran"Sosai Aira ta fashe da kuka tare da Fad'awa kan Arman ta ce "Na shiga ukku yaya shikenan Mamy Ma fushi take dani nasan k'ilama ita da Abba sun tsinemun yaya Ya zanyi da rayuwata"Sosai ta bashi tausayi Rungumeta yayi ya ce " Kiyi Hakuri Allah yana tare damu Insha Allahu babu wanda zai tsine maki cutie anringa an b'ata mu a wurinsune Wanda Goge hakan sai Allah insha Allahu nan gaba Gaskiya zata bayyana zasu yafe mana "cikin kuka ta ce " yaya sai yaushe Nifa Duka iyayena suke fushi dani ina tsoron hakkinsu yaya karya bibiyeni nasan ban kyautawa Mamy ba "daddabata ya fara ya ce " Insha Allah ba hakkin da zai bibiyemu cutie Allah da zuciya yake amfani kuma shi ya jarabcemu da son junanmu Wanda Bazamu iya rabuwa da junanmu ba Amma kina gani Iyayenmu saida sukayi yanda sukayi suka rabamu akan dalilinsu marar ma ana da tushe Sannan Abba da Daddy suma Allah zai fara kamawa da laifin yanke zumuncin da sukayi Bayan nasu suka hada da namu kin manta hadisin manzon Allah S a w da yake cewa "dukkan mai yanke zumunta bazai shiga aljanna ba " bana nufin iyayenmu bazasu shiga aljanna ba a a a ina nufin girman laifinsu yafi namu na farko dai Kinga ba zina muka aikata ba hasalima sharri akai mana"Sannan na biyu Aure da Mukayi ba haramun bane inbanda Lada da zamu samu saboda raya sunnar ma aiki da mukayi ko a mutuwar auren wancen ya isa ki gane Allah yana tare damu cutie sannan ki kwantar da hankalinki Mamy uwace bazata tab'a maki mugun bakiba Kinga kamar yanda Mummy tayi tsayin daka wajen ganin farincikinmu to hakan take ta bangaren Mamy itama uwace kuma har yanzu tana sonki kuma tanayimiki addu'ar alkhairi kisa wannan a ranki kinji my cutie ki kwantar da hankalinki "Shiru Aira tayi tana sauke ajiyar zuciya Tadanjin sauki a ranta nan yaci gaba da yi mata nasiha har ya samu ya mantar da ita damuwar da ta shiga. B'angaren Mamy kuwa sosai tayi kuka Bayan katse kiran Sosai Abun yake damunta ga kuma bakincikinta na bin namiji da Y'arta tayi kenanma barin k'asar sukayi tunda gashi da code din wata k'asa Suka kirata sosai Mamy ke kuka ta ce " ina ganin rayuwa ni Rahama Y'ata mace kenan a duniya ta kasa zama lfy ta kasa barinmu mu zauna lafiya Ta gurbata rayuwarta akan d'an namiji sosai take kuka Amer ne ya shigo cikin maganarsu ta y'an koyo ya ce "Mamy miya chameki" Shiru tayi mashi tana cigaba da hawaye "Shima kukan ya fara tare da rumgumeta washegari Mamy ta tashi da Rashin lafiyar koda sukaje Asibiti shaida musu akayi jinintane ya hau tana yawan tunani da sa damuwa