Sashe 26
Ni Da Yaya Arman Complete Hausa Novel · about 3 min read
Wajen la asr tana kwance a d'akin mamy kanta sai ciwo yake mata Amma ta shigo ta ce " Aira kije ya Umar na Kiranki"to ta fad'a tare suka fita a palour ta sameshi shi kadai Alamun Khady ta fita daga ita saishi yace Amma ta wuce ta basu waje kusa dashi taje ta zauna "Cikin nutsuwa ya ce " Hajara Naji Duka abunda kikayi yanzu Halimatu ke bani labari bani da labari sai yanxu na samu labari Dan kyautawa baku kyautaba Amma Duka ya wuce sai a tari gaba ke yanzu fad'amun Gaskiya kina son Mujahid ko a a magana ce tsakani na dake"Dagowa Aira tayi ta kalli ya Umar daman tasan shi baya da matsala Dan halin Mama yayo yana da hakuri ga nutsuwa komai cikin kwanciyar hankali yake binshi k'asa tayi ta kanta batasan lokacin da wasu zafaffan hawaye suka zubo mata ba ta ce "Yaya ina sonshi sosai kuma Shima yana sona banason a rabamu " ta k'arasa fad'a tana hawaye "Girgiza Kai Umar yayi ya ce " Arman bashi da Aibu Aira da zance wai ki rabu dashi amma ina baki shawarar kisan yanda kikayi kika rage sonshi a cikin zuciyarki sannan duk yanda zakiyi ki hakura dashi na y'an wani lokaci ki samu Ki shawo kan Abba ya barki ki jona makaranta kinajina duk abunda Abba yace kiyi kidinga yi ki dinga barin abunda ya hana saboda Kinsan dai Halin Abba mu Kanmu da girman mu da komai kiyaye umarninshi muke bareke Duka yaushe kikazo duniyar"Goge hawayenta tayi ta ce "Insha Allahu Yaya zanyi duk abunda kace nagode " Yawwa ko kefa y'ar wajen Inna sannan bance ki tada hankalinki ba kiyi rayuwarki.kamar yanda kike a baya kidaina sa damuwa a ranki ko so kike y'ar k'aramar kanwarmu ace ta kamu da hawan jini so kike tsufa ya kamaki da wuri"Murmushi Aira tayi ta ce "A a ayaya nadaina daga yau " To shikenan ko kefa yanzu kije kici abinci kinji y'ar kanwata"To yaya ta fad'a tare da tashi sosai taji d'an sanyi a ranta a ranta ta ce "Nidai nayi sa'ar yayyu Duka suna sona Allah na gode Maka da ka bani y'an uwa masu sona Nidai bansan wani Abu wai y'an ubanci ba har mamaki take idan a makaranta ana firar y'an uba ko ana zaginsu itadai Duka d'aya suka d'auketa" da wannan tunanin ta koma dakinsu ta tarar da Hafsa Na salla itama alwallar tayi taje tayi salla suna gamawa Amma ta zubo musu abinci a d'akin sukaci abinci su Ukku plate d'aya suna ci suna Hira Aira ce ta ce "Wai dazu daga ina kike naga kamar tare kuke da Abba " Daga B U K muke Registration mukaje Abba yayimun Bayan tafiyarki Mukayi jarabawar PUMB kuma naci sa a naci harsun bani admissions sosai na damu da bamuyi tare ba Kuma Kinga tare mukayi apply ta Online'"girgiza Kai Aira tayi ta ce "Allah ya taimaka ya baki sa'a nikam yanzu ba karatu ne gaba na ba nama fara hakura dashi " Sosai Amma tayi mamakin jin Abunda Aira ta ce "tana mata wani irin kallo ta ce " kamarya ba karatu ne ke gabanki ba to meye gabanki........✍🏿
*Ni da yaya Arman it's not free na kudi ne it's #200 via katin Mtn to 07026166536 VTU OR PC #300 kada ku fitarmun da littafi kudin karantawa kuka biya ba na mallaka ba*
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿🤙🏿
[6/13, 23:20] Hajo hajo: 🅿️........*41&42*
*Ni da yaya Arman it's not free na kudi ne it's #200 via katin Mtn to 07026166536 VTU OR PC #300 kada ku fitarmun da littafi kudin karantawa kuka biya ba na mallaka ba*
_*Miss Hajo ce*_🤙🏿🤙🏿
[6/13, 23:20] Hajo hajo: 🅿️........*41&42*